27/08/2026
An K**a Wani Matashi Mai Shekaru 25 a Borno Hoton da Aka Gano a Wayarsa Ya Jawo Zargi
Dakarun Operation Hadin Kai, tare da jami'an CJTF, sun k**a wani matashi da ake zargi da kasancewa da alaƙa da ISWAP a garin Mairari, Guzamala LGA ta Jihar Borno.
An k**a matashin, mai suna Bubba Hamadu, mai shekaru 25, da misalin ƙarfe 2:22 na rana ranar Litinin, 24 ga Agusta 2026.
Rahotanni sun ce yayin binciken farko, jami'an tsaro sun gano wani hoto a wayarsa da ke nuna shi tare da wasu mutanen da ba a tantance ko su waye ba, waɗanda ke ɗauke da bindigogi kirar AK-47.
Wannan hoton ne ya sa ake binciken yiwuwar alaƙarsa da ISWAP.