Hausaland

Hausaland Hausaland - Dandalin zamani domin masu alfahari da harshen Hausa!

Rediyo Tarayya  #1Akwai kuma manhajar Rediyo Tarayya ta Android a Play Store: https://rebrand.ly/5h4hjn9Ga masu iPhone d...
18/12/2023

Rediyo Tarayya #1

Akwai kuma manhajar Rediyo Tarayya ta Android a Play Store: https://rebrand.ly/5h4hjn9

Ga masu iPhone da wayoyin da ba an Android ba, sai ku saurari Rediyo Tarayya a browser ɗin wayarku kai tsaye a nan: https://rediyotarayya.webradiosite.com/

Muna kan aikin samar da app na iPhone nan ba da jimawa ba!

Rediyo Tarayya - Muna Tare!

Gabatar da Rediyo Tarayya!Ina mai farin cikin sanar da dukkan masu bibiyar wannan shafin nawa, cewa na kafa wani gidan r...
18/12/2023

Gabatar da Rediyo Tarayya!

Ina mai farin cikin sanar da dukkan masu bibiyar wannan shafin nawa, cewa na kafa wani gidan rediyo mai yaɗa shirye-shirye ta intanet mai suna REDIYO TARAYYA.

Ina fatan samar da labarai a rahotanni da za su ilmantar da nishaɗantar da kuma faɗakar da al'umomin da ke mu'amalla da harshen Hausa a faɗin duniya.

Saboda haka nake gabatar muku da wannan ƙafa mai albarka, da fatan za ku riƙa bibiyar dukkan shirye-shiryen Rediyo Tarayya a duk inda kuka sami kanku a duniyarmu ta intanet da shafukan sada zumunta.

Baya ga tashar rediyon, akwai shafin intanet mai adireshi da shafukan sada zumunta a Facebook da Instagram da TikTok da X (Twitter) da SoundCloud da kuma Threads, dukkansu da sunan .

Zan biyo wannan post ɗin da bayanai dalla-dalla kan yadda za a iya saurare da bibiyar Rediyo Tarayya.

Taken Rediyo Tarayya shi ne - Muna Taren

05/04/2023

Abin al'ajabi: Kalli yadda wata mage ta hau jikin limamin wani masallaci a Aljeriya yayin da ake sallar Tarawih.

Shugaba Buhari: Ina kira ga dukkan ku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Nagartacce ne kuma na yi amanna zai ci gaba ...
19/02/2023

Shugaba Buhari:
Ina kira ga dukkan ku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Nagartacce ne kuma na yi amanna zai ci gaba da ayyukan da muka yi.

Ni: Ba haka aka so ba wai kanin miji yafi miji kyau. 🙄

13/02/2023

Rahoton dan jarida Sani Aliyu na BBC Hausa wanda ya kai ziyara garin Dan Nakola na Daura a jihar Katsina. Garin Kifi da Shammai.

Idan da a kauyenmu ne, da jikin wadannan yaran ya gaya musu!
03/07/2022

Idan da a kauyenmu ne, da jikin wadannan yaran ya gaya musu!

Wannan matar Sarah Mohamed Abdullah ita ce fitacciyar mai gabatar da shirin safe a gidan rediyon Khartoum na Sudan 🇸🇩. J...
03/07/2022

Wannan matar Sarah Mohamed Abdullah ita ce fitacciyar mai gabatar da shirin safe a gidan rediyon Khartoum na Sudan 🇸🇩.

Jama'a sun san muryarta sosai, amma kadan ne s**a taba ganin hotonta.

02/07/2022

Kalli wata na'urar imbata ta zamani mai sauya karfin lantarkin batirin mota (12 volt) zuwa irin na cikin gida (240 volt) cikin sauki. 😳

An kori Volker Perthes, jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan.Cikin wata sanarwa da Janar Muhammed A...
02/07/2022

An kori Volker Perthes, jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan.

Cikin wata sanarwa da Janar Muhammed Al-Qali Ali Youssef na gwamnatin soja ta Sudan ya sanya wa hannu, gwamnatin Sudan ta ba Mista Volker Perthes sa'a 72 ya bar kasar daga lokacin da aka rubuta takardar.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta fara sayar wa jama'a filaye kan Naira 500,000 a sabuwar Unguwar Millennium City da ke...
02/07/2022

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta fara sayar wa jama'a filaye kan Naira 500,000 a sabuwar Unguwar Millennium City da ke gabashin birnin Kaduna.

📸 Inside Kaduna

Sudan - Yadda wasu matasa s**a gabatar da Sallar Juma'a a harabar asibitin al Quda da ke birnin Khartoum, yayin da suke ...
02/07/2022

Sudan - Yadda wasu matasa s**a gabatar da Sallar Juma'a a harabar asibitin al Quda da ke birnin Khartoum, yayin da suke zanga-zangar nuna bacin rai ga gwamnatin mulkin sojin kasar.

Kasuwar danyen kifi a garin Akubu da ke Jihar Jongli ta Sudan ta Kudu.
02/07/2022

Kasuwar danyen kifi a garin Akubu da ke Jihar Jongli ta Sudan ta Kudu.

Matsanancin matakin tsaro. 🤔
30/06/2022

Matsanancin matakin tsaro. 🤔

Wane ne ya gane wannan shahararren dan wasan kwallon kafan?Satar amsa - Ba Jay Jay Okocha ne ba! 😆
29/06/2022

Wane ne ya gane wannan shahararren dan wasan kwallon kafan?

Satar amsa - Ba Jay Jay Okocha ne ba! 😆

Wannan shi ne Adam Muhammad, maniyaci dan kasar Iraqi wanda ya isa Makkah daga Ingila a kafa, inda ya tsallaka kasashe 1...
29/06/2022

Wannan shi ne Adam Muhammad, maniyaci dan kasar Iraqi wanda ya isa Makkah daga Ingila a kafa, inda ya tsallaka kasashe 11 cikin kusan watanni 11 domin ya yi aikin Haji.

Ya baro Ingila ne tun watan Agustan bara.

Yadda ake girbin dabino a kasar Oman.Kakar dabino ta iso a Oman, kuma manoma sun dukufa domin girbe shi zuwa kasuwannin ...
29/06/2022

Yadda ake girbin dabino a kasar Oman.

Kakar dabino ta iso a Oman, kuma manoma sun dukufa domin girbe shi zuwa kasuwannin cikin gida da na waje.

📸 I love Muscat

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalan tarayyar Najeriya a ranar Litinin din nan a Fadar...
27/06/2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon alkalin alkalan tarayyar Najeriya a ranar Litinin din nan a Fadar Ado Rock.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola, dan asalin Jihar Oyo, shi ne ke bi wa alkalin alkalan Najeriya Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad baya.

Ya kuma ya sha rantsuwa tare da karɓar ragama a matsayin mukaddasshin alkalin alkalan Najeriya sakamakon murabus din da Mai shari’a Tanko yayi ta bazata da safiyar ranar Litinin 27 ga Yunin 2022.

Rahotannin da muka samu na cewa babban mai shari'a a Kotun Kolin Najeriya Tanko Muhammad ya ajiye mukaminsa.Mai shari'ar...
27/06/2022

Rahotannin da muka samu na cewa babban mai shari'a a Kotun Kolin Najeriya Tanko Muhammad ya ajiye mukaminsa.

Mai shari'ar ya sauka daga mukamin nasa ne saboda dalilai na rashin lafiya.

Address

Mambolo Street, Wuse Zone 2
Abuja
900281

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausaland posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Ilimi gishirin zaman duniya

Kafar zamani domin al’umar Hausawa na yau, da na jiya, da ma ‘yan shekaran jiya!

Ku ziyarci shafinmu na intanet domin ilmantarwa da nishadantarwa.

#Hausaland - Dominku ne, Takuce!