Nigerian Post

Nigerian Post Nigerian Post
(1)

ADC kuke ko APCin Tinubu a 2027?
03/07/2025

ADC kuke ko APCin Tinubu a 2027?

Na ɗauki Alkawarin Kafin karfe 12:00  Na Rana Zan kawowa Jam'iyyar ADC kuri'un Jihar Kano a Zaben Gwamna dana Shugaban k...
03/07/2025

Na ɗauki Alkawarin Kafin karfe 12:00 Na Rana Zan kawowa Jam'iyyar ADC kuri'un Jihar Kano a Zaben Gwamna dana Shugaban kasa, inji Malam Ibrahim Shekarau

Dan wasan ƙungiyar Liverpool Diogo Jota ya mutu sakamakon hadarin mota
03/07/2025

Dan wasan ƙungiyar Liverpool Diogo Jota ya mutu sakamakon hadarin mota

DA DUMI DUMI: Uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa Tayi Allah Wadai Bisa yadda Wasu daga cikin ya'yan jam'iyyar PDP S**a fice daga...
03/07/2025

DA DUMI DUMI: Uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa Tayi Allah Wadai Bisa yadda Wasu daga cikin ya'yan jam'iyyar PDP S**a fice daga jam'iyyar Zuwa jam'iyyar Haɗaka Ta ADC, inji Shugaban jam'iyyar PDP Umar Damagum

Uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ta Bayyana cewar Babu Abinda Ya damesu Sannan ta Barranta Kanta da Sabuwar jam'iyyar Haɗaka Ta ADC, Sannan tayi kira kada Su kuskura Su koma cikin Sabuwar jam'iyyar Haɗaka Ta ADC

Jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ta yi gargaɗi ga dukkan mambobinta da ke ƙulla shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa cewa suna “kallon su sosai” kuma za su ɗauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar ranar Laraba, Mukaddashin Shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Damagum, ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar su sani babu inda ya fi gida dadi.

Ya ƙara da cewa babu wata jam’iyya da za ta iya ba su dama da kulawar da PDP ta ba su tun farko.

Ambasada Damagum ya kuma ja kunnen su cewa soyayya da wasu jam’iyyu ba za ta daɗe ba, inda ya nuna tabbacin cewa da dama daga cikinsu za su dawo gida nan ba da jimawa ba.

Motar Hukumar Sufuri Ta KTSTA Ɗauke Da Fasinjoji Tayi HadariMun samu labarin motar hukumar sufuri ta jihar Katsina KTSTA...
03/07/2025

Motar Hukumar Sufuri Ta KTSTA Ɗauke Da Fasinjoji Tayi Hadari

Mun samu labarin motar hukumar sufuri ta jihar Katsina KTSTA ɗauke da fasinjoji ta gamu da hadari a dai-dai garin Makurdi bayan ta taso daga Funtua zuwa Katsina.

A rahoton da muka samu har kawo wa yanzu ba a kai ga tantance adadin mutanen da hadarin ya shafa ba.

DA ƊUMI ƊUMI: Tsagin jam’iyyar Labour Party, ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta bai wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na...
03/07/2025

DA ƊUMI ƊUMI: Tsagin jam’iyyar Labour Party, ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta bai wa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Peter Obi, wa’adin awanni 48 da ya fice daga jam’iyyar, bayan yanke shawarar da ya yi na shiga haɗakar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

A jiya Laraba aka sanar da Obi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasa da su ka ɗauki matakin shiga haɗakar ta ADC, wanda aka kafa domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a Abuja, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Obiora Ifoh, ya bayyana wannan haɗin gwiwa a matsayin taron “masu neman mulki” kuma ya zargi Obi da zama ɗan jam’iyyu biyu a lokaci guda.

Ya ce; “Mun san da tarurruka da dama da Peter Obi ke halarta da wasu daga cikin mambobinmu a cikin dare, yana lallaba su da su biyo shi zuwa sabuwar jam’iyyarsa. Mun kuma san cewa da dama daga cikinsu sun ƙi bin sa.”

A cewarsa, jam’iyyar Labour Party ba ta da alaƙa da wannan haɗin gwiwa kuma ba za ta yarda da mutanen da ke da “manufofi biyu” ko “fuska biyu” ba.

YANZU-YANZU: ’Yan majalisar wakilai bakwai daga jihar Akwa Ibom sun fice daga jam’iyyarsu ta PDP da YPP, sun koma APC.
03/07/2025

YANZU-YANZU: ’Yan majalisar wakilai bakwai daga jihar Akwa Ibom sun fice daga jam’iyyarsu ta PDP da YPP, sun koma APC.

Ba zan bar PDP ba amma ina maraba da haɗakar ƴan adawa don ƙwatar mulki a 2027 - Sule Lamido Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa...
03/07/2025

Ba zan bar PDP ba amma ina maraba da haɗakar ƴan adawa don ƙwatar mulki a 2027 - Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce a shirye yake ya mara wa kowacce haɗaka ta ƴan adawa don kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Vanguard a Abuja a jiya Laraba.

Lamido ya ce ko da ya ke yana goyon bayan haɗewar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa jagorancin Sanata David Mark, ba zai fice daga jam’iyyarsa ta PDP, wadda ya ce da shi aka kafa ta ba

Ya ce ba daidai ba ne a watsar da PDP saboda waɗanda ya kira “marasa godiya” da ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.

"Eh a shirye na ke da duk wani yunkuri na kifar da APC don a ceci Najeriya. Zan mara wa duk wanda ke da wannan buri. Zan yi kamfe tare da su. Amma mu PDP ita ce jam'iyya ta. Ko da ya ke tana fuskantar rikici, zan zauna in yi gwagwarmaya don ceto ta."

Ɗan wasan Liverpool Diogo Jota ya rasa ransa a haɗarin mota tare da ɗan uwansa Andre Silva a birnin Zamora da ke Sifaniy...
03/07/2025

Ɗan wasan Liverpool Diogo Jota ya rasa ransa a haɗarin mota tare da ɗan uwansa Andre Silva a birnin Zamora da ke Sifaniya inda su biyu s**a rasa rayukansu.

Jota ya mutu ya bar yara uku da matarsa Rute Cardoso wadda ya aura a watan Yunin da ya gabata.

An karrama Alhaji Idi Kwado da lambar girmamawa a Katsina
02/07/2025

An karrama Alhaji Idi Kwado da lambar girmamawa a Katsina

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerian Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Nigerian Post:

Share