DC Hausa

DC Hausa DC Hausa amintacciya kuma sahihiyar kafar samar da labarai da rahotanni da hirarraki masu ilimantarwa. A tuntuɓemu ta WhatsApp+234 707 799 2833
(2)

Mazauna karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a, domin nuna adawa da yawaitar...
11/09/2026

Mazauna karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a, domin nuna adawa da yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane a yankin.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto da su dauki matakan gaggawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sun kuma nemi a kara yawan jami’an tsaro da kayan aiki, tare da inganta sintiri, sa ido da tattara bayanan sirri domin dakile hare-haren.

Mazauna yankin sun ce rashin tsaron na haifar da fargaba tsakanin manoma da ’yan kasuwa, tare da barazana ga noma da sauran harkokin tattalin arziki.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro na sane da halin da ake ciki kuma suna daukar matakan da s**a dace domin kare rayuka da dukiyoyi.

Hukumar kare haƙƙin masu saye ta Jihar Kano (KCPC) ta rufe wani shagon maganin gargajiya mai suna Kashiful Alim, da ke k...
11/09/2026

Hukumar kare haƙƙin masu saye ta Jihar Kano (KCPC) ta rufe wani shagon maganin gargajiya mai suna Kashiful Alim, da ke kan titin Zoo Road a Kano.

Bayanin haka na ɗauke ne cikin sanarwar da Jamilu Mustapha Yakasai, jami'in hukumar ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook na hukumar.

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne biyo bayan wani ƙorafi da wani ɗan ƙasa ya shigar.

A halin yanzu, jami’an KCPC na gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da ya jawo ƙorafin.

Hukumar ta kuma ce za ta sanar da jama’a sakamakon binciken da halin da ake ciki da zarar an kammala binciken.

Sarkin Zazzau kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, Ambasada Ahmed Bamalli ya goyi bayan shirin ƙara albashi d...
11/09/2026

Sarkin Zazzau kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, Ambasada Ahmed Bamalli ya goyi bayan shirin ƙara albashi da alawus-alawus na sarakunan gargajiya a jihar da kashi 100.

Sarkin ya ce karin albashin zai zama babban sauƙi ga sarakunan, ganin yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa da kuma raguwar darajar Naira.

Ambasada Bamalli ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa da ke Zariya.

Ya ce shirin karin albashin ya shafe kusan watanni bakwai ana shirya shi, inda Gwamna Uba Sani da Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarauta, Sadiq Mamman-Lagos, ke aiki domin ganin an aiwatar da shi.

Sarkin ya yaba wa gwamnatin jihar kan kulawa da haɗin gwiwar da take bai wa masarautun gargajiya, yana mai cewa sarakuna ba ’yan siyasa ba ne, amma suna taka muhimmiyar rawa wajen warware rikice-rikice, samar da zaman lafiya da kuma gudanar da harkokin al’umma.

Ya kuma bayyana cewa Masarautar Zazzau ta warware fiye da ƙararraki 2,000 ta hanyar tsarin sasanci cikin shekaru biyu da s**a gabata.

A cewarsa, tsarin ya taimaka wajen rage yawan ƙararrakin da ke zuwa kotunan gwamnati, inda fadar ke karɓar matsakaitan ƙararraki biyar a kowace rana daga Litinin zuwa Alhamis.

Matatar man Dangote ta yi gargaɗin cewa sake dawo da tallafin man fetur ko kuma kayyade farashin mai na iya rage ribar d...
11/09/2026

Matatar man Dangote ta yi gargaɗin cewa sake dawo da tallafin man fetur ko kuma kayyade farashin mai na iya rage ribar da take samu tare da kawo cikas ga hasashen kuɗaɗen shiga na kamfanin.

Matatar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar bayanai da ta gabatar dangane da shirin fitar da hannayen jarinta ga jama’a (IPO).

Kamfanin ya ce yawan kuɗaɗen shigar sa da ribar da yake samu sun dogara ne kai tsaye da farashin da yake iya sayar da man da ya tace.

A cewar kamfanin, rashin tabbas kan manufofin gwamnati game da tallafin man fetur na iya kawo matsala wajen tsara harkokin kasuwanci da kuma hasashen kuɗaɗen shiga a nan gaba.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nadin sabbin kwamishinoni, shugabannin hukumomi da kuma wasu manyan ...
11/09/2026

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nadin sabbin kwamishinoni, shugabannin hukumomi da kuma wasu manyan masu taimaka masa domin ƙara saurin aiwatar da manufofin ci gaban gwamnatinsa.

Sabbin kwamishinonin da aka nada sun haɗa da Ben Kure a matsayin Kwamishinan Raya Wasanni, Amina Akilu Dalhat a matsayin Kwamishinar Harkokin Musamman I, da Abdullahi Garba Abbas a matsayin Kwamishinan Harkokin Musamman II. Haka kuma an naɗa Dr. Halliru Soba a matsayin Mataimakin Babban Hafsan Ma’aikatan Gwamna mai kula da Harkokin Gudanarwa.

Gwamnan ya kuma naɗa sabbin shugabannin hukumomi, ciki har da Alhaji Munir Jafaru (Hukumar Lafiya ta Kaduna), AVM Bashir Gamagira Saidu (Hukumar Vigilance), Justice Gideon Isa Kurada (Rtd) (Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya), Esther Bago (Cibiyar Horar da Sana’o’i), Dr. Yusuf Aliyu Bature (Hukumar Samar da Kayan Asibiti), da Engr. Namadi Musa (Hukumar Hanyoyin Karkara ta Kaduna).

Gwamna Uba Sani ya ce an zaɓi waɗannan mutane ne bisa ƙwarewa, gaskiya da jajircewarsu, tare da umartar su da su yi aiki da sabon tunani domin cika burin gina Kaduna mai ci gaba da ɗorewar tattalin arziki.

An yi jana'izar hadimin Gwamnan Kano da ya rasu a hadarin tirelaAn yi jana'izar Alhaji Sani Muhammad Hotoro, wanda aka f...
11/09/2026

An yi jana'izar hadimin Gwamnan Kano da ya rasu a hadarin tirela

An yi jana'izar Alhaji Sani Muhammad Hotoro, wanda aka fi sani da Dan Sani, Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan ƙungiyoyi, bayan ya rasu a wani hatsarin tirela.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne ranar Alhamis a kan titin Hotoro Eastern Bypass, kusa da gidan man Gade-Gade.

An ce Dan Sani ya rasu tare da ɗaya daga cikin ma’aikatansa, inda shaidu s**a bayyana cewa ya mutu ne a wurin da hatsarin ya afku.

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari saboda zargin rashin tura wasu ku...
11/09/2026

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari saboda zargin rashin tura wasu kudaden da ake cirewa daga albashin mambobinta da kuma gazawar gwamnati wajen cikakken aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a 2025.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, bayan taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) ta ƙungiyar da aka gudanar a Jami’ar Abuja.

Piwuna ya zargi gwamnatin tarayya da na jihohi da rashin cikakken aiwatar da yarjejeniyar FGN-ASUU ta Disamba 2025.

Ya ce malamai na fuskantar rashin tabbas kan lokacin da za a biya albashinsu da kuma adadin abin da za a biya a kowane wata.

Ya yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa da za su magance matsalolin jin daɗin malaman jami’o’i ba, ASUU ba za ta ɗauki alhakin matakin kiran mambobinta zuwa yajin aikin ƙasa baki ɗaya cikin kankanin lokaci ba.

A cewar Piwuna, wasu jihohi da s**a haɗa da Abia, Bauchi, Ekiti, Ogun, Benue, Yobe, Adamawa, Kebbi, Katsina da Borno sun fara aiwatar da yarjejeniyar 2025, yayin da wasu s**a yi alkawarin fara aiwatar da ita a watan Satumba ko Oktoba.

Shugaban ASUU ya kuma bayyana damuwa kan albashin watanni uku da rabi da har yanzu ba a biya malaman jami’o’i ba, daga cikin watanni bakwai da rabi da aka riƙe a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta biya albashin watanni huɗu daga cikin bashin, amma rashin biyan sauran kuɗin na ci gaba da jefa malaman cikin matsalar kuɗi da taɓarɓarewar tunani.

ASUU ta kuma nuna damuwa kan kudaden fansho, ƙungiyoyin haɗin gwiwar ma’aikata da kuma kuɗaɗen rajistar ƙungiyar da ake cirewa daga albashin mambobinta, waɗanda ta ce ba a tura su yadda ya kamata tsawon watanni.

Piwuna ya ce ƙungiyar ba za ta ci gaba da kallon yadda tsaiko na ofisoshin gwamnati ke raunana harkar ilimi da jami’o’in ƙasar ba.

Ƴan Birni wa ya fi sanarwa da al'ummar karamar hukumar Birnin Kano romon demokradiyya?Me za ku ce?
11/09/2026

Ƴan Birni wa ya fi sanarwa da al'ummar karamar hukumar Birnin Kano romon demokradiyya?

Me za ku ce?

Wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, ya ce Atiku Abubakar ba zai iya dawo da tall...
11/09/2026

Wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, ya ce Atiku Abubakar ba zai iya dawo da tallafin man fetur ba.

‎Sheikh Musa ya ce Atiku yana da damar ya fito ya yi kamfen, amma maganar cewa zai dawo da tallafin man fetur ba gaskiya ba ce.

‎Ya ce a zaɓen 2023 ya yi wa Atiku kamfen a kusan jihohi 20, amma bayan zaɓen ba ta sake samun wata alaƙa tsakaninsu ba.

‎Malamin ya ce bayan rasuwar mahaifiyarsa, Atiku ya nemi lambar wayarsa ta hannun wasu daga cikin ’yan uwansa, amma tun da ya karɓa bai taɓa kiransa ba, har ma a lokacin Ramadan.

11/09/2026

📢 SANARWA GA MASU SHA’AWAR KARATUN AIKIN JINYA

Belba College of Health Sciences Hadejia ta sanar da fara sayar da fom ɗin neman shiga karatun HND Nursing (Jinya) na shekarar 2026.

🩺 Idan kana da sha’awar karatun aikin jinya kuma kana cika sharuddan shiga, wannan wata dama ce da bai kamata ka bari ta wuce ba.

📌 Belba College of Health Sciences, Hadejia – Jihar Jigawa.

👉 Don ƙarin bayani kan sharuɗɗan shiga, da yadda ake samun fom, ku tuntubi makarantar kai tsaye.

📍 Address: Abattoir Road, bayan Hadejia Jama’are, Hadejia, Jihar Jigawa.

08032127767

07044116060

Ko ta shafin internet www.belbacollage.edu.ng

Address

Abuja
123

Telephone

+2348183350725

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DC Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DC Hausa:

Shortcuts

Share