06/10/2025
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قَالَ
كُنْتُ رِدْفَ النَّبِيِّ ﷺ عَلَى حِمَارٍ، فَقَالَ لِي:
يَا مُعَاذُ، أَتَدْرِي مَا حَقُّ اللَّهِ عَلَى الْعِبَادِ، وَمَا حَقُّ الْعِبَادِ عَلَى اللَّهِ؟
قُلْتُ: اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ
قَالَ: فَإِنَّ حَقَّ اللَّهِ عَلَى الْعِبَادِ أَنْ يَعْبُدُوهُ وَلَا يُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا،
وَحَقُّ الْعِبَادِ عَلَى اللَّهِ أَنْ لَا يُعَذِّبَ مَنْ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَفَلَا أُبَشِّرُ النَّاسَ؟
قَالَ: لَا تُبَشِّرْهُمْ فَيَتَّكِلُو
Abinda wannan Hadisi ya ƙunsa da Hausa:
Mu‘az bin Jabal (Allah ya yarda da shi) ya ce:
Na kasance ina bin Annabi ﷺ a bayan jaki (yana goye da shi), sai Annabi ya ce mini:
“Ya Mu‘az! Ka san menene haƙƙin Allah a kan bayinsa, da kuma haƙƙin bayin Allah a kansa?” Na ce: “Allah da ManzonSa sun fi sani.” Sai Annabi ﷺ ya ce:
“Haƙƙin Allah a kan bayinsa shi ne, su bauta masa kada su yi masa shirka da komai .
Kuma haƙƙin bayin Allah a kanSa shi ne, ba zai azabtar da wanda bai yi masa shirka ba.”
Sai na ce: “Ya Manzon Allah, shin ba zan sanar da mutane wannan bushara ba?” Sai ya ce: “Kada ka sanar musu, kar su dogara (su daina aiki suna tsammanin za a gafarta musu kawai).”
Darussa biyar a takaice daga wannan Hadisi:
Tauhidi shi ne haƙƙin farko da Allah yake da shi akan bayinsa, kuma wajibi ne su kawo wannan haƙƙi.
Yin shirka shi ne, mafi girman zunubi a gurin Allah, wanda akan rasa rahma saboda wannan laifi.
Yana nuna cewa Allah yana da rahama sosai ga wanda yake bauta masa shi kaɗai, batare dayi masa kishiya ba.
Manzon Allah ﷺ yana da hikima, wadda har bai yarda a yaɗa labarin rahama kawai ba, domin mutane kada su daina aiki, shi ke kara nuna maka cewa ana addini ne, Bayna’l khawf wa Raja, hadisin na nuna cewa Ilimi da hikima su ne ginshikin isar da saƙon addini.
Fassarar wasu kalmomi da Sharhin Hadisin, don ƙara fito da ma’ana.
Kalmar Mu‘az ta farko wadda yake cewa: “Na kasance ina bayan Annabi ﷺ akan jaki, sai ya ce mini: ‘Ya Mu‘az, ka san menene haƙƙin Allah akan bayinsa da haƙƙin bayinsa akan Allah?..
Kalmar tana nuna yadda Annabi ﷺ yake nuna ƙauna da kulawa ga sahabbansa. Ta yanda har yana iya ɗaukar Mu‘az a bayansa, kaga kenan ashe duk shugaba, yana da kyau ya fahimci cewa, rashin girman kai da kyautatawa na ƙasa shi ne nagarta, tunda ga wanda yafi kowa ﷺ yana hawa abin hawa daya da sahabinsa, har yana tambayarsa don koyar da shi wasu darussa da bai sani ba.
Malam Ibn Hajar al-‘Asqalani (a Fath al-Bari) ya ce: Annabi ﷺ yana yin hakan ne domin ya sa Mu‘az ya fahimci darasi sosai, ma’ana cikin hikma ta Annabi ﷺ zaka fahimci kenan ana jan mutum ne a jiki, batare da kyara ko tsangwama ba, idan ana son a fahimtar da shi wani ilmi.
Abu na gaba shi ne Tambayar: “Ka san menene haƙƙin Allah a kan bayinsa da haƙƙin bayinsa a kan Allah?”
Tana nuna hikima ta yanda Annabi ﷺ ya fara da tambaya domin ya jawo hankalin Mu’az, Wannan hanya ce ta malamai masu hikima, a tambayi ɗalibi kafin a faɗa masa amsa, domin ya natsu ya kuma bayar da hankalinsa wajen sararo, ta nan zaka ƙara fahimtar irin fasaha da hikimar Allah ya yiwa Manzon Allah ﷺ.
Sannan amsar Annabi ﷺ ya bayar cewa,“Haƙƙin Allah akan bayinsa shi ne su bauta masa, kada su haɗa shi da wani wajen bauta, tare da faɗinsa.“Haƙƙin bayin Allah a kansa shi ne, ba zai azabtar da wanda bai yi masa shirka ba.
Wannan yana nufin cewa, haƙƙin Allah akan bayinsa, kai tsaye wannan yana nufin tauhidi, kenan yin ibada ko bauta ga Allah yake shi kaɗai, ba tare da yin shirka, kuma wannan shi ne tushen dukkan wata bauta a musulunci, k**ar yadda Allah ya ce:
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
“Ban halicci aljannu da mutane ba sai domin su bauta mini.” (Surat adh-Dhariyat: 56)
Faɗin Haƙƙin bayi akan Allah kuwa, wannan ba yana nufin Allah yana da wajibi a kansa saboda wani iko na bayi ba, amma saboda karamci da rahama ta Allah, ya alƙawarta rahama da gafara ga wanda bai yi masa shirka ba, ma’ana wanda baya haɗa Allah da kowa a cikin bautarsa.
Imam An-Nawawi ya ce a Sharh Sahih Muslim:
Wannan hadisi yana nuna cewa Allah yana da rahama da alƙawari na adalci, amma wannan haƙƙi ya tabbata ne saboda alƙawarin da Allah Ya yi, ba domin wani ya tilasta masa ba, ko kuma yana da ikon yasa Allah yayi hakan.
Faɗin maganar Mu‘az ta cewa, “Ya Rasulallah, shin ba zan sanar da mutane wannan bushara ba?.
Wannan kai tsaye yana nuna ƙaunar Mu‘az ga mutane, yana so mutane su san wannan ni’ima, saboda sahabban Annabi basa taɓa jin wani ilimi su ɓoye shi don amfanin kansu, Amma kuma Annabi ﷺ ya nuna hikima a amsar daya bawa Mu’az.
“Kada ka sanar da su, kar su dogara.”
Kai tsaye wannan na nuna maka irin yanda Annabi ﷺ ya san halin mutane, ta yanda idan sun ji cewa wanda bai yi shirka ba, ba zai shiga wuta ba, wasu zasu iya kasala wajen bautar Allah, su daina aiki, su dogara kaɗai kan cewa in basuyi shirka ba, bazasu shiga wuta ba.
Don haka Annabi ﷺ ya hana yaɗa wannan bayani a lokacin, har sai mutane sun karɓi tauhidi sosai, sannan sai a sanar dasu wannan ni’ima.
Anan gurin yakai mai karanta wannan dogon rubutu zaka fahimci cewa, Tauhidi shi ne ginshiƙin addinin Musulunci, sannan shirka ita ce babban zunubin da Allah baya gafartawa idan mutum bai tuba ba, sannan zaka ƙara fahimtar Rahamar Allah tana da girma da faɗi sosai, amma kuma aikin ibada yana da muhimmanci, sannan zaka ƙara fahimtar cewa, Ilimi yana da daraja Annabi ﷺ yana koyar da sahabbai ta hanya mai taushi da hikima, batare da kyara ko ɗaga murya ba, kuma zai ƙara nuna maka cewa, ba’a yaɗa ilimi ba tare da hikima ba, k**ar yanda Annabi ﷺ ya hana Mu‘az ya rarraba labarin kafin lokacin da ya dace mutane su sani.
Abun nufi dai wannan hadisin yana nuna cewa, dukkan wata bauta da ibada ga Allah ne shi kaɗai, saboda shike karɓa ya bada sak**ako, matuƙar dai babu shirka, wannan ita ce hanyar tsira da rahama.
Sannan wannan hadisi yana jaddada ma’anar Kalimatut Tauhid ta “Lā ilāha illallāh”
Allah yasa mu dace duniya da lakhira, mu kwana lafiya…
Abdallah Amdaz