04/09/2025
Shehu Buba ya tsolewa maƙiyansa ido
Sanatan Bauchi ta kudu, Shehu Buba Umar ya yiwa masu adawa da shi zarra, domin kuwa babu abinda s**a iya sai sharri da bita-da-kulli. Shehu Buba kullum burinsa shi ne kyautatawa alummarsa ta Bauchi ta kudu da yake wakilta.
Sanata Shehu Buba ba shi da wani buri face kyautatawa alummar mutanen Bauchi ta kudu da yake wakilta ta hanyar gwangwaje su da romon demokaraxiyya, wannan ta sanya a Koda yaushe yake kokarin hidima wa mutane ta hanyar rabon kayan arziki da na sana'o'i.
Shehu Buba mutane da kullum burinsa sanya farinciki a zukatan alummar da yake wakilta. Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci yana rabon kayan abinci da babura da injinan noma da sauran kayayyaki domin tallafawa mutanan jihar Bauchi musamman Bauchi ta kudu.
Mutane da yawa suna bin wannan bawan Allah da sharri da kage da kuma kazafi dan kawai ya tsole musu ido. Don haka, dukkan magiya baya da masoyan Sanata Shehu Buba suyi watsi da kalaman balancing da ake jingina masa, da kuma wanda ake yadawa a video dan kawai aci mutuncinsa.
Shehu Buba mutumin kirki ne mai kaunar al'ummarsa da son hidimta musu a ko da yaushe.