Citizenship HAUSA

Citizenship HAUSA Takenmu: 'Yanci, Adalci, Cigaba...
(2)

Manufarmu ita ce wayar da kan jama’a kan hakkin ɗan ƙasa da nauyin da ke kansa, da kuma yadda za a rayu cikin zaman lafiya, adalci da haɗin kai a cikin al’umma tare da yadda zai samu cigaba da nasara a rayuwarsa.

23/07/2025

Wane rubutu kuke so mu dinga saka muku wannan satin?

🏆 Jerin Masu Himma na Mako (Weekly Engagement List) 🏆Muna taya murna tare da yaba wa waɗanda s**a fi ba da gudummawa a w...
22/07/2025

🏆 Jerin Masu Himma na Mako (Weekly Engagement List) 🏆

Muna taya murna tare da yaba wa waɗanda s**a fi ba da gudummawa a wannan makon a shafin mu Citizenship HAUSA! 👏

🥇 Mannir S Kaura — 330 maki
🥈 Sharu Dan-momcy — 188 maki
🥉 Isah Ibrahim — 127 maki

Kuna da jajircewa da kishin da ya cancanci yabo! 👏👏👏

💬 Albishirinku!
Idan kuka ci gaba da nuna wannan ƙwazo, akwai girmamawa da kyaututtuka na musamman da za su biyo baya in sha Allah! Wannan dama ce ta zama gwarzo/gwarzuwar wannan tafiya mai albarka.

🔔 Ku ci gaba da:
✅ Yin comment mai amfani
✅ Yin share da like
✅ Kiran wasu su biyo shafin
✅ Taimakawa wajen bada shawarwari

Muna tare da ku domin gina al'umma mai wayewa da ƙima!

21/07/2025

Gaskiya daya ce, Dimokradiya ba zata gyara Nigeria ba in ba da dokokin Allah ba.

GYARAN HALAYYA – MUTUM NE KASA, BA GINE-GINE BANajeriya za ta yi kyau ne idan halayen ‘yan Najeriya sun gyaru. Idan muka...
17/07/2025

GYARAN HALAYYA – MUTUM NE KASA, BA GINE-GINE BA

Najeriya za ta yi kyau ne idan halayen ‘yan Najeriya sun gyaru.
Idan muka gyara zuciya, dokoki ba za su sha wahala ba.

🗣️ Kai fa, wane hali ne da ka lura yana lalata Najeriya fiye da komai? Me za mu yi don mu gyara shi a kai a kai?

GYARAN RAYUWAR MATASA – SU NE GOBEMatasa sune gobe, amma idan gobe ta lalace yau, to babu makoma. Muna bukatar matasa ma...
17/07/2025

GYARAN RAYUWAR MATASA – SU NE GOBE

Matasa sune gobe, amma idan gobe ta lalace yau, to babu makoma. Muna bukatar matasa masu ilimi, halaye, da hangen nesa.
Duk wanda ya gyara matasa — ya gyara ƙasa.

🗣️ A matsayinka na matashi ko uwa/uba, wane abu kake ganin zai fi tasiri wajen gyaran rayuwar matasa? Mu hadu a comment section.

GYARAN YAN JARIDU – KAFOFIN LABARI SU DAINA RUDA AL’UMMAYadda kafafen watsa labarai ke bayar da rahoto yana tasiri sosai...
17/07/2025

GYARAN YAN JARIDU – KAFOFIN LABARI SU DAINA RUDA AL’UMMA

Yadda kafafen watsa labarai ke bayar da rahoto yana tasiri sosai a kan tunanin mutane. Idan labarai sun zama na son rai da kage, wane gyara muke tsammani?
Gaskiya ta fi tsoro. Jarida ta gaskiya – gidauniyar gyaran kasa ce, amma akasin haka lalata kasa ce.

🗣️ A ra’ayinka, kafofin labarai a Najeriya suna taimakawa wajen gyara ko suna ƙara rikita al’umma? Me yasa?

GYARAN TSARI – TSAFTACE DOKOKI DA AIKI NA NAJERIYAAkwai dokoki masu kyau a Najeriya, amma ba su aiki. Tsarin da ba ya la...
17/07/2025

GYARAN TSARI – TSAFTACE DOKOKI DA AIKI NA NAJERIYA

Akwai dokoki masu kyau a Najeriya, amma ba su aiki. Tsarin da ba ya ladabtar da mai laifi — yana ƙarfafa rashin gaskiya ne.
Dole ne a gyara tsarin mulki, aikin gwamnati da shugabanci gaba ɗaya.

🗣️ Kana ganin me ya fi bukatar gyara cikin tsarin mulkin Najeriya? Kuma ta yaya za a tabbatar ana bin dokoki?

GYARAN ZABE – ZAƁE NA GASKIYA, BA NA NAIRA BAIdan har muna sayar da ƙuri’a, to kar mu yi kuka idan muka samu shugabanni ...
17/07/2025

GYARAN ZABE – ZAƁE NA GASKIYA, BA NA NAIRA BA

Idan har muna sayar da ƙuri’a, to kar mu yi kuka idan muka samu shugabanni marasa amfani.
Gyaran kasa ba zai yiwu ba muddin zaɓe yana ginuwa bisa kudi ba cancanta ba.

Mu koyi kin cewa a'a idan an bamu kudi don mu kadawa wanda bai dace ba.

🗣️ Ka taɓa kin karɓar kudi ko kayan masarufi saboda ƙuri’a? Me ya sa, kuma me ya faru daga baya?

GYARAN ILIMI – DOMIN ILMI YANA GYARA AL'UMMAIlimi ba kawai karatu ba ne. Ilimi ya kamata ya koyar da mutum aiki, gaskiya...
17/07/2025

GYARAN ILIMI – DOMIN ILMI YANA GYARA AL'UMMA

Ilimi ba kawai karatu ba ne. Ilimi ya kamata ya koyar da mutum aiki, gaskiya, da sadaukarwa.
Yadda za mu gyara Najeriya, sai mun gyara makarantunmu — daga tsarin karatu har zuwa malamai da ɗalibai.

🗣️ Wane canji kake ganin ya kamata a fara dashi a ilimin Najeriya domin gobe ta fi yau?

GYARAN SHARI’A – ADALCI GA KOWANajeriya ba za ta cigaba ba muddin shari’a tana yi wa wasu kallon “manyan mutane” a lokac...
17/07/2025

GYARAN SHARI’A – ADALCI GA KOWA

Najeriya ba za ta cigaba ba muddin shari’a tana yi wa wasu kallon “manyan mutane” a lokacin da take murkushe talaka.

Idan mai laifi bai ji tsoron hukunci ba — to ina tsoron Allah?

🗣️ Kana ganin shari’a a Najeriya tana aiki ne daidai? Idan ba haka ba, me ya kamata a canza?

GYARAN TARBIYYA – SHINE TUSHEN GYARAN KASAIdan muna son Najeriya ta gyaru, sai mu fara da tarbiyyar iyali da yara. Yaro ...
17/07/2025

GYARAN TARBIYYA – SHINE TUSHEN GYARAN KASA

Idan muna son Najeriya ta gyaru, sai mu fara da tarbiyyar iyali da yara. Yaro da ya tashi da gaskiya, adalci, da ɗa’a, ba zai zama barazana ga al’umma ba idan ya girma.

Shugaban da ke mulki yau — ya taɓa zama ɗan makaranta ne jiya.

🗣️ Me kake ganin ya fi tasiri a tarbiyya: iyaye, makaranta, ko al’umma? Kuma yaya za mu gyara tarbiyya a Najeriya?

17/07/2025

Yau kuma akan manya-manyan hanyoyin gyaran Najeriya ne zamu yi ta posting.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Citizenship HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Citizenship HAUSA:

Share