GNN Hausa

GNN Hausa Shafin da ya dace ka Ku amince dashi dan kawo muku sahihan labarai

GWAMNA ABBA KABIR NASON HANA KWANKWASO SHIGOWA JIHAR KANO - Buba GaladimaJigo a NNPP, Buba Galadima, ya zargi Gwamnan Ka...
12/02/2026

GWAMNA ABBA KABIR NASON HANA KWANKWASO SHIGOWA JIHAR KANO - Buba Galadima

Jigo a NNPP, Buba Galadima, ya zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da rubuta wa Gwamnatin Tarayya wasiƙa domin hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shigowa jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da DCL Hausa, yana mai cewa suna jiran martanin Gwamnatin Tarayya. Ya ce idan aka yi yunƙurin hana shi shiga, za su kalubalanci matakin a kotu.

Galadima ya kuma yi watsi da zargin tsananta wa Kiristoci da ake yi wa Kwankwaso, yana mai cewa siyasa ce kawai. Ya ƙara da cewa duk da barazanar da ake yi masa, Kwankwaso ya ƙi shiga APC sai dai idan an cika sharuddan da za su amfani jama’a.

Game da zaɓen 2027, ya ce NNPP za ta ɗauki matakin da ya dace da muradun mabiyanta da al’ummar ƙasa.

Kwankwasiyya ta yi watsi da Zargin tsattsauran ra’ayi da ƴan majalisar Amurka s**a yi wa Kwankwaso Ƙungiyar Kwankwasiyya...
12/02/2026

Kwankwasiyya ta yi watsi da Zargin tsattsauran ra’ayi da ƴan majalisar Amurka s**a yi wa Kwankwaso

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da zargin da ake yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a cikin wani kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka, tana mai cewa zarge-zargen marasa tushe ne kuma na yaudara.

A cikin kudirin mai taken Nigeria Religious Freedom and Accountability Act 2026 (HR 7457), an ambaci sunan Kwankwaso dangane da zarge-zargen take hakkin ‘yancin addini.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya fitar a Kano, ya ce tarihin rayuwa da hidimar Kwankwaso ba su nuna wani laifi na tsattsauran ra’ayi ko cin zarafin addini ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa tsarin Shari’a da aka kafa a wasu jihohin Arewa yana ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ba Kano kaɗai ba ce ta aiwatar da shi.

Ta kuma buƙaci Majalisar Dokokin Amurka da ta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirin, tana mai zargin cewa wasu na ƙoƙarin amfani da batun domin cimma manufofin siyasa.

Kwankwasiyya ta jaddada cewa Kwankwaso ɗan kishin ƙasa ne wanda ya tsaya kan adalci, haɗin kai da zaman lafiya.

Ko masu karatu zasu iya Rubuta mana sunan wannan?Matar wani tsohon shugaban kasa ne a Nigeria
12/02/2026

Ko masu karatu zasu iya Rubuta mana sunan wannan?

Matar wani tsohon shugaban kasa ne a Nigeria

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share