Mu koma zuwa ga allah

Mu koma zuwa ga allah Dan uwa yi kokari ka aekata me kyau tunkan lakaci yaqure maka domin ita duniyan nam ba matabbata bane

24/03/2025
15/03/2025

سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ

15/03/2025

أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ

13/03/2025

فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ

13/03/2025

وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَى تَنْفَعُ الْمُؤْمِنِينَ

Abubuwa 15 Da Za Su Kankaro Maka Mutunci A Zamantakewarka Da Mutane:1- Idan ka kira mutum a waya sau ɗaya ko biyu, amma ...
16/01/2025

Abubuwa 15 Da Za Su Kankaro Maka Mutunci A Zamantakewarka Da Mutane:

1- Idan ka kira mutum a waya sau ɗaya ko biyu, amma bai ɗauka ba, kada ka sake kira, kuma ka kyautata masa zato, la'alla bai gani ba ne, ko kuma yana cikin yanayin da ba zai ɗauka waya ba, sai dai idan kana da tabbacin dalilin da ya sa bai ɗauka ba.

2- Ka mayar da kuɗi ko wani abu da ka ara, kada ka bari sai an tambaye ka.

3- Kada ka yi wa mutum tambaya da take da alaƙa da sirrin rayuwarsa, idan ma buƙatar hakan ta k**a, to ka fara da neman izininsa.

4- Idan abokinka ya biya muku kuɗin mota ko abinci ko wani abu, to ka yi ƙoƙari ka biya muku na gaba.

5- Idan mutum yana magana kada ka katse shi, ka ba shi dama ya gama faɗin duka maganarsa koda ba ka yarda ba.

6- Idan ka yi wa mutum raha ko barkwanci, sai ka kula ba ya so, to kada ka sake, kuma ka nemi afuwarsa.

7- Idan mutum yana magana da kai, kada ka riƙa ba shi amsa alhali idonka na kan waya, zai ga ka raina shi.

8- Idan mutum ya gaya maka zai je asibiti, kada ka tambaye shi me zai je yi, ka yi masa addu'a kawai, idan yana son ka sani, zai gaya maka da kansa ba sai ka tambaye shi.

9- Kada ka riƙa saurin ba da shawara idan ba a nema daga gare ka ba.

10- Idan ka sanya glass mai duhu, to ka cire shi idan kana magana da wani.

11- Idan mutum ya ba ka wayarsa domin ka ga photo ko video ko wani abu, to kada ka yi scrolling gaba ko baya, don ba ka sani ba ko sirrinsa ne a wajen.

12- Idan ka fahimci ba a so ka ji magana, to koda ka ji, ka yi k**ar ba ka ji ba.

13- Idan mutum ya yi kuskure a gabanka, sai ya yi sauri ya gyara, to ka yi k**ar ba ka fahimci ya yi kuskuren ba.

14- Idan mutum ya ɗauki nauyin biya maka kuɗin abinci ko wani abu, kada ka ɗauki mai tsada sosai.

15- Idan mutum ya rubuta abin da ya burge ko ya amfanar da kai, amma ba ka yaba masa ba, to idan ya rubuta wanda bai burge ka ba, kada ka soke shi, hakan ƙaranta ne.
16/01/2025

Shin ko ka canza rayuwarkaAcikin wadannan watanniDaga16/July/2024Zuwa yau16/November/2024CANZA RAYUWARKA (3/4)Abin da za...
22/11/2024

Shin ko ka canza rayuwarka
Acikin wadannan watanni
Daga
16/July/2024
Zuwa yau
16/November/2024
CANZA RAYUWARKA (3/4)

Abin da zaka aikata a cikin watanni 6 masu zuwa zai iya canza rayuwarka na har abada.

Wannan ita ce fitowa ta uku kuma ta kusa da na ƙarshe a jerangiyar saƙonmu mai taken, "Canza Rayuwarka a Cikin Wata 6."

A karanta da idanun basira, sannan a tura ma ƴan uwa.

Muna godiya da gudunmawarku ga wannan shafin.

Ku cigaba da bibiyar mu a wannan shafin don samun saƙonni masu zaburarwa a cikin harshen Hausa.

Allah ya sa mu gudu tare mu tsira tare Ƴan Uwa 😊🙏

Hausa Motivation

"Kowa yana da jahilcin wasu abubuwa, amma mutum mai nutsuwa ne kaɗai ya san haka, da kuma inda nasa jahilcin yake. Mara ...
17/10/2024

"Kowa yana da jahilcin wasu abubuwa, amma mutum mai nutsuwa ne kaɗai ya san haka, da kuma inda nasa jahilcin yake. Mara nutsuwa yakan jahilci abubuwa da dama, amma kaico! Bai san haka ba.

Kamar dai Ilmi ne; sai ka ga wasu suna ta ƙoƙarin sai sun burge mutane da son nuna sun san komai, har su je suna bayar da amsoshin da za su ɓadda mutane, su kuma jefasu cikin halaka.

Amma idan mai Nutsuwa ya ji tambaya, ko wani abu da bai sani ba, nan-da-nan zai san aikin dake gabansa shi ne ya nemo amsar abin don inganta nasa ilmin shi ma, maimakon ya ba da amsar da ba daidai ba ce, nan gaba a ji kunya.

Gudu daga Jahilci yanayi ne a zuciyar mai- hankali, mai-nutsuwa, wanda ya san abin da yak**ata. A kullum nutsatstsen mutum ya kan nesar da tunaninsa daga ra’ayin riƙau, son iya-yi, son nuna sani, da hanzarin ɗaukar matsayi ba tare da cikakken sanin bayanin matsalar ba, ko saurin bayar da amsa ba tare da sanin haƙiƙaninta ba.

Irin waɗannan mutane masu shisshigi su ne suke dulmiyar da al’umma, musammam a inda jahilci ya yi yawa, su jawo ruɗani da muguwar hasara ga jama’a, musammam waɗanda su ka dogara da su."

📚 Tunaninka Kamanninka.

**anninka

"Farin tunani shi ne wanda yake wanke zuciyar mutum daga duk wasu abubuwa munana, ya kuma cetar da ita daga halin gazawa...
17/10/2024

"Farin tunani shi ne wanda yake wanke zuciyar mutum daga duk wasu abubuwa munana, ya kuma cetar da ita daga halin gazawa. Ba illa ga mutum irin yin tunanin gazawa, ko kuma ya ringa yin zaton wata illa tare da shi, ba tare da cikakken nazari ba.

Sai ka ji mai niyyar tafiya yana cewa, “Abin da ma jirgin latti zai yi”; ko, “Ƙarshenta ma a yi ruwa”, ko, “Wataƙila ma tafiyar banza zan yi”. Wani lokaci sai ka ji ɗan-kasuwa yana cewa: “In an kawo kayan ma faɗuwa za a yi”. Ko ka ji mai neman aiki yana cewa: “Da ƙyar zan sami aikin nan”, ko, “Wannan aikin ya fi ƙarfina, ba zan iya ba”. Ko ka ji mai sana’a yana cewa, “wallahi na tsani wannan sana’ar”, ko ma ya ringa jin kunya ana danganta shi da ita. Dukkaninsu kaiconsu!

Yawancin waɗanda ba sa zaton nasara tun kafin su taɓuka, to ba sa samunta ko sun taɓukan. Irin waɗannan mutane ne baƙin tunaninsu yake sa wa su yi ta kura-kurai saboda raunin zuci, har sai hasarar ta wanzu, k**ar dai yadda s**a ayyanata tun farko. Da ma ita suke zato, to kuwa ita za su tarar. Ko da nasara ta same su a wannan ɗawainiya ta su, ba za ta yi ƙarko ba, domin ba za su riƙe martabar da hanneye biyu-biyu ba.

A dangantakar tunani da halayya, idan ka nemi lalura sai ta zo maka; idan ka ayyana zazzaɓi sai ka ji shi; idan ka tsoraci mutum sai ya azabtaka; idan ka nemi barci sai ya k**aka; idan gabanka ya faɗi an gama da kai.

Kada ka yarda tunanin gazawa ya sami gurbin da zai zauna ya yi saƙarsa a zuciyarka. Ko mene ne ƙasƙancin sana’arka a idanun wasu, lallai ne ka ɗauke ta da ƙarfi da muhimmanci domin ita ce sana’arka. Idan ka girmamata, ita ma wataran za ta girmamaka. Idan kuwa ba ka sonta, ko ba ka jin ɗaɗinta, to canja ta maza. Lallai ne ka zamto mai jin ɗaɗin abin da ka sa a gaba da sana’arka."

📚 Tunaninka Kamanninka.

**anninka

Address

AJIYA Treet
Alkaleri

Telephone

+2349075695000

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu koma zuwa ga allah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mu koma zuwa ga allah:

Share