Tambarin Gaskiya

Tambarin Gaskiya Tambarin Gaskiya Wata Kafa Ce Da Zata Rika Kawo Sahihan Labarai Da Bunkasa Al'adu da Dabiun Hausawa Na Gargajiya

Tambarin Gaskiya is a leading innovative media company that informs and engages Africa's audience and provides expansive media reach and creative marketing solutions to our partners.

04/05/2025

Kashi na Biyu na Tattaunawa ta Musamman tare da Dr. Sirajo Yakubu a Tambarin Gaskiya.

Dr. Sirajo Yakubu kwararren ɗan siyasa ne, ɗan kasuwa, lauya, kuma Shugaban Sashen Public & International Law a Jami'ar Nile dake Abuja.

26/04/2025

Kashi na Ɗaya na Tattaunawa ta Musamman tare da Dr. Sirajo Yakubu, Esq a Tambarin Gaskiya.

Dr. Sirajo Yakubu kwararren ɗan siyasa ne, ɗan kasuwa, lauya, kuma Shugaban Sashen Public & International Law a Jami'ar Nile dake Abuja.

Dr. Sirajo Yakubu  Ya Bayyana Dalilan Da S**a Sa Ya Mika Slot Ɗinsa Na Supervisory Councillor Ga Hon. Abdulbaki Babban G...
17/04/2025

Dr. Sirajo Yakubu Ya Bayyana Dalilan Da S**a Sa Ya Mika Slot Ɗinsa Na Supervisory Councillor Ga Hon. Abdulbaki Babban Gawo a Batagarawa ‘A’ Ward

Batagarawa, Katsina – Dr. Sirajo Yakubu ya bayyana cewa ya yanke shawarar mika damar sa ta zama Supervisory Councillor a mazaɓar Batagarawa ‘A’ Ward ga tsohon Kansila, Hon. Abdulbaki Babban Gawo, bisa dalilai masu muhimmanci da s**a shafi biyayya, adalci, da haɗin kai a harkokin siyasar ƙaramar hukuma.

A cewar Dr. Sirajo, daya daga cikin manyan dalilan wannan mataki shi ne biyayya ga umarnin maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON. Gwamnan ya bukaci cewa duk wani shugaban ƙaramar hukuma ko Kansila da ya nemi takara bai samu ba, amma ya bada gudunmuwa har aka kai ga nasara ba tare da jin haushi ba, a ja shi a jiki a ba shi dama. Dr. Sirajo ya ce Hon. Abdulbaki ya cika wannan sharadi, inda ya nuna biyayya da kwazo tun daga farko har zuwa ƙarshen wannan hidimar siyasa a Batagarawa.

Dalili na biyu da Dr. Sirajo ya gabatar shi ne kokarinsa na tabbatar da adalci a wakilcin al’umma. Ya bayyana cewa mazaɓar Batagarawa ‘A’ na da rumfunan zaɓe guda 29, rabinsu suna cikin gari, yayin da rabin kuma ke waje. Yace kasancewar Kansilan yanzu ya fito daga cikin gari, ya ga dacewar a baiwa rumfunan waje wakilci a matsayin Supervisory Councillor, domin su ma suna da muhimmanci wajen samar da ƙuri’u da goyon baya a lokacin zaɓe.

"Na yanke wannan shawara ne ba dan son zuciya ba, ko dan yana yaro na ba. Na yi haka domin tabbatar da adalci a tsakanin jama’ar rumfunan cikin gari da na waje, da kuma cika umarnin Gwamna na ganin an haɗa kai a tafiyar siyasa," in ji shi.

A ƙarshe, Dr. Sirajo ya mika godiyarsa ga Gwamnan Katsina bisa jagoranci mai cike da adalci da tausayi, da kuma ga sabon shugaban ƙaramar hukumar Batagarawa, Hon. Yahaya Lawal Kawo, bisa baiwa sa wannan dama. Ya kuma sake tabbatar da alkawarin sa na ci gaba da bada gudunmuwa ga gwamnatin jihar da ƙaramar hukuma bisa ƙaunar da Gwamna Dikko ke nuna masa.

Ya kuma yi godiya ga al’ummar Batagarawa bisa goyon baya da addu’o’i, tare da kira da a ci gaba da yiwa shugabannin addu’a domin samun nasara.

A Tribute to Hajiya Safara’u: A Mother of Grace and VirtueLate Hajiya Safara’u Umaru Barebari Radda, the beloved mother ...
24/03/2025

A Tribute to Hajiya Safara’u: A Mother of Grace and Virtue

Late Hajiya Safara’u Umaru Barebari Radda, the beloved mother of Katsina State Governor, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, PhD, CON, was more than just a mother, she was a beacon of love, strength, and unwavering devotion. Her kindness knew no bounds, her prayers never ceased, and her heart embraced not only her children but everyone who crossed her path. She raised her family on the pillars of humility, integrity, respect, and service to humanity, leaving behind a legacy of goodness that will outlive generations.

Even in her final days, as illness weakened her body and made speech difficult, her spirit remained unshaken. Lying on her sickbed, she never stopped praying. Her love for her son extended to all who were associated with him. The moment a visitor was introduced as Gwagware’s friend or associate, her frail voice would rise in supplication, praying for their success, their protection, and the prosperity of their families. Malam Dikko, fondly called ‘Gwagware’ by his family, was her pride and joy. It was as if the mere mention of his name rekindled her strength, allowing her to pour out endless blessings. She would not stop until the visitor prepared to leave, at which point, she would reluctantly rest, her heart still whispering prayers. Such was the depth of her love, the purity of her soul.

Fate, however, had its own plans. She departed this world while her son was thousands of miles away in Mecca for Umrah. Despite their unbreakable bond and his position as a sitting governor, Malam Dikko refused to use public resources to secure a chartered flight to return home for her burial. He made the painful sacrifice of missing his mother’s final moments, choosing instead to uphold the values she had instilled in him. He waited patiently for a seat on a commercial flight, accepting the heartbreak of not being there, all in honor of the principles she had taught him, integrity, humility, and accountability.

Even in death, she inspired one final lesson: that true greatness lies in selflessness. Malam Dikko’s decision to let the funeral rites proceed in his absence was a testament to his deep respect for family hierarchy. He deferred to his elder brother, the traditional ruler of Radda District, allowing him to lead the family in their time of grief. Where power could have disrupted traditions, he chose humility, proving that leadership is not about position but about values.

Late Hajiya Safara’u did not just raise children; she nurtured greatness. She was a mother in every sense of the word, selfless, prayerful, and full of boundless love. Today, the people of Katsina State, and indeed, Nigeria mourn her passing. Yet, even in grief, they celebrate the remarkable life she lived, the virtues she upheld, and the prayers she left behind.

May Allah, in His infinite mercy, grant her Jannatul Firdaus and make her resting place one of peace and light. Ameen.

Tribute By Dr. Sirajo Yakubu, Esq.

An rasa rayuka a jihar Neja bayan matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan....
01/08/2024

An rasa rayuka a jihar Neja bayan matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.

Aƙalla mutane shida ne s**a rasa rayukansu yayin da ƴan sanda s**a yi ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zangar da s**a toshe hanya.

Daga cikin mutanen da aka harba har da wani bawan Allah mai suna Yahaya Nda Isah, wanda ke tafiya a kan baburinsa.

Gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar hana fita na tsawon awanni 24 domin dakile barna da ake yi.Gwamna Abba Kabir ya tabba...
01/08/2024

Gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar hana fita na tsawon awanni 24 domin dakile barna da ake yi.

Gwamna Abba Kabir ya tabbatar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a gidan gwamnati

Gwamnan ya ce wannan dokar ita ce mafita don dakile cigaba da barnar da ake yi da lalata dukiyoyin al'ummar jihar.

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana matsayarsa kan shirin zanga-zanga da matasa ke y...
29/07/2024

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana matsayarsa kan shirin zanga-zanga da matasa ke yi. Obi ya jaddada cewa hakkinsu ne na 'yan kasa su gudanar da zanga-zanga, kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama a Najeriya.

Jigon jam'iyyar LP ya ce ya kamata shugabanni su yi gaggawar kawo mafita a Najeriya, duba da halin kunci da ake ciki a kasar.

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya fitar da bayani game da matsalar karancin man fetur da ta addabi Legas da Abuja.NNP...
29/07/2024

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya fitar da bayani game da matsalar karancin man fetur da ta addabi Legas da Abuja.

NNPC ta bayyana cewa wannan karancin ya jawo gidajen man suna sayar da fetur a farashi mai tsada fiye da wanda NNPC ke sayarwa. Tambarin Gaskiya ta gano cewa 'yan kasuwar bumburutu suna sayar da litar fetur sama da Naira 1,000 a wasu sassan kasar.

29/07/2024

[Vidio] Bello Turji ya yi wata magana Dake da alamar tambaya.

An yi kira ga matasa masu shirin yin zanga-zanga da su janye tare da ba gwamnati goyon baya wajen samar da ababen more r...
28/07/2024

An yi kira ga matasa masu shirin yin zanga-zanga da su janye tare da ba gwamnati goyon baya wajen samar da ababen more rayuwa.

Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi wannan kiran a lokacin da yake kaddamar da wani shiri na "Operation Free Our Roads" a Abuja.

Mista Umahi ya yi ikirarin cewa da yanzu Najeriya ta lalace idan ba don ubangiji ya sa Bola Tinubu ne shugaban kasa a yanzu ba.

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku bayan wani gini mai hawa biyu ya rufta kansu a garin G...
28/07/2024

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku bayan wani gini mai hawa biyu ya rufta kansu a garin Gujungu, karamar hukumar Taura. Lamarin ya afku ne da misalin karfe 10 na safe yau Asabar. Haka kuma, an samu jikkatar wasu mutum huɗu daga karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, waɗanda suke samun jinya a asibitin Jahun.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya miƙa ta'azziyarsa ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu, tare da addu'ar Allah ya gafarta musu.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu bai karɓi wata wasika kan buƙatar amfani da danda...
28/07/2024

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu bai karɓi wata wasika kan buƙatar amfani da dandalin Eagle Square ba domin zanga-zangar da aka shirya fara wa ranar 1 ga watan Agusta.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a babban birnin tarayya ranar Asabar, gabanin zanga-zangar da aka yi wa lakabi da "Zanga-zangar Adawa da Tsadar Rayuwa". Ya jaddada cewa babu wata wasika da aka aika wa ofishinsa domin amfani da dandalin Eagle Square.

Ministan ya yi kira ga masu niyyar yin zanga-zanga da su guji amfani da kafafen sada zumunta kawai wajen aika sako zuwa ofishinsa, amma su bi hanyoyi da s**a kamata wajen yin hakan.

Tun da farko, Wike ya yi gargadi kan shirya zanga-zangar. "Ga waɗanda ke son yin zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta, babu wurin yin hakan a babban birnin tarayya," in ji shi. Ya kuma gargaɗi masu shirya zanga-zangar da su guji yin hakan.

Address

Abuja
900103

Telephone

09052875145

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tambarin Gaskiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tambarin Gaskiya:

Share