
22/10/2024
Ministan Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, Nyesom Wike ya gargaɗi mabarata da ke kara-kaina a kan titunan birnin da cewa ko dai su daina ko kuma hukumomi su fara k**a su.
Wike ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da fara gina wani t**i a unguwar Katampe da ke birnin.
Ya koka cewa yawan mabarata a titunan Abujan lamari ne da ke da barazana ga tsaron mazauna birnin.
Daga nan sai ya ba da sanarwar cewa daga ranar Litinin mai zuwa, 27 ga watan Oktoban 2024 za a fara k**a duk wanda aka gani yana bari a t**i.