Arewa Post

Arewa Post Sahihan labaran ciki da wajen Najeriya.

Al'umma A Jihar Imo Sun Yiwa El'rufai Tofin Alatsine, Sun Yi Watsi Da Shi Tare Da Nuna Ƙyma Da Irin SiyasarsaDaga Abdul-...
09/09/2025

Al'umma A Jihar Imo Sun Yiwa El'rufai Tofin Alatsine, Sun Yi Watsi Da Shi Tare Da Nuna Ƙyma Da Irin Siyasarsa

Daga Abdul-Azeez Suleiman

Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna, ya gamu da zanga-zangar ƙin karɓarsa a Owerri, Jihar Imo, lokacin da ya halarci Taron Odenigbo 2025 a Assumpta Cathedral. Jama’a sun fito da kwalaye da ƙorafe-ƙorafe, suna zarginsa da kalaman wariya kan kabilar Igbo a baya.

Wannan martani bai tsaya kan shi kaɗai ba, ya kuma fito da tsohuwar matsalar rashin haɗin kai, raunin Yaƙin Basasa, da kuma gajiyar jama’a ga shugabannin da ake ganin sun rabu da halin rayuwar talakawa.

Masu zanga-zangar har sun yi kira ga a tsawatar wa Peter Obi saboda kusancinsa da shi, abin da ya nuna cewa kowane ɗan siyasa na iya fuskantar tambaya muddin yana da alaƙa da mutanen da ake kallon masu raba kan ƙasa.

Zanga-zangar ta zama alamar cewa jama’a na da ƙarfi wajen kalubalantar manyan ‘yan siyasa, musamman a wannan zamani na kafafen sada zumunta. Darasin da ke ciki shi ne shugabanni su daina rarrabuwar kawuna, su rungumi tattaunawa, su girmama tarihi, domin kawai haka za a samu haɗin kan ƙasa mai bambance-bambance.

Jama’a Sun Yi Masa Watsi, Sun Nuna Ƙiyayya da Siyasar Rarrabuwar irin ta El'rufai, sun kuma shawarci Peter Obi da ya gaggauta nesanta kansa da El'rufai don tsira da mutuncinsa.

Gidauniyar Matawallen Matazu ta bayar da tallafin kayan Abinci da kayan Dogaro dakai  na Miliyoyin Kuɗaɗe a Jihar Katsin...
08/09/2025

Gidauniyar Matawallen Matazu ta bayar da tallafin kayan Abinci da kayan Dogaro dakai na Miliyoyin Kuɗaɗe a Jihar Katsina.

A yau Litinin 08/09/2025, Gidauniyar Matawalle Foundation Wacce take ƙarƙashin jagoranci Engr Abubakar Matazu ( Matawalle Matazu GM ) ta bayar da tallafin kaya na Miliyoyin Kuɗaɗe ga al'ummar. Jihar Katsina.

Kayan da gidauniyar ta Raba Sun haɗa da :
Shinkafa Buhu Dubu biyu 2000 Injinan ban Ruwa Ɗari Biyar 500 Kekunan Dinki Ɗari Biyar 500

Sai kaddamar da littattafan rubutu as pilot project wanda ko wane local government za'a baiwa Ɗaliba Dubu biyar 5000

Allah yasaka masa da alkhairi Ameeen.

Ba fa jam'iyyar APC bace kawai matsalar Najeriya ba, gurbatattun 'yan siyasa ne da jami'an Gwamnati da wasu talakawan ka...
22/08/2025

Ba fa jam'iyyar APC bace kawai matsalar Najeriya ba, gurbatattun 'yan siyasa ne da jami'an Gwamnati da wasu talakawan kasar, kuma dukkanninsu suna nan a cikin kowace jam'iyya ~ Inji Matashi Abba Sani Pantami

Me za ku ce?

Nan Jami'an Sojojin Saman Nijeriya Ne Ke Sarawa Sarki Sanusi II A Yayin Da Ya Ziyarci Ofishinsu Dake Filin Jirgin Sama N...
18/08/2025

Nan Jami'an Sojojin Saman Nijeriya Ne Ke Sarawa Sarki Sanusi II A Yayin Da Ya Ziyarci Ofishinsu Dake Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano

2027: Hukumar EFCC ta damƙe tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanatan jihar Sokoto a yanzu Aminu Waziri Tambuwal kan zarg...
11/08/2025

2027: Hukumar EFCC ta damƙe tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanatan jihar Sokoto a yanzu Aminu Waziri Tambuwal kan zargin almundahanar Naira biliyan 189bn.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yana hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) a birnin Abuja.

Tambuwal, wanda yanzu haka yake matsayin Sanata a majalisar dattawa, na fuskantar tambayoyi kan zargin fitar da kuɗaɗe daga baitul-mali ba bisa ka’ida ba, waɗanda rahotanni ke cewa sun kai kimanin Naira biliyan 189.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa EFCC ta tsare shi domin gudanar da bincike kan wannan zargi, yayin da ake ci gaba da samun ƙarin bayanai kan lamarin.

Mikiya.

“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR“A lokacin da nake Kwa...
08/08/2025

“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR

“A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba.

Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu 'yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu.

A wani shingen bincike “checkpoint” dake t**in Herbert Macaulay, wasu matasan 'yan sanda s**a tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace:

> "Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?"

Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Mohammed. Yace dole sai na nuna ID card. Na ce masa, to ya fara nuna mini nasa. Bai da ID card, don haka sai ya kira sergeant dinsu.

Shi ma sergeant din ya bukaci ID card dina, na ce masa ya nuna mini nasa kafin nawa. Ganin bana jin tsoro ko nuna daraja, sai s**a ce mu tafi ofishin ‘yan sanda na Yaba (Panti) domin “gano ko ni wanene”.

Muna isa station – babu parking sai a wajen DPO. Na ajiye motata a can, constable din ya fusata yace: “Wannan wajen parking din DPO ne fa!” Ko uffan ban ce masa ba.

Bayan mun shiga ciki, sai s**a kaini wurin wani ASP (Assistant Superintendent of Police) wanda ke sanye da gajeren wando 'shorts'!. Yace na shigo, na ki, nace masa ba zai yiwu ya tuhumeni cikin kayan gida ba. Yayi fushi ya jawo ni ciki da ƙarfi – nima ina jan shi. Da ya duba fuskata da kyau sai ya fara zare ido…

A gefe guda, wani tsoho da ke ofishin ya leƙa ofishin DPO don duba hoton shugabannin rundunar Ƴan sanda dake jikin bango. Da ya tabbatar cewa ni ne, sai kawai ya tsallake taga ya gudu!

Sergeant da ya kawo ni ya kasa gane me ke faruwa, har sai da wani Ɗan sanda ya matso kusa da kunnensa, ya ce masa: “Kai, CP ne wannan fa!”.

Cikin firgici, ASP ɗin da ke sanye da shorts ma ya bi taga ya gudu!

Bayan haka, Area Commander ya kirani ya tambaya me ya faru. Aka gaya masa cewa an tsare DPO, ASP, da sauran ‘yan sanda da s**a shiga lamarin – suna jiran umarni na.

Abin da ya fi tada min hankali ba wai kamun da s**a yi min ba ne – a’a, amma irin yadda s**a nuna rashin tarbiyya, rashin horo, da rashin kwarewa a aiki.

Yaya dan sanda zai tsaya a t**i ba tare da ID ba, yana tsare jama’a? Yaya ASP zai zauna da kaya irin na gida yana sarrafa aiki? Wannan ya kara tabbatar min da cewa shugabanci ba sai ka zauna ofis ba – dole ka fita ka duba, ka gani da idonka, ka tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki.

Fassara: AB Damare

'Yan Kwankwasiyya Suna Cikin Wahala Ba'a taimakonsu kullum da shegiyar hula  yar N200 Suke yawo jama'a in sun gan Mu dau...
05/08/2025

'Yan Kwankwasiyya Suna Cikin Wahala Ba'a taimakonsu kullum da shegiyar hula yar N200 Suke yawo jama'a in sun gan Mu dauka Suke mune Masu Gwamnati.

Cewar ~ Abdullahi Abbas Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Kano.

Idan Aka Zaɓe Ni Zan Yi Wa'adi Ɗaya Na Shekaru 4 Na Sauka Daga Mulki, Cewar Peter Obi Tsohon ɗan takarar shugabancin Naj...
03/08/2025

Idan Aka Zaɓe Ni Zan Yi Wa'adi Ɗaya Na Shekaru 4 Na Sauka Daga Mulki, Cewar Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.

Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, "sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana cigaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci."

Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, "amma wa'adi ɗaya kawai ya yi."

"Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa. Saboda haka ne nake sake nanata alƙawarin da na yi cewa wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zan yi idan na zama shugaban Najeriya," in ji shi.

Ya ƙara da cewa ya san ƴan Najeriya ba su cika yarda da maganar ƴan siyasa ba, "amma duk da haka akwai masu cika alƙawari."

"Na ga wani yana rubuta cewa ko da me zan rantse ba zai yarda cewa wa'adi ɗaya zan yi ba, wani kuma ya ce duk wanda ya ce wa'adi ɗaya zai yi ya je asibitin ƙwaƙwalwa."

Obi ya ce ya fahimci abin da suke nufi, amma a cewarsa, yana da tarihi mai kyau wajen cika alƙawari tun daga lokacin da ya fara siyasa a Anambra, inda ya ce wata 48 sun isa duk wani shugaba da ya shirya mulki ya yi abin da ya dace.

"Idan na zama shugaban Najeriya a wa'adi ɗaya zan magance matsalar tsaro, zan yaƙi da talauci in inganta aikin gwamnati, sannan zan fifita ɓangaren ilimi da kiwon lafiya, sannan in yaƙi cin hanci da rashawa. Sannan uwa-uba zan inganta ɓangaren noma ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha domin Najeriya ta zama ƙasa.

Daily Nigerian Hausa

Kalli Yadda Bikin Baje Kolin Dabino Mafi Girma Na Duniya Ke Gudana A Yankin Buraidah Dake Kasar Saudiyya.Shin Me Ke Burg...
03/08/2025

Kalli Yadda Bikin Baje Kolin Dabino Mafi Girma Na Duniya Ke Gudana A Yankin Buraidah Dake Kasar Saudiyya.

Shin Me Ke Burge Ku Game Da Dabino?

Hotuna: Fb/KSA Expats

Sarakuna Ku Girmama Matsayinku: Ku Fice Daga Rikicin Jam’iyyar ADC, Ku Bar Malam Nafi’u Bala Gombe Ya Cigaba Da Aikin Gy...
02/08/2025

Sarakuna Ku Girmama Matsayinku: Ku Fice Daga Rikicin Jam’iyyar ADC, Ku Bar Malam Nafi’u Bala Gombe Ya Cigaba Da Aikin Gyara Jam’iyya Cikin Gaskiya

Ofishinmu na Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) yana bayyana damuwarsa matuka kan yadda wasu sarakunan gargajiya ke kiran waya da nufin matsin lamba ga Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar, Alhaji Nafiu Bala Gombe, domin ya sauya matsayinsa na kare tsarin dimokuradiyya da doka na jam’iyyar.

Wannan barazana da kuma kiran da ake yi ga wasu mambobin Kwamitin Zartaswa na Kasa (NWC) domin su ja da baya daga goyon bayan shugabansu, abin takaici ne kwarai, musamman ganin cewa sarakuna sun bar turbarsu ta raya al’adu da zaman lafiya, sun rungumi muradin wasu 'yan siyasa masu son karbe jam’iyya ta kowane hali.

MAKIRCI NA BAYA-BAYAN NAN

Bayanan sirri daga majiya mai karfi na nuni da cewa wasu manyan ’yan siyasa da s**a hada da Janar David Mark da Mallam Nasir El-Rufai da wasu gungun mutane sun hada wata kungiya da ke shirin tura dattawa su je Gombe domin matsawa mahaifiyar Shugaban rikon kwarya da nufin tilasta masa mika jam’iyyar da nufin cinma burinsu na siyasa a shekarar 2027.

Wannan yunkuri na ziyarar mahaifiyar Shugaban jam’iyyar abu ne da ba za mu lamunta da shi ba. Hakan na nuna cewa wasu sun sadaukar da dimokuradiyya ga son zuciya da yin coge don biyan muradinsu na 2027.

1. Muna da tabbaci daga bayanen sirri masu inganci cewa wadannan sarakuna na kokarin tilasta Alhaji Nafiu Bala Gombe ya mika jam’iyya ga 'yan siyasa masu matasanancin kwadayin mulki ta hanyar matsa masa da kiraye-kiraye a wayarsa tare da shisshigi a boye. Wadannan sarakuna ba su kyauta ba, saboda suna neman rage kima da martabar al'adunmu masu nagarta ta hanyar neman zama 'yan koren masu mayatar son mulkin siyasa a shekarar 2027. Wannan abin jimami ne ga dukkan mai kishin martabar masarautinmu.

2. Wannan kuskure ne mai muni daga bangaren sarakuna, wadanda ya kamata su tsaya a gefe su kasance iyayen kasa masu kima.

3. Mu na kara fayyacewa: Sarakuna ba su da hurumin shiga harkokin jam’iyyar ADC ko zama 'yan gada-gadar 'yan siyasa. Wannan ba shekarar 1983 ba ce; yanzu idon kowa a bude yake. ADC ba ta sayarwa ba ce!

4. Alhaji Nafiu Bala Gombe ba zai ja da baya ba, yana da cikakken goyon bayan dokokin jam’iyya da mambobinta masu kishin kasa.

5. Wadanda suke fakewa da cewa suna hidimar “sasantawa”, yaudarar jama'a suke, da nufin biyan muradin 'yan cogen Hadaka ta Zaben 2027. Su sani cewa za mu bayyana sunayensu da cikakken bayani game da boyayyiyar manufarsu, in bukatar yin hakan ta taso.

6. Ga wadanda suke matsayin sarakuna amma s**a tsunduma siyasa da goyon bayan hargitsi, muna ba ku shawara: ku koma ku kula da masarautunku. Kada ku sayar da martabarku da al'adunmu masu nagarta don biyan bukatun 'yan siyasan da s**a shahara wajen yaudarar al'umma shekara da shekaru.

MATSAYARMU A KAN WANNAN KATSALANDAN:

Jam’iyyar ADC ba ta sayarwa ba ce. Ba za mu bar makircin wasu mayaudaran 'yan siyasa ya kassara mulkin dimokuradiyyan kasar nan ba, ko ya lalata alkiblar jam’iyyar ADC ba. Kuma za mu fallasa kowane mai hannu a ciki — ko saraki ne shi ko dan bangar siyasa.

In kunne ya ji, jiki ya tsira.

Sanya hannu:
Dr. Aminu Sani Alhassan
Mai Baiwa Shugaban Rikon Kwarya Shawara kan Harkokin Jama’a
Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC)
Abuja

Rikicin ADC Ya Kara Ta'azzara: Bala Gombe Ya Ayyana Kansa a  Matsayin Shugaban Jam'iyya, Ya fatattaki su El-Rufa’i Rikic...
31/07/2025

Rikicin ADC Ya Kara Ta'azzara: Bala Gombe Ya Ayyana Kansa a Matsayin Shugaban Jam'iyya, Ya fatattaki su El-Rufa’i

Rikicin cikin gida a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya ƙara ɗaukar sabon salo, bayan Nafiu Bala Gombe, Mataimakin Shugaban ƙasa na jam’iyyar, ya ayyana kansa a matsayin Shugaban rikon kwarya.

A cewarsa, hakan ya zama dole sakamakon abin da ya kira ƙoƙarin wasu manyan 'yan siyasa – ciki har da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i – na mallake jam’iyyar tare da cusa son zuciya a harkokin tafiyar da ita.

Bala ya zargi tsoffin shugabannin jam’iyyar da mika madafun iko ga wasu 'yan bangar siyasa a cikin ADC, inda ya bayyana su a matsayin ‘sojojin gona’ masu burin hallaka tsarin dimokuradiyya da jam’iyyar ta gina tsawon shekaru.

Ya ce wadannan sojojin haya, wadanda ba su wata alaka da ADC, suna shirin mayar da ita jam’iyyar aljihun mutane irin su Elrufai, domin cimma muradun kansu na siyasa.

A cewarsa, El-Rufa’i da magoya bayansa suna kokarin amfani da ADC a matsayin wani tsani na wucin-gadi domin cimma wata manufa ta siyasa da ke nuni da shirinsu na fuskantar zaben 2027.

Ya bayyana yunkurin Elrufai da 'yan korensa a matsayin babbar barazana ga tsarin shugabanci na jam’iyyar da dimokuradiyya gaba ɗaya.

Bala ya kuma bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta girmama kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC, tare da kin amincewa da duk wani yunƙurin da ya saba da tsarin. Ya ce matakin da ya ɗauka na zama Shugaban rikon kwarya yana da cikakken tushe a kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ya ti hakan ne don kare mutuncin ADC daga mamayar da ke neman hana ta numfashi.

Ya jaddada cewa ba za su yi shiru ba yayin da wasu ke yunƙurin lalata abin da s**a gina na tsawon shekaru, kuma duk wani yunkuri da El-Rufa’i da abokan tafiyarsa ke yi ba zai kai ga nasara ba.

A karshe ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa ta jaddada kasancewarsa shugaba a hukumance.

YANZU YANZU: Na koma jam'iyyar Apc ne Saboda Tausayin talakawa, Na bar jam'iyyar NNPP na koma APC ne don samar wa al'umm...
23/07/2025

YANZU YANZU: Na koma jam'iyyar Apc ne Saboda Tausayin talakawa, Na bar jam'iyyar NNPP na koma APC ne don samar wa al'ummar yankina abin da zai amfanar da su, inji Kawu Sumaila

ɗan majalisar dattawa daga jihar Kano, Sanata Abdurahman Kawu Sumaila wanda ya fice daga NNPP ya koma APC, ya bayyana dalilinsa na ɗaukar matakin.

Ya kuma ce nan gaba akwai wasu ƙarin ƴan jam'iyyar NNPP a jihar da su ma za su fice daga jam'iyyar.

Address

Nsukka Street Abuja
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Post:

Share