
12/08/2025
Meyasa muke yin tattaki?? Amsa zuwa ga masu Hankali.
Bayan an kashe Imam Hussain a karbala, sojojin yazidu sun daddaure ragowar iyalan wadanda s**a kashe a karbala babu takalma a kafafun su suna dukan su da bulala ana jansu a kafa tun daga karbala wadda take kasar Iraki a yanzu har zuwa fadar yazid bin Muawiya a Damascus wadda take Siriya a yanzu.
Sannan bayan sun isa an gama abinda za'a yi musu, sun taka da kafafun su ne tun daga fadar yazidu har zuwa karbala domin ziyarar wanda aka kashe ranar da s**a iso shine kuma ranar da suke cika kwana 40 da kashe wa "Yaumu Arbaen" Maulana Imam Ali bin Hussain(as) shiya jagoranta kuma muma sunnar su muke rayawa.
Sahabin manzon Allah(S) Jabir bin Abdullahi Al-ansari shima yayi wannan tattakin a karbala kuma ya ziyarci Imam Hussain(as) sannan Imamai da dama da manyan bayin Allah na gari sun cigaba da raya wannan Al'amari. Misali kamar Shehu Ibraheem Inyass yayi tattakin Imam Hussain a Karbala shi ya fada ma da kansa a rubuce.
Allah ya tashe mu tare da Imam Hussain ranar kiyama ya sanya mu a cikin wadanda Manzon Rahama zai musu Masauki.
• Auwal Salisu