30/03/2024
ABINDA SHEIK ABDULLAHI DANDUME YA FAƊAMA 'YA'YANSA KENAN..!!
Shek Abdullahi Dandume Allah ya ƙara haskaka Qabarin sa, Haka ya yima 'Ya'ya da Muridai Wasiyya Kamar haka:
👇
✅ 1. Duk juyin zamani kar ku Yadda ku Raina ibadar wani. Domin Amsar IBADAR BAYEE, Lamarin Ubangiji ne
✅ 2. kar ku zagi Addini ko Aqeedar da ta saɓa da taku Aqeedar.
✅ 3. Ku yi duk yadda zaku yi kar a Tsere maku a Harkar Ilimi, Musamman Ilimin Addini.
✅ 4. Duk juyin Rayuwa kar ku Wulaƙanta kanku ma'ana Shine ku yi (Sana'ah), dan ku Kauce ma Kaskanci.
✅ 5. Kar ku Yadda a Bautar da ku a sha'anin Duniya, Sai in dan nema ma Al'umma Mafita ne.
✅ 6. Kar ku Kyamaci Kowane irin Ilimi matukar yin shi zai fa'idantar.
✅ 7. Kar ku Yadda wani abu ya Ruɗeku ga barin Ganin Girman Annabi Muhammad saw.
✅ 8. Ku kyautata zato ga kowa, Domin komi da kuka gani Halittar Allah ne k*ma daga gare shi ne, Allah yana son halittar sa, shiyasa ya Halicce shi.
✅ 9. Ku girmama Kowane Malami musamman BATIJJANE!
✅ 10. Idan ana zagin Bayin Allah, to ku bar wajan, Musamman Waliyyai.
✅ 11. Ya ce mana Wallahi Tallahi billahillaze la'ilaha illa huwa!
Duk wanda yake Ambaton wannan kalmar
لا إله إلا الله محمد رسول الله
To ku bishi Sallah, Domin La'ilaha illallahu, Muhammadur Rasulullah, Tafi ƙarfin wasa.
Wanda duk ka gani a cikin Musulunci, to ba Dabararsa bace, Saboda haka ba Ruwanku da Rashin Ilimin sa, Tsarkin sa, Aqeedar sa, ko Yawan Sabonsa, Domin Hisabinsa yana ga Allah Ta'ala.
A ƙarshe ya ce mana:
✅ 12. Ku tsaya iyakar yinku a Cikin Bautar Allah SWT, ku k*ma Riƙe alƙawarin SHEHU Tijjani bakin ƙarfin ku Iya Rayuwar Ku, amma kar ku Hantari kowa Sannan kar ku ɗauka cewa dole sai mai Wuridin Tijjaniyya ne kaɗai Mai Rabon shiga Cikin (Aljanna).!!
*
*
Ya taɓa faɗama ALHAJI MAHE MAI ALLURA, (Allah ya kara masa Rahma): Ya ce: " Alhaji Mahe, ka faɗima 'Ya'yanka Masu Ra'ayin Izala, Muna masu fatan Alkhairi , k*ma su yi iya bakin kokarin su wajan bin Allah da riƙo da Addini, Tabbas su Masu Arziƙi ne Duniya da Lakhira.