Zamfara media

Zamfara media Good

Sanarwa: Za A Yi Taron Karawa Juna Sani A Katsina Ranar Juma'a mai zuwa ne za a shiga Mu'utamar wanda 'yan uwa almajiran...
24/01/2023

Sanarwa: Za A Yi Taron Karawa Juna Sani A Katsina

Ranar Juma'a mai zuwa ne za a shiga Mu'utamar wanda 'yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na ɓangaren Dandalin Dalibai (Academic Forum) da Dandalin Yan uwa mata (Sisters Forum) s**a shirya.

Za a shiga taron na karawa juna sani ne a garin Katsina, a ranar Juma'a 27 a rufe ranar Lahadi 29 ga watan Junairun 2023.

Taken Taron shine; Manufar Halittan Dan Adam A Doron Kasa.

Za a saurari jawabai a kan bangarori daban daban daga Malamai da manazarta a wajen taron na tsawon kwanaki biyu.

Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne zai gabatar da jawabin rufe taron ta hanyar 'majigi', kamar yadda aka saba.

Ana gayyatan duk dan uwan da Allah Ya h**e ma damar halarta don amfanuwa da jawaban da za a saurara a wajen.

Hakkin Shiga; Maza Naira 2,000 ne, Mata kuma 1,500.

Allah Ya ba da ikon halarta. Ilahi Ameen Ya Allah.

24/01/2023

A can Baya Idan Mukace Manjo Buhari Azzalumi ne Sai S**e Addu'a akeyiwa Shugaba Ko Ynx Fatwar ta Canza Ne da Har Ashar akemasa😂

Update: The Kaduna state gubernatorial candidate of the People’s Redemption Party (PRP), Malam Hayatuddeen Lawal Makarfi...
22/01/2023

Update:

The Kaduna state gubernatorial candidate of the People’s Redemption Party (PRP), Malam Hayatuddeen Lawal Makarfi, on Sunday evening paid a visit to the leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), at his Abuja residence.


22/01/2023

Hausa

Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna na Jami’iyyar PRP, Mallam Hayatuddeen Lawal Makarfi, ya ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), yammacin yau lahadi a gidansa dake Abuja.


22/01/2023

Bamu Yadda Cewa Kungiyoyin Siyasa Ne Zasu Warware Matsalar Talaka Ba-Inji Shaheed mlm Muhammd Turi Kano.Bamu yadda cewa ...
22/01/2023

Bamu Yadda Cewa Kungiyoyin Siyasa Ne Zasu Warware Matsalar Talaka Ba-Inji Shaheed mlm Muhammd Turi Kano.

Bamu yadda cewa kungiyoyin Siyasu su zasu warware matsalar Talaka ba, in talaka yaga dama ya maida kansa kwallo A Shurashi Yadda Akaga Dama wannan kuma ya Rage Nashi Amma wannan Baze warware matsalar sa ba,Su wayennan Gagga-gaggan kurayen Sune kullum Suke Rikida Su Chanza Sunan Jam'iya S**e To Ga Sabuwar Jam'iya ta ceto, Shi kuma talaka dake Rudaddene Sai yabi Duuu yace
An samu Chanji Ansamu chanji Ansamu Sabuwar jam'iya Sabuwar jam'iyar cuta dai koh.?ko ba'a Gane Ba .?.

'In Mutum yanason yanci to ba'abinda zai bashi Yanci kamar Gwagwarmayar Addinin Musulunci mu dubi Abinda yake faruwa a sassa-sassan Daban-daban Na duniya mana,Mudubi Abinda ya fari a Iran, Yau An wayi Gari Ana batun Babu Jabberiyar Gwamnati a duniya kamar America muna iya ganin Abinda America takeyi taje kasar da taga dama ta kamo Shugaban kasar kamar gafiya ko bera ta kashe-shi ko takaishi America ta Rufeshi Kasashen duniya Nawa America tayiwa Wannan.?

To inba tsoro ba ta shiga Iran mana Mu Gani Bama iran ba Iran ta mata yawa to akwai jaririyar Iran Hizbullah taje ta Dan lakutosu mu Gani ko ba,a luraba ga Abu Nan A duniya Ana gani A sarari Ta ina ita Iran ta samu wannan Karfin.?Bata samu karfi Ba sai ta hanyar Addinin Musulunci,Sabi da haka Abinda muke cewa Addinin musulunci Addini ne Na yanci Tafarki ne Na Tsira,Jma'iya ce ta ceto,Sabi da haka in mutane suna so su zama yantattu ba bayi ba a kasar su To basu da zabi sai gwagwarmaya ta Addini musulunci.

Daga: Mujaheed Umar D Giwa.

Wannan matashin, Allah Ya yi masa taufiqin  gaisawa da Imamul Khamna'ei (H). Yayin da ya isa inda Qa'eed yake zaune, sai...
22/01/2023

Wannan matashin, Allah Ya yi masa taufiqin gaisawa da Imamul Khamna'ei (H). Yayin da ya isa inda Qa'eed yake zaune, sai ya mikawa Sayyid hannunsa na dama ya manta cewa hannun Sayyid na dama baya aiki sakamakon harin bom da makiya s**a kai masa bayan nasarar juyin musulinci a Iran.

Sai Sayyid ya miko masa hannun hago, sai matashin ya dora hannunsa na dama akan kirjinsa ya fashe da kuka

Sai Imam ya kalleshi cikin murmushi yace masa, Karka damu ammina Abbas (A.S) shima haka aka yanke masa hannayensa a Karbala.

Ya Allah Ka kara lafiya da nisan kwana ga wannan babban jagora.

DAGA TSAFE JIHAR ZAMFARA  Maulidin sayyada fatimatu zahra kegudana yanzu haka wanda yan uwa muslimi almajiran sayyid zak...
21/01/2023

DAGA TSAFE JIHAR ZAMFARA

Maulidin sayyada fatimatu zahra kegudana yanzu haka wanda yan uwa muslimi almajiran sayyid zakzaky s**a shirya kamar yanda kuke gani cikin hotuna 👇

Jawad lawali ziza
21/1/2023

Daga talatar mafara jihar zamfara,   Yan uwa musulmi almajiran sayyid zakzaky (h) na garin talatar mafara dake jihar zam...
20/01/2023

Daga talatar mafara jihar zamfara,

Yan uwa musulmi almajiran sayyid zakzaky (h) na garin talatar mafara dake jihar zamfara sun fito muzahara maulidin tunawa da ranar haihuwar yar manzon allah (saww) sayyada fatimatu zahra (s a) muzahara wadda aka fara daga baban masallacin jumma'a dake garin na mafara wakilin yan uwa na garin mlm abba nuhu ne ke jagorantar muzahara kamar yanda kuke gani cikin hotuna👇

Jawad lawal ziza
20/1/2023

Happy jumma'atAllah yaimana kyakyawan karshe albarkacin wannann ranar ta jumu a🌹🌹❤️❤️
20/01/2023

Happy jumma'at

Allah yaimana kyakyawan karshe albarkacin wannann ranar ta jumu a

🌹🌹❤️❤️

Sheikh El-Zakzaky da NIA: An Sake Ɗage Zaman Kotun Zuwa Wata FebrairuBayan tsawon lokaci da aka zauna, yau ma kotun ta s...
18/01/2023

Sheikh El-Zakzaky da NIA: An Sake Ɗage Zaman Kotun Zuwa Wata Febrairu

Bayan tsawon lokaci da aka zauna, yau ma kotun ta sake zama, inda mai shari'ar ya dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Fabarairu shekerar nan.

Lauyan Sayyid Ibraheem Zakzaky da Matarsa Malama Zeenah, Barrister Abubakar Marshall ya bayyana cewar zasu sake dawowa domin ci gaba da zaman kuma suna jin ƙamshin nasara akan abunda s**a sa a gaba.

Sai dai a bangare guda kuma Almajiran Malamin ne Mazansu da matan su s**a yi dafifi a ƙofar kotun domin neman a saki Fasfo din Malamin nasu.

Sahara Reporters Hausa

Don't wait till January 31, 2023, to deposit your old N200, N500, and N1,000 banknotes with your bank or agent. Visit ww...
17/01/2023

Don't wait till January 31, 2023, to deposit your old N200, N500, and N1,000 banknotes with your bank or agent. Visit www.cbn.gov.ng for more info.

Home page of the Central Bank of Nigeria's website. Nigeria's Macro Indicators, foreign exchange details, inflation rate, CBN's latest news, documents and publications can be found here.

ABUBUWA BIYAR DA YA KAMATA KOWANE ƊAN UWA YA SAN SU Daga Sheikh Sunusi Abdulkadir"Abubuwa ne guda biyar wanda ya kamata ...
17/01/2023

ABUBUWA BIYAR DA YA KAMATA KOWANE ƊAN UWA YA SAN SU

Daga Sheikh Sunusi Abdulkadir

"Abubuwa ne guda biyar wanda ya kamata kowane ɗan uwa ya san su, Su Malam (H) suna cewa a manta da abin da ya faru a baya wato lokacin dasu Malam suna tsare a hannun azzalumai ta iya yiwuwa 'yan wasu abubuwa sun ɗan faffaru a tsakankanin mu (mu 'yan uwa) to Malam (H) yace a manta. Na biyu kuma Malam yana cewa a yafewa juna, wato dai koda wani yayi maka laifi har ga Allah kaji ka yafe masa".

"Na uku Malam yana cewa a buɗe sabon shafi, to daga nan ne muka samo gwagwarmaya a sabon shafi. Na huɗu kuma Malam yana cewa wato a haɗu ayi aiki tare, ba dai-dai bane ko bai kamata ba ace yan uwa suna haɗe suna tafiyar da abu sai ya zamana waɗansu sai su ɓalle s**e mu 'yanzu ai baza mu haɗu dasu wane ba, ai anyi kaza-kaza-kaza, ba dai-dai bane kuskure ne".

"Sannan kuma su Malam suna cewa a yi don Allah (wato a sa Iklasi) kar mutum ya dinga yin gwagwarmayar nan ko aikin gwagwarmayar nan da wata manufa, manufar nan ta neman duniya ko ta neman shugabanci ko ta neman tabbata akan shugabanci ko ta neman kuɗi ko ta neman suna koma wani irin abu ne indai ba neman yardar Allah bane to laifi ne. Ana yin gwagwarmaya ne kawai saboda neman yardar Allah".

— Dr. Sunusi Abdulkadir a cikin jawabin sa jiya Litinin 16/01/2023 a garin Saminaka jahar Kaduna.

Address

Magazu
Asokoro
THANKS

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamfara media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zamfara media:

Share