
13/07/2025
ALLAHU AKBAR RAYUWA
Maigirma Shugaban Kasa Tinubu ya tabbatar da mutuwar Shugaba Buhari a birnin London, yace Shugaba Buhari ya rasu yau Lahadi da misalin karfe hudu da rabi na yamman nan
Sannan Shugaba Tinubu ya tura Mataimakinsa Kashim Shettima zuwa London domin ya dawo da gawar Shugaba Buhari Nigeria, kuma ya bada umarni a sauko da tutar Nigeria kasa-kasa domin tunawa da girmama Shugaba Buhari
Shugaba Tinubu Yace Yayi Magana da Aisha Buhari ta waya
Don Allah jama'a kowa yafe wa Shugaba Buhari
Yaa Allah Ka sa jinyar da yayi ta zama kaffara a gareshi