16/10/2025
Shugaban Iran Ya yi Gargadi ga Makircin Maƙiya
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce maƙiyan ƙasarsu koyaushe suna neman ɓarkewar rigima a tsakanin ƙasashen Musulmi don raunana su. Kalaman na zuwa ne, ne bayan an dakatar da fada tsakanin Pakistan da Afghanistan.
Pezeshkian ya furta wadannan kalaman a wani zaman daki na ranar Laraba yayin da yake bayyana matsayin Iran game da tashe tashen hankulan da ke tsakanin makwabtan kasashen biyu na Musulmi.
Kazalika, ya ce al'ummomin Musulmi ba sa son rikici da sabani, wanda shi ne sakamakon makircin maƙiyan da na sahyoniya na duniya.
Ya kara da cewa, tashe-tashen hankulan da ya barke tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da matukar damuwa a duk ƙasashen yankin, ciki har da Iran, wadda ke da iyaka da ƙasashen biyu.
Al'ummomin Musulmi, musamman waɗanda ke da tushe da al'adu iri ɗaya a yankin, suna da karfin imani da al'adu da ba za a iya karyawa ba, kuma suna da alhakin yin aiki tare a jiki ɗaya don inganta zaman lafiya adalci, da ci gaba, in ji Pezeshkian.
Ya nanata cewa Iran za ta yi amfani da duk wata hanya da za ta iya da kuma yin iya ƙoƙarinta na rage tashin hankali, inganta tattaunawa, da ƙarfafa dangantakar 'yan'uwantaka tsakanin ƙasashen makwabtan biyu. Ya bayyana cewa, tattaunawa da haɓaka alaƙar 'yan'uwa za su taimaka rage tashe tashen hankulan da ke tsakanin Afghanistan da Pakistan.
Yankin yana buƙatar zaman lafiya, haɗin kai, da haɗin gwiwa fiye da kowane lokaci, in ji Pezeshkian, yayin da ya bayyana yakinin cewa gwamnatoci da al'ummomin Afghanistan da Pakistan za su shawo kan matsalolinsu ta hanyar basira.
Noor Al-haq News
16-10-2025.