ANC Hausa News

ANC Hausa News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ANC Hausa News, Media/News Company, Anchau.

Permanently closed.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata manyan motoci 25 na barasa a 2022Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta lalata man...
29/12/2022

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata manyan motoci 25 na barasa a 2022

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta lalata manyan motoci 25 na barasa tare da k**a wasu mutane 2,260 da ake zargi da aikata laifuka a ayyukanta da ta gudanar daga watan Janairu zuwa Disamba na 2022.

Dakta Harun Sani Ibn-Sina, babban kwamandan hukumar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar a yau Alhamis a Kano.

Ya ce manyan motocin na dauke da dubban kwalabe na barasa iri-iri, inda ya ce za a farfasa wasu karin kwalaben na giya kafin watan Janairu.

“Yawancin wadanda aka k**a da laifin aikata laifuka, an mika su ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace, wadanda ke kasa da kasa sun hadu da iyalansu.

“A shekarar da ake bankwana da ita, domin a rage barace-barace a cikin birni, mun kwashe mabarata kusan 1,269 a cikin wata daya, 386 aka mayar da su jihohinsu.

“Hukumar Hisbah ta jihar Kano kuma ta yi nasarar tarwatsa tarurrukan lalata 86 da sauran laifuka mak**antansu domin dakile munanan dabi’u a fadin jihar,” inji shi.

~ Daily Nigeria

Bikin Balbela ANCHAU Home, Allah ya kai mu lokacin lafiya.
28/12/2022

Bikin Balbela

ANCHAU Home, Allah ya kai mu lokacin lafiya.

M A S H A  A L L A H Anyi Auren dan gidan Marigayi Alhaji Umar Malumfashi(Kafi Gwamna) kuma tuni har sun tare.Muna Addu'...
28/12/2022

M A S H A A L L A H

Anyi Auren dan gidan Marigayi Alhaji Umar Malumfashi(Kafi Gwamna) kuma tuni har sun tare.

Muna Addu'ar Allah Ya sanya Alheri Ya basu zaman lafiya, kwanciyar hankali da zuri'a dayyiba.

Daga Abba El-Mustapha

Babban jarumar shirya fina-finai na masana'ar Kannywood Rahma Sadau ta saki sababbin hotunan a yau daga birnin Paris.Wan...
28/12/2022

Babban jarumar shirya fina-finai na masana'ar Kannywood Rahma Sadau ta saki sababbin hotunan a yau daga birnin Paris.

Wani fata za kuyi mata?

Shi'a Ta Yi Kiran Sakin Abduljabbar Cikin Gaggawa Ba Tare Da Ɓata Lokaci BaƘungiyar Shi'a ta IMN ƙarƙashin Jagorancin Ib...
28/12/2022

Shi'a Ta Yi Kiran Sakin Abduljabbar Cikin Gaggawa Ba Tare Da Ɓata Lokaci Ba

Ƙungiyar Shi'a ta IMN ƙarƙashin Jagorancin Ibraheem Zakzaky, ta nemi a saki Abduljabbar Nasiru Kabara, cikin Gaggawa kuma ba tare da wani Sharaɗi ba.

A wata sanarwa da s**a fitar wacce s**a rabawa maneman labarai a yammacin Laraba, wacce take ɗauke da sanya hannun Halima Aliyu, ta ɓangaren Dandalin Ɗaliban Harkar IMN.

Sun kuma nemi al'umma tare da dukkan masu hankali da su sanya baki su shiga tsakani domin Abduljabbar ya samu ƴanci daga hukuncin Kotun Shari'ar Musulunci ta Kano.

Sanarwar ta bayyana Abduljabbar a matsayin wani mutum me ƙoƙarin kawo gyara a wannan al'umma kuma ɗan Shaikh Nasiru Kabara da ake girmamawa a Kano, Najeriya da kuma Afrika ma baki ɗaya.

DA DUMI-DUMI: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Babban Bankin Nigeria CBN Data Tsawaita Wa’adin Daina Amfani Da Tsofaffin Kuda...
28/12/2022

DA DUMI-DUMI: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Babban Bankin Nigeria CBN Data Tsawaita Wa’adin Daina Amfani Da Tsofaffin Kudaden Nigeria Daga Ranar 31 Ga Watan Janairu Zuwa 31 Ga Watan Yuni, 2023.

Wane fata kuke musu??

Daga Muhammad Kwairi Waziri

YANZU-YANZU: An k**a mai rike da sarautar gargajiya na zazzau da laifin luwadi a ZariyaRundunar ‘yan sandan jihar Kaduna...
28/12/2022

YANZU-YANZU: An k**a mai rike da sarautar gargajiya na zazzau da laifin luwadi a Zariya

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta k**a wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Zazzau da aka sakaya sunansa a Zariya bisa zargin yin luwadi da wani yaro dan shekara 14.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammadu Jalige, ya shaida wa manema labarai a Zariya, jihar Kaduna a ranar Laraba, inda ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin idan aka kammala bincike.

Yayan yaron, Hamza Zubairu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Disamba a Unguwar Kwarbai da ke Zariya.

Mista Zubairu ya ce wanda ake zargin, makwabcin iyayen yaron ne ya kasance yana girmama su sosai a unguwar.

Ya kara da cewa a ranar da lamarin ya faru, wanda ake zargin ya aika wanda abin ya shafa cikin dakinsa domin ya dauko kudi amma ya bi matashin cikin dakin ya kulle kofa.

Daga baya mai wannan laifin ya zare wuka kuma ya yi barazanar kashe yaron idan yai ihu kan abin da zai yi masa.

Ya ce yaron ya shiga damuwa kuma bai iya gaya wa kowa abin da ya faru da farko ba har sai da ya samu kwarin gwiwa ya gaya wa innarsa.

“Goggon ce ta kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sanda ta birnin Zariya,” inji Mista Zubairu.

A nata jawabin, Aishatu Ahmed, Ko’odineta, Salama Sexual Assault Referral Referral Centre, Gambo Sawaba General Hospital, Zaria, ta shaida wa NAN cewa cibiyar ta samu bukatar kulawar lafiyar wanda abin ya shafa.

Ta ce cibiyar ta aike da sak**akon bincikenta zuwa hedikwatar ‘yan sanda na birnin Zariya.

NAN

Ina Kokarin Ganin Na Zama Ta Gari, Ya Allah Ka Yafe Min Kura-kuraina, Ka Dawo Da Ni Kan Hanya Madaidaiciya, Cewar Safara...
28/12/2022

Ina Kokarin Ganin Na Zama Ta Gari, Ya Allah Ka Yafe Min Kura-kuraina, Ka Dawo Da Ni Kan Hanya Madaidaiciya, Cewar Safara’u

Jama'a a taya ta da addu'ar Allah ya cika mata burinta.

~ Idon Mikiya

An Karrama Matashiyar Likita, Dr. Na'ima Idris Usman Kan Guddummuwar Da Take Badawa Wajen Ilmantar Da Mata Akan Lafiyars...
27/12/2022

An Karrama Matashiyar Likita, Dr. Na'ima Idris Usman Kan Guddummuwar Da Take Badawa Wajen Ilmantar Da Mata Akan Lafiyarsu A Sabbin Kafafen Sadarwa Na Zamani

Na Daina Jin Daɗin Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu DantataHamshakin  attajirin nan na Jihar Ka...
27/12/2022

Na Daina Jin Daɗin Rayuwa, Burina In Cika Da Imani Kawai, Cewar Alhaji Aminu Dantata

Hamshakin attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani.

Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan.

Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye.

“Na karade jihohin Nijeriya, kuma na yi harkoki da jama’a a daukacin jihohin, na yi abokai da dama sai dai abin bakin cikin shi ne, da wuya in ambato 10 daga ciki wadanda ke raye.

“Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani.

“Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini ahuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini.

“A zuri’armu ni kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” in ji Dantata.

Daga nan, ya yaba da ziyarar da aka kai masa, kana ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya ga Nijeriya da al’ummarta.

27/12/2022

ZABI DAYA: First Class a jami'a ko miliyan 50 wanne kafi so?

Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Jagoranci Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam'iyyar APC A Jihar Zamfara A yau Talata mai ...
27/12/2022

Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, Ya Jagoranci Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Jam'iyyar APC A Jihar Zamfara

A yau Talata mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar, shugaban yakin neman zaben Gwamnan jihar Zamfara Dr. Bello Matawalle a karo na biyu, ya jagoranci taron kaddamar da yakin neman zaben wanda ya gudana a garin Kauran Namoda dake jihar Zamfara.

Ga jadawalin takarkarun da aka kaddamar k**ar haka;

•Governor.
•27 State House Of Assembly.
•7 Member House Of Representatives.
•3 Senators.

Muna rokon Allah (SWT) ya shiga cikin wannan tafiya akarkashin Jagorancin mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, jagoran jam’iyyar APC kuma shugaban babban kwamitin yakin neman zaben Mai girma Gwamnan jihar Zamfara His Excellency, Hon. (Dr.) Bello Muhammad (Matawallen Maradun) karo na biyu a matsayin Gwamnan jihar Zamfara 2023, Allah (SWT) ya baiwa wannan tafiya cikakkiyar nasara da galaba saboda Annabi Muhammad (SAW).

Al’mansoor Gusau,
Babban daraktan yada labarai na mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Dr. Abdul'aziz Yari Abubakar.

Address

Anchau

Telephone

+2347017404636

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ANC Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to ANC Hausa News:

Share