ROtv24 Hausa

ROtv24 Hausa News, Interviews, Promotions and Advertisement.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) na sanar da farashin kuɗin Hajj na shekarar 2026.Bayan shawarwari da dukkan masu ruwa d...
27/09/2025

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) na sanar da farashin kuɗin Hajj na shekarar 2026.

Bayan shawarwari da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin jihohi da samun amincewar Gwamnatin Tarayya, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya sanar da farashin Hajj na 2026 kamar haka:

Yankin Maiduguri Yola (Jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya: N8,118,333.67
Sauran Jihohin Arewa za su biya: N8,244,813.67

Jihohin Kudu za su biya: N8,561,013.67

Idan aka kwatanta da abin da aka biya a bara, a bana kowanne ɗan Alhaji zai biya kusan naira dubu dari biyu (₦200,000) ƙasa da na bara.

A halin yanzu, tawagar NAHCON da ke Saudiyya sun gana kuma sun rattaba hannu kan yarjejeniya da Kamfanin Bayar da Hidimar Hajj na shekarar 2026 (Mashareeq Al-Zahabiyya) da kuma Kamfanin Sufuri (Daleel Al-Ma’aleem).

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi, ya yi kira ga dukkan masu niyyar yin Hajj da su kammala biyan kuɗin su kafin ranar 31 ga Disamba, 2025





Labarai: An Karrama Mawaki Rarara Da Digirin Digirgir A European American University An gudanar da babban taro na karram...
20/09/2025

Labarai: An Karrama Mawaki Rarara Da Digirin Digirgir A European American University

An gudanar da babban taro na karrama shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara, inda ya samu lambar girmamawa ta Doctorate Degree daga European American University dake Jamhuriyar Panama.

Wannan digiri an ba shi ne saboda gudummawar da yake bayarwa wajen tallata al’adun Najeriya da kuma zaburar da matasa ta hanyar waƙoƙinsa.

Wani fata zaku masa?

Big shout out to my newest top fans! 💎 Khairat Al'amin, Abk S Pawa, Yunusa Muhammad, Imran Lawal Imam, Munubia HussainiD...
20/09/2025

Big shout out to my newest top fans! 💎 Khairat Al'amin, Abk S Pawa, Yunusa Muhammad, Imran Lawal Imam, Munubia Hussaini

Drop a comment to welcome them to our community, fans

Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashin Daukan Nauyin Tagwaye A Jihar KanoGwamnatin Kano ta karɓi tagwaye ƴan jihar da aka hai...
14/09/2025

Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashin Daukan Nauyin Tagwaye A Jihar Kano

Gwamnatin Kano ta karɓi tagwaye ƴan jihar da aka haifa manne da juna, bayan yi musu tiyata a Saudiyya.

Rohotonin BBC Hausa ta bayyana Cewan, an kai Hassana da Husaina asibitin King Abdullah na yara ne a 2023, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin ɗaukar nauyin yaran.



07/09/2025

Mummunan yanayi ya jawo mutuwar mutum uku a sansanin gudun hijira na jihar Neja. =BBC Hausa

07/09/2025

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS ta buƙaci mahukuntar kafar X da ta rufe shafin ɗan gwagwarmaya, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore cikin awa 24. =BBC

15/07/2025

Yanzu haka an kammala jana'izar Buhari a Daura

15/07/2025

Gawar Buhari ta baro Landan
tana hanyar isowa Najeriya

14/07/2025

Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai a gobe Talata ne za a yi jana'izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

13/07/2025

Tinubu ya umurci Kashim Shettima ya tafi London don taho da gawar tsohon shugaban kasa Buhari zuwa Nijeriya

DA DUMI-DUMI: Allah Ya yiwa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwa.
13/07/2025

DA DUMI-DUMI: Allah Ya yiwa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rasuwa.

13/07/2025

Na bankado manyan kura-kurai tattare da hadakarsu El-Rufai da Atiku, ba ruwana da ADC - Manjo Hamza Almustapha

Address

Abuja
90300

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ROtv24 Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share