Hantsi24

Hantsi24 Jaridar Hantsi24, Jarida ce mai zaman kanta data shahara wajen kawo muhimman labarai da dumi duminsu tare da tsage gaskiya dangane da kowanne al`amari.

GWAMNATIN TARAYYA TA RUFE MAKARANTU KUSAN 50 SABODA DALILAN TSAROMa'aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da rufe wasu makar...
21/11/2025

GWAMNATIN TARAYYA TA RUFE MAKARANTU KUSAN 50 SABODA DALILAN TSARO

Ma'aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da rufe wasu makarantun Sakandare 47, da ke sassan kasar sakamakon yadda ake fama da satar dalibai 'yan makaranta da 'yan bindiga ke yi.

Wata sanarwa da daraktar sashen kula da ilimin makarantun sakandare ta ma'aikatar Binta Abdulkadir ta aiko wa Hantsi24, ta ce an dauki matakin ne don kare daliban.

Ga jerin makarantun da aka rufe a kasa 👇

1. FGGC MINJIBIR
2. FTC GANDUJE
3. FGGC ZARIA
4. FTC KAFANCHAN
5. FGGC BAKORI
6. FTC DAYI
7. FGC DAURA
8. FGGC TAMBUWAL
9. FSC SOKOTO
10. FTC WURNO
11. FGC GUSAU
12. FGC ANKA
13. FGGC GWANDU
14. FGC BIRNIN YAURI
15. FTC ZURU
16. FGGC KAZAURE
17. FGC KIYAWA
18. FTC HADEJA
19. FGGC BIDA
20. FGC NEW-BUSSA
21. FTC KUTA-SHIRORO
22. FGA SULEJA
23. FGC ILORIN
24. FGGC OMUARAN
25. FTC GWANARA
26. FGC UGWOLAWO
27. FGGC KABBA
28. FTC OGUGU
29. FGGC BWARI
30. FGC RUBOCHI
31. FGGC ABAJI
32. FGGC KAZAURE
33. FGC KIYAWA
34. FTC HADEJIA
35. FGGC POTISKUM
36. FGC BUNI YADI
37. FTC GASHUA
38. FTC MICHIKA
39. FGC GANYE
40. FGC AZARE
41. FTC MISAU
42. FGGC BAJOGA
43. FGC BILLIRI
44. FTC ZAMBUK
45. FTC IKARE AKOKO
46. FTC IJEBU-IMUSIN
47. FTC USHI EKITI

DAN NAJERIYAR DA YA ZAMA GWARZON GASAR KARATUN ALQUR'ANI TA DUNIYAWani matashi dan jihar Borno Albashir Goni Usman kenan...
14/03/2021

DAN NAJERIYAR DA YA ZAMA GWARZON GASAR KARATUN ALQUR'ANI TA DUNIYA

Wani matashi dan jihar Borno Albashir Goni Usman kenan wanda ya zama gwarzon gasar karatun alqur,ani ta duniya da aka gudanar a Kenya.

Jihar Borno dai ta yi shuhura ta fuskar karatun aqur'ani mai girma, har ta kai ana ganin duk karatunka in baka je "Gabas" ba to da sauranka.

WUFF TA TABBATA !!!Hotunan kafin aure na wata 'yar shilar budurwa kenan, da wani dattijon angonta da ake fatan daura aur...
14/03/2021

WUFF TA TABBATA !!!

Hotunan kafin aure na wata 'yar shilar budurwa kenan, da wani dattijon angonta da ake fatan daura aurensu nan bada jimawa ba 😂

Muna fatan Allah ya sanya alheri ya kawo kazantar daki.

RIJISTAR APC A KANO TA ZAMA TAKARDAR MASU SAYAR DA KIFI DA KOSAIWannan dai shine yadda masu kifi a jihar Kano ke amfani ...
14/03/2021

RIJISTAR APC A KANO TA ZAMA TAKARDAR MASU SAYAR DA KIFI DA KOSAI

Wannan dai shine yadda masu kifi a jihar Kano ke amfani da rijistar shiga Jam,iyyar APC wajen zuba kifi ga jama,a a jihar

Baya ga wuraren masu kifi, ana iya ganin takardun a wuraren masu kifi da masu nama da kuma masu kosai.

Wannan na zuwa ne yayin da jam,iyyar ke cewa adadin wadanda s**a yo rijista a jihar ya matukar zarce yawan wadanda s**a zabi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

TURKASHI !An samu iska mai ƙarfin gaske a birnin Riyadh na ƙasar Saudiya cikin daren Juma,a.
13/03/2021

TURKASHI !

An samu iska mai ƙarfin gaske a birnin Riyadh na ƙasar Saudiya cikin daren Juma,a.

10/03/2021

YADDA WASU YAN KAROTA S**A NEMI HALLAKA WANI DIREBAN A DAIDAITA SAHU KE NAN A KANO...

KOTU ZANKAI KARAR YAN JARIDU- ZAHRA BUHARI NDIMIYar gidan Shugaban kasa Buhari Zahra Buhari, ta bayyana cewar batun zanc...
10/03/2021

KOTU ZANKAI KARAR YAN JARIDU- ZAHRA BUHARI NDIMI

Yar gidan Shugaban kasa Buhari Zahra Buhari, ta bayyana cewar batun zancen badakalar nan ta Naira Biliyan 51 da cewar zata kai karar yan jaridun da s**a wallafa labarin badakalar nan da ake zargin wai da ita a ciki da ta hadar da wasu manya a Hukumar kwastam, da kuma wani babban kusa a Jam'iyya mai mulkin ta APC mai sunan DANU.

Me nene ra'ayinku

AN SANYA ALHAMIS DA JUMA'A KADAI A MATSAYIN RANAKUN ZUWA ZANCE A KANO. Dagacin garin Tudun Yola dake Kano Malam Nasidi H...
09/03/2021

AN SANYA ALHAMIS DA JUMA'A KADAI A MATSAYIN RANAKUN ZUWA ZANCE A KANO.

Dagacin garin Tudun Yola dake Kano Malam Nasidi Hamisu ya bayyana dokoki guda hudu da ya ce ya zama dole al’ummar yankin su bi domin tsaftace garin daga muggan ayyuka.

Dokar ta shafi zawarawa da yan mata da kuma samari, inda dokar tace daga yanzu ranakun Alhamis da Juma'a ne kawai na zance a yankin, wanda kuma ya saba haka doka zata yi aiki akan sa.

KA IYA BAKINKA ! — RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA GA SHEIKH GUMI.Rundunar sojin Najeriya ta gargadi fitaccen malamin addinin mu...
09/03/2021

KA IYA BAKINKA ! — RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA GA SHEIKH GUMI.

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, a kan kalaman da ya furta na cewa wasu sojoji kiristoci ne ke kashe yan fashin daji saboda kabilanci.

A cewar rundunar kalaman malamin na iya haifar da rikici, don haka ba za ta lamince su ba.

Dama malamin ya taba cewa sojoji basa son a kawo karshen rikicin yan fashin daji, saboda suna amfana da shi, kalaman da ake ganin na iya fusata su.

KANNYWOOD: ASHIRU NAGOMA YA SAMU SAUKIDarakta Ashiru Nagoma daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, ya samu sa...
09/03/2021

KANNYWOOD: ASHIRU NAGOMA YA SAMU SAUKI

Darakta Ashiru Nagoma daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, ya samu sauki bayan shafe tsawon watanni biyu a asibiti ya jinya.

Daraktan dai ya dauki tsawon lokaci yana fama da ciwo da ya shafi Kwakwalwa, amma wasu na ganin cewa tabin hankali ya samu, wasu daga cikin 'yan uwansa kuma na ganin, jifa ne a ka masa.

A watan Janairun da ya gabata ne, marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman, karkashin jagorancin gidauniyarta ta tallafawa marasa karfi, s**a dauki nauyin yi masa magani a asibiti.

Tun daga wannan lokaci aka kai shi asibiti inda likitoci s**a shiga kula da shi.

Labaran Kannywood sun wallafa hotunan daraktan tare sa Fauziyya D. Sulaiman, a shafinsu na twitter bayan sallamo shi daga asibiti, cikin yanayi mai kyau.

Sheikh Abduljabar?  Turkashi!Wadannan littattafan ne Sheikh Abduljabbar ya shirya zuwa Mukabala da su ba don kotu ta han...
09/03/2021

Sheikh Abduljabar? Turkashi!

Wadannan littattafan ne Sheikh Abduljabbar ya shirya zuwa Mukabala da su ba don kotu ta hana ba.

MATASA MANYAN GOBEMatashi Khalil Nur Khalil kenan dan shekara 28 a duniya, wanda shine sabon Darakta a hukumar tattara b...
09/03/2021

MATASA MANYAN GOBE

Matashi Khalil Nur Khalil kenan dan shekara 28 a duniya, wanda shine sabon Darakta a hukumar tattara bayanan zuba jari ta jihar Kaduna wato (KADIPA).

Wani abin ban sha'awa shine ya taba zama shugaban riko na sashen kyautata alakar masu zuba jari a hukumar tun kafin ya kai wadannan shekaru.

Address

Mai Tama
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hantsi24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hantsi24:

Share