12/08/2024
Babu adalci Ga masu iƙrarin Shugaba Tinubu ya fifita yankin Kudu fiye da Arewa Inji Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi tsokaci kan zage-zagen da ake yi cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da yankin Arewa, yana mai cewa irin waɗannan ikirari ba su da tushe b***e makama. Ya kuma jaddada cewa, bai kamata yankin Arewa ya fuskanci talauci ba, ganin dimbin albarkar dake cikinsa.
A wata hira da Rediyo Faransa RFI da Sashen Hausa na RFI da ke sa ido a Kaduna a ranar Lahadi, Shettima ya tattauna kan zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, inda ya ce, “A tsarin dimokuradiyya, ‘yan kasa na da ‘yancin fadin kokensu cikin lumana. Duk da haka, dole ne mu guji barin ’yan siyasa masu mugun nufi da ’yan iskanci su tada fitina da rashin zaman lafiya. Abin takaici, irin wannan tarzoma ta faru.”
Shettima ya yarda cewa yayin da Shugaban kasa ke goyon bayan 'yancin 'yan kasa, abubuwan da s**a faru na baya-bayan nan sun kasance masu damuwa ga al'umma da gwamnati.
Dangane da tallafin da ake bai wa Arewa, Shettima ya ce, “Gwamnati ta dukufa wajen taimakawa al’ummar Arewa. Mun ware Naira Biliyan 100 don tallafa wa harkar noma da kuma shirin tallafa wa manoma miliyan 500, wadanda yawancinsu ‘yan Arewa ne. Bugu da kari, shugaban ya kafa ma’aikatar kiwo domin tallafa wa makiyayan da s**a fi yawa a Arewa. Mun kuma raba kimanin tan 42,000 na abinci daga asusun gwamnati don magance tsadar rayuwa da tsadar abinci.”
Akan ma’aikatan gwamnati, Shettima ya bayyana karin albashi mafi karanci daga N30,000 zuwa N70,000 tare da tabbatar wa ‘yan kasar kudurin shugaban kasa na magance matsalolin da suke ciki. Ya kara da cewa "Mun amince da matsalolin da mutane ke fuskanta kuma mun kuduri aniyar daukar matakan da s**a dace don rage musu radadi."
Shettima ya jaddada cewa, “’yan siyasar da ke ikirarin cewa gwamnatin ta fifita Kudu kan Arewa, ba Gaskiya suke ba. Daga cikin ministoci 46, 24 daga Arewa ne. A tarihance, babu wata gwamnati da ta samu wakilan Arewa masu yawa a manyan mukamai. Misali, Ministan Tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar, dan Jigawa ne, sai kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle Maradun, dan Zamfara ne. Ministan Noma, Abubakar Kyari dan Arewacin Borno ne, kuma Ministan Ilimi Tahir Mamman dan Adamawa ne.”
Shettima ya musanta zarge-zargen nuna son kai, inda ya bayyana cewa wakilcin gwamnati da ayyukanta na nuna aniyar magance bukatun dukkan yankuna.
KCB Hausa News