17/09/2025
Remi Tinubu Ta Yi Addu’a Don Zaman Lafiya a Duniya, Ta Karɓi Jakadan Qatar Don Haɗin Gwiwa a Fannin Ilimi
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a gina duniya bisa zaman lafiya da fahimtar juna, tana roƙon ƙasashe su guji tayar da rikici da yaƙe-yaƙe.
Ta bayyana hakan ne yayin da take karɓar bakuncin Jakadan Qatar a Najeriya, Ali bin Ghanem Al-Hajri, a ofishinta da ke Abuja.
Yayin da take mayar da martani kan harin da aka kai a birnin Doha, babban birnin Qatar, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ce zaman lafiya yana da matuƙar muhimmanci kuma yana kusa da zuciyar Allah. Ta ƙara da cewa dukkan manyan addinai suna koyar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma da ƙasashe.
Taron da aka gudanar a bayan fage ya tattauna sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin shirin Renewed Hope Initiative da Qatar Foundation don ci gaban ilimi, kimiyya da al’umma. An mai da hankali kan inganta tsarin Almajiri da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Jakadan Qatar ya gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa da al’ummar Najeriya bisa goyon baya da addu’o’in zaman lafiya bayan harin da aka kai a Doha, tare da tabbatar da ƙudurin ƙasarsa na ƙarfafa dangantaka da Najeriya.