Musa Abubakar Na Sidi

Musa Abubakar Na Sidi YA RASULULLAH YA YAUSHE ZANGA FUKANKA ���

Ina yiwa đaukacin abokai da 'yan uwa na wannan saha musamman masoya Shugaba ﷺ daga kowace da'ira murna da zagayowar sall...
07/06/2025

Ina yiwa đaukacin abokai da 'yan uwa na wannan saha musamman masoya Shugaba ﷺ daga kowace da'ira murna da zagayowar sallar yanka, ina addu'ar Allah ya tabbatar mana da alkhairi da albarka a rayuwar mu baki ɗaya...

Musa Abubakar Na Sidi

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa)A irin wannan ranar ce 9 ga watan ...
05/06/2025

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa)

A irin wannan ranar ce 9 ga watan Zul-Hijjah, SHEKARA ta goma bayan Hijira a Dutsen Arafat (ranar Arfa kenan) Annabi Muhammad S.A.W ya yi wata huduba mai ratsa zuciya.

Fiyayyen Halitta (S.A.W) Ya fara da cewa:

“Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai
yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan
wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari
abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar
da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a
wannan wuri a yau.

🎇
Ya ku mutane kamar yadda ku ka ri'ki wannan
wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da
kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma
abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi
da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma
karewa, ku maida wa mutane kayan da s**a ba
ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu
su cuce ku.

🎇
Ku tuna fa, hakika Allah zai yi
sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana
cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin
da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye
addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku
akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka
ku guji binshi akan kanana.

🎇
Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa
matayenku, amma su ma suna da hakki bisa
kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su,
Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su
kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu
domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma
mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi
abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci
zina.

🎇
Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah
(SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku
azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka.
Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.

🎇
Ku sani fa, kowane musulmi dan uwan musulmi
ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da
fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da
aikata kyawawan ayyukka.

🎇
Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya
gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku,
saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da
hanya madaidaiciya bayan na kau.

🎇
Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai
zo bayana kuma babu wani addini da zai zo
(bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi
tunani sosai akan wannan magana da na gaya
maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

🎇
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkur
ani) da kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba
za ku taba bata ba.

Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji maganata daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.

🎇
Ya Allah... ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar
da aikenka zuwa ga bayinka.”

'Yan uwa ku yada (sharing? wannan HUDUBAR Ta Masoyin mu Annabi Muhammad S.A.W ga 'yan
uwa musulmai

03/06/2025

•Insha Allahu Yau Talata 7/12/1446H = 3/June/2025 Sheikh Sharif Sani Janbulo Zai Gabatar Da Majalasi A👉Kuregen Sani Kano,9:00pm.

Zul hijjah!Watan zul hijja yana daga cikin watanni  guda huɗu (4) a musulunci masu alfarma sune;1. Muharram2. Rajab3. Zu...
28/05/2025

Zul hijjah!

Watan zul hijja yana daga cikin watanni guda huɗu (4) a musulunci masu alfarma sune;

1. Muharram
2. Rajab
3. Zul Qa'adah
4. Zul hijjah

Wađannan sune watanni guda huɗu masu alfarma ba'a yaƙi a cikin su, sannan Allah Subhanahu Wa ta'allah ya tare falaloli masu dimbin yawa da albarka a ciki, wanda ya kyautu musulmi ya zage dantse wajen yawan ibada, yawan ambaton Allah da kuma yawaita addu'a saboda akwai ijaba a ciki saboda alfarmar su.

Kamar yadda ya tabbata yau talata 29th ga watan Zul Qa'adah 1446 AH In Sha Allah gobe Laraba shine zai zama đaya ga watan Zul hijjah.

Wađannan kwanaki da zamu shiga gobe kwanaki ne masu girma wanda Allah Subhanahu Wa ta'allah ya rantse dasu a cikin alƙur'ani;

وَلَيَالٍ عَشْرٍ

Waɗannan kwanaki goma da Allah ya ambata sune kwanaki goma na farkon watan zulhajj, wanda a cikin wannan kwanaki Allah Subhanahu Wa ta'allah ya sanya rana guda ɗaya wanda idan mutum ya azumci wannan ranar Allah Subhanahu Wa ta'allah zai gafarta masa zunubin Shekara biyu wacce ta gabata da wacce take fuskanto shi, wannan azumin shine azumin ranar tara (9) ga zul hijjah wato ranar arfa.

Saboda mahimmancin wannan kwanaki da falalar dake cikin su bayin Allah suna azumtar kwanaki goman gaba ɗaya saboda neman dace da sa'ada a wajen Allah Subhanahu Wa ta'allah saboda sun san mahimmancin wannan kwanaki da kuma alkhairan da Allah ya zuba a cikin su.

Ɗan uwa idan kana da wata muhimmiyar buƙata a wajen Allah wannan dama ce ka samu ka dage cikin wannan kwanakin dan cimma wannan buƙatar da kake nema a wajen Allah, ka dage da ayyukan alkhairi, yawaita karatun alƙur'ani, salatin Annabi ﷺ, kyauta, sadaka, kyawawan đabi'u, yafiya da afuwa ga wanda yai maka ba dai dai ba, kada kai wasa cikin wannan kwanaki dama ce Allah ya baka mai girman gaske wadda ba lallai ka sake samun irin ta ba, yanzu kana da lafiya tayu ta gaba zata riske ka babu lafiya koma rayuwar ta ƙare.

Allah yasa muna cikin masu morar alkhairin dake cikin waɗannan gwalagwalan kwanaki.

Musa Abubakar Na SidiMusa Abubakar Na Sidi

*اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُه*Prayer is the foundation of Faith.The most potent weapon against all ...
16/05/2025

*اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُه
*Prayer is the foundation of Faith.The most potent weapon against all evil, the most effective medicine against sickness, and the most valuable gift to those we really love and care for.*

*May Almighty ALLAH in His infinite mercies continue to shower His grace, mercies, blessings and protection upon us and our families.*
*Ameen thuma Ameen*

Juma'at Mubarak

Barkwancin sa!Barkwanci shine abinda yake saka nishađi ko dariya haka, a taƙaice dai zaka fađawa mutum magana kamar gask...
15/05/2025

Barkwancin sa!

Barkwanci shine abinda yake saka nishađi ko dariya haka, a taƙaice dai zaka fađawa mutum magana kamar gaske amma kuma da wasa kake saboda ai nishađi.

Barkwanci yana daga cikin đabi'un Shugaba AlayHis Sallam kamar yadda ya tabbata a hadithn Sayyidina Aba Hurairah Rta ;

قالوا يا رسول الله إنك تداعبنا، قال لا أقول إلا حقا

Sahabbai s**a ce ya Ma'aikin Allah ka kasance kana mana barkwanci, sai yace eh haka ne amma bana fađa sai gaskiya (ma'ana bawai kawai yana fađar abinda za'ai dariya ayi nishađi bane, duk abinda zai fađa gaskiya ne kuma za'a nishađantu a hakan)

Wata tsohuwa dattijuwa tazo wajen Manzan Allah ﷺ sai tace;

يا رسول الله ادع الله لي أن يدخلني الجنة، فقال صلى الله عليه وسلم يا أم فلان إن الجنة لا يدخلها عجوز، فولت المرأة وهي تبكي، فقال ﷺ أخبروها أنها لا تدخل وهي عجوز

Ya Ma'aikin Allah kai min addu'a Allah ya shigar dani aljannah, sai Shugaba ﷺ yace mata yake wannan dattijuwa lallai tsofaffi ba zasu shiga aljannah ba, sai matar nan taita kuka, sai Manzan Allah ﷺ yace aje a fađa mata (abata labari)cewa ba zata shiga aljannah ba a tsohuwa (yake nufi) har sai an mayar da ita budurwa (mai ƙananun shekaru, kuma cikakkiyar mace wacce babu tawaya tare da ita)

Alƙur'ani ya bamu labarin irin siffar su ;

إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً # فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا # عُرُبًا أَتْرَابًا

Za'a mayar dasu masu tasowa, kuma a sanya su zama 'yan mata cikakku wanda basu taɓa haida ba ko haihuwa, ababen so ga duk wanda ya gansu, kuma shekarun su zasu kasance duk đaya (bawai wata ta girmi wata ba b***e kaga ai wacce ta tsufa saboda yawan shekarun ta).

Suratu Waƙi'a 56/35, 36 & 37.

Ya kake tinanin yanda wannan tsohuwar zataji idan aka bata labari? Tabbas ita kanta abin zai nishađantar da ita bayan da ta gama daga hankalin ta ashe bata fahimci maganar mafi fasahar harshe bane صلوات ربي وسلامه عليه

-
Musa Abubakar Na Sidi

Duk abinda mutum yake nema zai samu idan ya fake da Shugaba ﷺ, neman suna yake, đaukaka yake nema, alfarma ce a wajen mu...
13/05/2025

Duk abinda mutum yake nema zai samu idan ya fake da Shugaba ﷺ, neman suna yake, đaukaka yake nema, alfarma ce a wajen mutane, ko yaudarar mutane zaiyi, duk wannan abubuwan mutum zai samu idan yaje da Shugaba ﷺ amma ƙarshen sa bazai kyau ba idan yayi amfani da sunan Annabi ﷺ ta hanyar da bata dace ba.

Musa Abubakar Na Sidi

22/04/2025

AQIDAH TA!

Aqidata guda ɗaya ce itace "Gaskiya" babu wani tafarki dana keɓanta dashi shi kaɗai ɗariƙa ce, Da'ira ce ko kuma ƙungiyace, a wajen mafi yawan mutane rashin matsaya akan tafarki guda ɗaya musamman irin yanda firƙoƙi s**a bayyana cikin musulunci suna kiran wannan da munafunci wanda ni kuma a waje na ba haka bane.

Abinda nake kiran wannan fahimtar tawa shine neman gaskiya tare da yaƙinin bata keɓanta a waje ɗaya ba zaka iya samun ta a ko ina bawai sai abinda kai ka yarda dashi ba, mafi girman sunana da nake alfahari dashi da godiyar Allah Subhanahu Wa ta'allah bisa ni'imar sa gare ni shine musulunci, saboda duk wani alkhairi a bayan wannan yake ko mene kuwa.

Amma bana alfahari da kasancewa ta cikin ɗariƙa kaza, da'ira kaza ko ƙungiya kaza saboda kowanen su yana da son ransa da son zuciyar sa a cikin tafiyar sa, amma kuma haka bashi ya nuna babu alkhairi ko daidai a cikin tafarkin ba.

Idan daa mutane suna kallo na a matsayin ɗan ƙungiya kaza, ko wata ɗariƙa ko wata da'ira to su daina ba haka bane, kawai na yadda da cewa kana tasirantuwa da abinda yafi zama jikin ka ko kafi yarda da gamsuwa dashi, ga wanda ya sanni yake bibiya ta yasan ni mutum ne mai 'yanci wajen yin magana akan abinda na fahimta na gaskiya daga kowace firƙa kuma har yau haka nake na yadda da wasu abubuwa da yawa daga cikin ɗariƙun sufaye kuma na saɓa da wasu to haka ma cikin ƙungiyoyi da da'irori na addini, hatta ƙungiyar da mutane suke ganin a ciki nake akwai abinda na yadda dashi akwai wanda na saɓa dashi a fahimtata ni kaɗai.

Ka bawa kanka 'yancin karɓar gaskiya daga ko ina tare da gujewa son zuciya koda a cikin abinda kake ne shine zai baka damar kuɓuta daga tuhumar da Allah Subhanahu Wa ta'allah zai maka akan wannan abin, saboda mutane da yawa suna mantawa da cewa za'a mutu kuma tabbas za'a bujirowa kowa da abinda ya aikata duk ƙanƙantar abin wannan ranar zata zo.

Kowanen mu yana da sauran lokacin neman gaskiya, lokaci be ƙure masa ba na yabi gaskiya kuma ya yaƙi son zuciyar sa

Address

Nasarawa
Agyaragu

Telephone

+2348066031477

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Musa Abubakar Na Sidi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Musa Abubakar Na Sidi:

Share