
17/07/2025
DA DUMI DUMI: Iyalan Marigayi Janar Buhari Za Su Rika Karban Albashi 300,000 Duk Wata.
A yunkurin gwamnatin tarayya na kyautata goben iyalan Marigayin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Buhari, gwamnatin tarayya zata rika bawa iyalan nasa naira dubu dari uku duk wata tare da basu alawi-alawi naira dubu dari biyu da hamsin duk karshen shekara, za a gina masu gida daya a duk In da su ke so a fadin Najeriya gwamnati zakuma ta basu motoci uku.
Bugu da kari gwamnatin tarayya zata bawa Iyalan tsohon Shugaban Ƙasar jami'an tsaro guda hudu, biyu 'yan sanda biyu na farar kaya, sannan za a rika fita dasu yawon bude ido duk shekara, bihasali tare da duba lafiyar su kyauta tun daga gida Najeriya har wajen kasar.
Shin ko menene ra'ayoyin ku game da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka kan iyalan Marigayin?