Mujallar Kwankwasiyya

Mujallar Kwankwasiyya is a political news on kwakwasiyya, it was created by comrade JILI to print online news based on kwankwasiyya around the globe

Fact
14/08/2024

Fact

Gwamna Abba Kabir Yusuf Bawan Allah har yashiga mota yazauna Sai ga wata baiwar Allah, tace yana ina akace mata yana cik...
02/07/2024

Gwamna Abba Kabir Yusuf Bawan Allah har yashiga mota yazauna Sai ga wata baiwar Allah, tace yana ina akace mata yana cikin mota, tace gaisheshi nazo nayi sai akacemata ai yariga yashiga cikin mota, tace to nidai kutaimaka inaganshi mugaisa ana cikin wannan dambarwar da Hajiya ashe Mai Girma Gwamna ya hango mu kawai sai gani mukai yataso ya futo Hajiya tana ganinsa tace Alhamdulillah Allah Nagode maka.

Shine Gwamna yace adaukesu a hota yaiwa Hajiya Godiya bisa irin Addu'oin datayi agareshi 🙏

 WASU DAGA AIYUKAN MAI GIRMA GWAMNA ENGR. ABBA KABIR YUSUF A SHEKARA DAYA BANGAREN ILIMI1. Mayar da jarrabawar WAEC, NEC...
29/05/2024



WASU DAGA AIYUKAN MAI GIRMA GWAMNA ENGR. ABBA KABIR YUSUF A SHEKARA DAYA

BANGAREN ILIMI

1. Mayar da jarrabawar WAEC, NECO da NABTEB kyauta ga yan makarantun sakandare.

2. Zabtare kudin makarantun gaba da sakandare da kaso 50 cikin 100

3. Kai dalibai masu hazaka 1001 kasashen waje don digiri na biyu

4. Biyawa daliban wasu daga jami'o'in gwamnatin tarayya kamar BUK, FUD, da ABU kudin makaranta

5. Fara gyaran makarantun firamare da sakandare da s**a lalace a fadin jihar Kano

6. Dawo da makarantu 26 da tsohuwar gwamnati ta rufe.

7. Hadin gwiwa da Bankin Duniya don ci gaban ilimin fasaha da na sana'a (Technical and Vocational)

8. Kammala gyaran makarantar Fasahar Sadarwa da ke Kura

9. Samar da tallafin karatu ga daliban gaba da sakandare na jihar Kano

10. Raba fom din jarrabawar JAMB ga dalibai 6,500 yan jihar Kano.

11. Yarda da biyan kudi miliyan 75 domin samar da sababbin kwasa-kwasai (accreditation) a makarantun Polythechnic.

12. Dawo da kwamitin CRC a fadin jihar Kano

MANYAN AIYUKA

13. Aikin rufe babbar kwata daga Jakara zuwa Kwarin Gogau (Wuju-Wuju)

14. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Dawakin Kudu

15. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Gwarzo

16. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Bebeji

17. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Albasu

18. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a t**in Rano zuwa Rurum

19. Aikin t**in 5 kilomita mai hannu biyu a Kabo

20. Aikin t**in 5 kilomita a Gezawa

21. Gyaran manyan kwalbatoci biyu da s**a hade Rano da Rurum

22. Gyarawa da canja karafan raba t**in Katsina

23. Gyaran gadojin tsallaka t**i a kusa da makarantun BUK, Sa'adatu Rimi, Legal, da sauransu.

24. Kammala gadojin tsallaka t**i na karfe a Kurna Babban Layi kusa da masallacin Kandahar.

25. Kammala gadar siminti a t**in Sheikh Ja'afar, Kwanar Dawaki, Rumfa Kwaleji, da kuma Titin Gwarzo.

26. Gyaran t**in Kuntau-Dorayi Babba.

27. Kiyayewa daga zaizayar kasa a gadar Garanga dake Bunkure.

28. Yin kwatoci a unguwar Indabawa da ke Karamar Hukumar Birni.

29. Kammala gyare-gyare a biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo

30. Gyaran masallacin Idi.

31. Yin manyan kwalbatoci a Rafin Gora da Rafin Zur da ke Karamar Hukumar Rano

32. Kananun gyararraki a duka titunan jihar Kano

33. Bayar da kwantaragin biliyan uku da miliyan dari shida domin fadada t**in Zaria

34. Fara gyaran makarantun Technical a fadin jihar Kano

35. Fara yin gadar kasa a t**in Dan Agundi

36. Fara yin t**in sama a t**in Tal'udu.

37. Fara saka fitulan solar a fadin titunan jihar Kano

38. Gyaran makarantar Bagauda

39. Gyaran sakatariyar Audu Bako

40. Aikin t**in Hotoro zuwa Unguwa Uku

41. Fara gyaran duka makarantun koyon sana'a guda 22 a jihar Kano (Vocational Schools).

42. Gyaran gadar Kasa ta Muhammadu Buhari (Kabuga da Kofar Ruwa)

43. Ginin ofisoshi da masallacin mata da dakin taro a hukumar Hisbah.

44. Gyaran hukumar shari'a ta jihar Kano (Law Reform Commission)

45. Ginin gidaje guda takwas da gyaran katangar gidan gwamnatin Kano

46. Ginin bangaren buge-buge na zamani a hukumar ɗab'i ta jihar Kano

47. Sabunta makarantar kiwon dabbobi ta Bagauda.

48. Gyaran t**in Bayero-Soli da kuma samar da hanyar shiga a kusa da rukunin gidajen Ado Bayero Mall.

49. Ginin kwalbatin da ta rushe a hanyar Takai-Fajewa - Kayarda - Birnin Bako a karamar hukumar Takai.

BANGAREN LAFIYA

49. Kwacewa da gyaran asibitin yara na Hasiya Bayero

50. Bawa yara sama da 200,000 magani kyauta a asibitin Hasiya Bayero

51. Sabunta asibitin Sir Sanusi General Hospital

52. Sabunta asibitin Nuhu Bamalli.

53. Sabunta asibitin BELA

54. Samar da tsarin haihuwa kyauta

55. Yawon duba marasa lafiya a kauyukan jihar Kano

56. Kaddamar da tsarin "Abba Care" don kula da masu cutar sikila a fadin jihar Kano.

57. Gyara da sake ginin asibitin Murtala Muhammad

58. Siyan motocin ambulance don amfanin kananan hukumomi

59. Diban ma'aikatan lafiya da likitoci guda 106 a fadin jiha.

60. Daukan manyan likitoci "consultants" don su taimakawa asibitoci wajen samar da lasisin bude wasu ɓangarori kamar ENT, family medicine, gynecology da sauransu.

61. Samar da tsarin gwajin masu niyyar aure don kiyaye lafiyarsu

62. Hadin guiwa da Global Health Partners don zuwa dollar million hamsin cikin shekara uku a harkar lafiyar jihar Kano

63. Hadin gwiwa da gidauniyar Bill and Melinda Gates domin tallafawa harkar lafiya a jihar Kano

64. Biya don saka kayan ICU na zamani a asibitin Murtala Muhammad

65. Samar da motocin aiki ga bangarorin lafiya guda uku na jihar Kano

BANGAREN JIN KAI

66. Rarraba hatsi kyauta ga masu karamin karfi, taki da kayan aikin noma ga manoma a jihar don rage tasirin cire tallafin man fetur.

67. Fara kashin farko na na Auren Zaurawa

68. Raba shinkafa da masara 457,000 kilogiram 10 a matayin tallafi ga unguwanni 484 da ke jihar.

69. Shirin ba da tallafi na wata-wata ga mata na basu jarin N50,000 da yanzu ya samarwa mutane 5,200 a fadin jiha.

70. Kashi na 2, na 3 da na 4 na rabon kayan jin kai (palliative) a fadin jihar

71. Rarraba kayan amfanin gona irin su shinkafa da irin masara da akuya da injinan fanfo ruwa ga mata kusan 1000 a jihar.

AIKIN GWAMNATI

72. Biyan duk wasu basuss**an kudaden fansho na wadanda s**a yi ritaya daga aikin gwamnati na jihar Kano.

73. Dakatar da cirar da ba dole ba daga albashin ma'aikatan jihar da wadanda s**a yi ritaya.

74. Biyan kashi na biyu na bashi ga ’yan fansho da gwamnatin da ta shude ta hana biyansu na tsawon shekaru. An ware biliyan biyar don hakan.

75. Buga sakamakon taron majalisar zartarwa na mako-mako a jaridu da shafukan sada-zumunta

76. Horowa, sake horarwa, da haɓaka ingantaccen yanayin aiki don haɓaka yawan aiki da haɓaka ingancin sabis.

77. Samar da majalissar biya da bibiyar hakkin yan fanshon da s**a mutu.

RUWAN SHA

78. Amincewa da Naira Miliyan 225 don samar da ton 600 na Aluminum Sulfate (Alum) ga ma'aikatun sarrafa ruwa na jihar.

79. Sayan ƙarin injunan bututun ruwa daga Jamus waɗanda za su kasance a matsayin tsarin ajiya idan aka sami lalacewa a nan gaba.

80. Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a kauyukan Danya da Kyallin Bula da ke karamar hukumar Bichi da Bebeji a jihar Kano bayan shafe shekaru 40 ana fama da karancin ruwa.

81. Aikin gyara na ci gaba a Hukumar Albarkatun Ruwa ta (WRECA), don kammala aikin gyarawa tun daga Tushen Ruwa na Tamburawa.

82. Ci gaba da babban gyara a bangaren tace ruwa na Challawa..

83. Gwamnatin jihar Kano ta cimma matsaya da gwamnatin Faransa na zuba jarin Yuro miliyan 63.4 domin gina kamfanin samar da ruwan sha na Kano karo na uku.

84. Gyara magudanar ruwa da ta tarwatse don hana ambaliyar ruwa ta kowace shekara a lokacin damina a fadin jiha.

NOMA

85. Samar da jimillar gidaje 500,000 don cin gajiyar shirye-shiryen Gwamnatin Jiha ta Tallafawa Noma.

86. Samar da ingantaccen kayan aikin noma ta hanyar KASCO

87. Kokarin dasa itatuwa miliyan 2.5 a jihar domin dakile tasirin sauyin yanayi

88. Dawo da shirin tallafin aiyukan kiwo

89. Gyaran asibitin dabbobi na Gwale

90. Kimanin matasa 200 ne aka horas da su tare da ba su damar gudanar da ayyukan kiwon dabbobi masu zaman kansu a kananan hukumomi 44 na jihar.

91. Haɓaka Cibiyar Insemination na Kadawa, gyara wurin da samar da kayan aiki na zamani.

92. An fara shata shataletalen hanyoyin dabbobi kusan kilomita 1,950 don magance rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.

93. An tallafa wa mata 2,357 da raguna da tumaki da akuya domin yin kitso da hayayyafa ta hanyar aikin noma na manoma na jihar Kano (KSADP).

94. An baiwa manoman gyada 1,200 ‘Aflasafe’ a karkashin shirin sarkar darajar legumes na KNARDA domin hana asara bayan girbi.

95. Sayan famfunan ruwa guda 2,050 wanda kuma aka baiwa manoman a matsayin wani abin karfafa gwiwa.

96. Gwamnatin jiha a karkashin shirin Agro Processing and Productivity Enhancement and Livelihood Support (APPEALS) na tallafawa manoma 300 akan noman shinkafa, alkama, da tumatur mai daraja.

Bamuyi za6en tumun dare ba

Sen. Kwankwaso Visit Cameroon 🇨🇲 National Leader of New Nigeria People's Party, NNPP Sen Rabiu Musa Kwankwaso PhD FNSE t...
01/05/2024

Sen. Kwankwaso Visit Cameroon 🇨🇲

National Leader of New Nigeria People's Party, NNPP Sen Rabiu Musa Kwankwaso PhD FNSE today (1st May, 2024) arrived at Nsimalen International Airport, Yaoundé, Cameroon on a private visit.

He was received by some Cameroonian National Assembly members, Hon Abubakar, Dr. Abdouraman, Hon Yakubu, Chief Imam of Cameroon Grand Mosque, Sheikh Saminou and Sarkin Hausawa of Cameroon including other Nigerians leaving there.

Saifullahi Hassan
Media aide to Sen Kwankwaso

 !Koya yasan halin da Talakawan   suke ciki, na Kunchi tare da matsin rayuwa. A baya bayan nan bayan  hauhawar kayan mas...
01/05/2024

!

Koya yasan halin da Talakawan suke ciki, na Kunchi tare da matsin rayuwa.

A baya bayan nan bayan hauhawar kayan masarufi, sai ga Matsalar manfetir ta kunno kai!

Babban abin takaicin shine kasa kamar , Muke sayan man fetir fiye da Naira Dari Tara (900) a duk lita. wanda a baya ko Naira Dari Uku (300) a kace zamu saya zamu ce karya ne duba da arzukin man fetir din da ya bamu.

duk da wannan hali na kunchi tare da matsi da talakawan muke ciki, (RARA) Yaki magantuwa akan hakan. Kawai sai mukaji ya wake .

A baya yayi wakoki domin a za6i wannan gwamnatin kamar yadda yayi ikirarin yana daya daga cikin wadan da s**a sa aka kafa wannan . Amma sabida tsabar rainin wayo sai gashi yana wakeh don kawar da hankalin kan halin da wannan gwamnatin tasa Talakawan Nigeria a ciki.

A karshe muna kira ga Gwamnatin Nigeria dama dukkanin Masu fada aji dasu duba halin da talakawan mukeh ciki, ko ma samu sauki.

ya kawo mana sauki

✍️✍️✍️✍️

Cikin Yardar Allah yadda Aikin Asibitin kulawa da Mata da kananan yara na Bamalli Nuhu dake yankin birnin kano yake guda...
30/04/2024

Cikin Yardar Allah yadda Aikin Asibitin kulawa da Mata da kananan yara na Bamalli Nuhu dake yankin birnin kano yake gudana cikin Nasara.

karkashin jagorancin Mai Girma Gwamnan jihar Kano H.E Alhaji Abba

Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)

Taron Gwamnonin Arewacin Nigeria kenan daya gudana a Gidan gwamnatin jihar Kaduna, Mataimakin Gwamnan Kano Comrd Aminu A...
30/04/2024

Taron Gwamnonin Arewacin Nigeria kenan daya gudana a Gidan gwamnatin jihar Kaduna, Mataimakin Gwamnan Kano Comrd Aminu Abdussalam Gwarzo Ya wakilci gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf a gurin. Antattauna Muhimman batutuwa na tsaro da kawo cigaba da Inganta noma da Kasuwancin Arewacin Nigeria.


30 April 2024.

 !Bazan dena kira ga Danmajalissa mai wakiltar   ba har sai mun ga gyara.idan muka kalli sauran wakilin da aka tura waki...
19/04/2024

!

Bazan dena kira ga Danmajalissa mai wakiltar ba har sai mun ga gyara.

idan muka kalli sauran wakilin da aka tura wakilci a majalissar tarayya sai kullum nayi kuka da idona tare da yin takaici duba da yadda suke shan roman sa6aninmu.

Nasan mutane zasu gasgata ni idan nace kaf ta arewa babu cima baya ko kuma wadda akayi wa nisa irin , a fannin samar da Ayyukanyi ga matasa, Ayyukan more rayuwa tare da gina Dan'adam.

Babban abin takaicin shine kaf Kano ta arewa babu wanda ya kai wannan wakili namu da dewa a , wanda ni a tuna nina kamata yayi ace munfi kowa kwankwatar romon dimokradiya fiye da kowacce maza6a a Kano ta Arewa.

Ba zan gushe ba zanci gaba da kira tare da janyo hankalin wannan Dan majalissa namu, ko ya dubi wannan yanki namu tare da samar wa Matasa Aiyukanyi, Aiyukan more rayuwa tare da gina Al'Ummar wannan Yanki.

Ya mai girma Member ka tuna cewa ita rayuwa komai lokachi ne, kuma ubangiji shike bada mulki ga wanda yasa a kuma lokacin da yaso. Don haka zai iya kar6a ya kuma bawa wanda yakeh so a kuma lokacin da yakeh so.

mai girma Member ba kiyayya ko adawa ce tasa nakeh maka hakan ba face cewa mu mukabi lungu da sako domin nemo yarda tare da amincewar Talakawa kan su fito su za6eka domin kayi mana Alkawarin zaka Gyara.

A karshe ina mai fatan mai girma member zai chanza tare waiwayar wannan maza6a tasa mai Albarka, ka tuna cewa kai ne shugaban kwamitin yakar a majalissa! to muna so kayi amfani da wannan dama domin gina rayuwar Al'ummar wannan yankin, ko muma ma samu abin fada a matsayin mu na "Yan siyasa. Domin 2027 ta ce shi yasan wa zai bawa damar wakiltar mu a zauran majalissa.

!!

naku;
✍️

Matsalar Tsaro: Ƴan Bindiga sun sace ɗalibai 3 a Jami’ar Kalaba da ke jihar Kuros Ribas
01/04/2024

Matsalar Tsaro: Ƴan Bindiga sun sace ɗalibai 3 a Jami’ar Kalaba da ke jihar Kuros Ribas

01/04/2024
 SANARWA SANARWA SANARWA       GAYYATA GAYYATAGa Kafitanin Yayan Wanan Kungiya Mai Suna A Sama Karkashin Jagorancin Chai...
15/03/2024



SANARWA SANARWA SANARWA
GAYYATA GAYYATA
Ga Kafitanin Yayan Wanan Kungiya Mai Suna A Sama Karkashin Jagorancin Chairman Nata Hon Kamilu A Bala Zakin Kwankwasiyya Tana Sanar Da GaGarumin Taro Data Saba Gabatarwa Dukk Shekara (7) Ga Ramadan Domin Tattauna Mushiman Batutuwa Dazasu Kawowa Alummar Jahar kano Cigaba Da Kasa Da Yayan Wanan Kungiya Zuwanka Zuwanku Zuwanki Zuwanmu Yana Damatukar Mashimmanci Domin Isar Da Wani Mushiman Sako Ga Kowa
Wurin Taro :Kabuga Office
Lokaci Taro: 10:00Am
Ranar Taro:Lahadi :17/03/2024 Wadda Yai DaiDai Da

  YAYAI NASARA
29/11/2023

YAYAI NASARA

Address

Asokoro

Telephone

+2347039804718

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujallar Kwankwasiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category