
25/12/2023
EFCC ta bankado wasu makudan kudade da s**a kai biliyan 37 da ake zargin an wawure a ma’aikatar jin kai a karkashin tsohuwar Minista Sadiya Umar-Farouk.
Sadiya Umar-Farouk tana cikin majalisar ministocin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
A shekarar 2020, hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) karkashin jagorancin Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana cewa hukumar ta bankado Naira biliyan 2.67 na asusun sirri, wanda ake biyan wasu kwalejojin gwamnatin tarayya don ciyar da makarantu yayin da jama'a suke gida saboda COVID-19
Tsohon shugaban ICPC ya ci gaba da cewa an biya kudin ne lokacin da yara ba sa makaranta.
Sai dai duk da bukatar da kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa ta bukaci Sadiya Umar-Farouq da ta buga bayanai da sunayen wadanda ake zargin, amman tsohuwar ministar ta kasa bayyana sunayensu.