
15/06/2025
YAUMUL GHADEER KHUM
Ghadeer khum wani guri ne dake tsakanin Makkah da Madina,ma'ana mahaɗa wanda idan anzo wajen kowa zai k**a ganyar garin su
A shekara ta goma (10) bayan aiko Annabi Muhammad (S) a ranar 18 ga watan Zul-Hijjah Manzo ya naɗa Imam Ali AS a matsayin Khalifa magajinsa a bayan a bisa umarnin Allah Ta'ala
Bayan naɗa Imam Ali AS maka'ika Jibril AS ya ƙara sakkowa da wahayi cewar a yau addini ya cika.
Wannan Idi na ghadeer khum shine idi na farko mafi daraja a wajen Musulmi da duniya baki daya
A ranar ne Manzon Allah sallahu alaihi wa Alihi wa sallam ya ɗaga hannun Imam Ali AS yace:
"Man kuntu mawlaahu fa-hadha Aliyyun mawlaahu"
Ma'ana: Wanda na kasance shugabansa ne to ga Ali AS nan ya zama shugaban sa a baya na.
Bayan kammala doguwar huɗuba da Manzon Allah yayi wanda a wurin akwai Sahabbai sama da mutane 100,000+
Cikar mutanen da ke wurin kowa ya miƙa bai'ar sa ga Imam Ali AS,bayan haka Manzon Allah ya ce duk wanda yaji ya sanar da wanda baiji ba
Muna ƙara sanar da duniya saƙon Manzon Allah na nasabta Imam Ali AS a matsayin Khalifa a bayansa,kuma muna ƙara jaddada bai'ar mu ga Imam Ali AS (Laibbaika Yaa Ali)
©Uwar Ɗaki Sayyidah Zainabul-Kubra Foundation.