Aminiya

Aminiya Sahihin Shafin Jaridar Aminiya. Jaridar Hausa Ta Rukunin Kamfanin Media Trust; Mamallakin Jaridar Daily Trust, Trust TV Da Kuma Trust Radio.
(400)

Burinmu shi ne: Zama wata babbar kafar yada labarai a duniya wadda za ta samu amincewar jama'a. Bayani kan kamfanin da ke wallafa Aminiya:
Kamfanin Media Trust da ke Abuja ne ya ke wallafa jaridar Aminiya da shafukan Aminiya na intanet. Shi ne kuma ya ke buga jaridar Daily Trust, da Daily Trust on Saturday, da Daily Trust on Sunday, da kuma shafukan intanet na Daily Trust. Adireshin Hedikwatar Kamfanin:
Lamba 20, P.O.W. Mafemi Crescent, Gundumar Utako, Abuja.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa ...
09/08/2025

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka.

Ƙungiyar ta ce idan gwamnati ta gaza cika alƙawuran da ta ɗaukar musu, za su koma yajin aiki.

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin ...
09/08/2025

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno.

Abu Nasr ne ya jagoranci kai hari garin Rann a makon da ya gabata.

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba.
09/08/2025

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba.

Jarumar ta shammaci mutane tare da yin aure a lokacin da ba zato ba tsammani.

09/08/2025

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da s**a rasu.

Ɗan uwan Jaruma Rahama Sadau ya ƙara da cewa jarumar ta yanke shawarar aure ne tun bayan rasuwar mahaifinsu wanda ya so ...
09/08/2025

Ɗan uwan Jaruma Rahama Sadau ya ƙara da cewa jarumar ta yanke shawarar aure ne tun bayan rasuwar mahaifinsu wanda ya so ace sun yi auren tun yana raye.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar tsohon shugaban ...
09/08/2025

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.

Ogbeh ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗ...
09/08/2025

Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara.

Kotun ta yanke mata hukuncin ne bayan samun ta da laifin aikata damfara.

Iyalan Cif Audu Ogbeh sun sanar cewa a safiyar Asabar Allah Ya yi masa cikawa, yana da shekara 78 a duniya.Iyalansa sun ...
09/08/2025

Iyalan Cif Audu Ogbeh sun sanar cewa a safiyar Asabar Allah Ya yi masa cikawa, yana da shekara 78 a duniya.

Iyalansa sun sanar cewa a safiyar Asabar Allah Ya yi masa cikawa, yana da shekara 78 a duniya.

Rahotanni na bayyana cewa an ɗaura auren jaruma Rahama Sadau a Kaduna a yau Asabar.Wasu makusantan ta sun tabbatar da da...
09/08/2025

Rahotanni na bayyana cewa an ɗaura auren jaruma Rahama Sadau a Kaduna a yau Asabar.

Wasu makusantan ta sun tabbatar da daura auren a masallacin Masallacin Atiku Auwal Unguwan Rimi, tare da angonta Ibrahim Garba.

An ɗaura auren ne kan sadaki Naira 300,000.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne mutum mafi dacewa da...
09/08/2025

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne mutum mafi dacewa da Jam'iyyar PDP za ta iya tsayarwa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Sule Lamiɗo ya buƙaci jam'iyyar da ta dawo da Jonathan, domin babu wani ɗan jam'iyyar PDP a yankin Kudu da ya kai ƙwarewar Jonathan.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake ƙoƙarin shawo kan Jonathan a PDP domin ya dawo a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen 2027.

Address

20 P. O. W Mafemi Crescent, Utako District
Abuja
900001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminiya:

Share