
17/09/2025
WATA SABUWA:~ Ni da Barrister Abba Hikima mun yanke shawarar komawa kotu akan kudaden N-Power da Ministan Jinkai Nentawe s**a ce an kusa biya tun July.
Zamu koma kotu a karshen wannan wata sanda kotu ta dawo hutu mu cigaba da case. Mun basu wa’adi ne bayan sun bayar da hakuri amma yanzu hakurinmu ya kare saboda ba mu ji daga gare su ba, duk da alkawari da su ka yi.