03/09/2026
LABARI DA DUMI-DUMI
Sheikh Malam Zakzaky ya magantu kan taron da ‘yan Wahabiyya s**a gudanar a Abuja, wanda s**a gayyato wani da suke cewa malami ne daga ƙasar Saudi Arabia, wai domin samar da zaman lafiya a wannan ƙasa.
Shehin malamin ya yi dogon bayani a cikin jawabinsa, inda ya bayyana cewa ai kowa ya san suwaye ke ta da fitina a wannan ƙasa. Har ma ya ambaci wani sabon suna da waɗannan malamai suke amfani da shi, wanda a yanzu duk wanda ka ji ana cewa Lakurawa, wannan sabon sunan nasu ne.
Sai dai a yanzu Lakurawa kala biyu ne: akwai na cikin gari, akwai kuma na daji, k**ar yadda ya faru shekarun baya. Ba komai ne ya sa ake kwatanta waɗannan da waɗanda s**a gabata ba, sai irin koyarwar da suke yi, wadda ake ganin iri ɗaya ce.
Wannan ya sa ya zama dole Atba’uddalil TV ta fito ta yi wannan shimfiɗa, domin duniya ta sake fahimtar waɗannan mutane, duk da cewa mun san wasu sun shiga cikin gwamnati.
Sai kuma sak**akon fitowar Sheikh Yahaya Ibrahim Masusss**a, ita ma gwamnati ta fahimci suwaye da ake zargin suna haifar da masifar wannan ƙasa.
Saboda haka, muna kira ga shugabannin wannan ƙasa da su sa ido sosai a kansu, su daina yin sakaci da wannan ƙasa. Haka kuma muna kira da a yi nazari sosai kan irin tasirin da wasu ƙasashe da cibiyoyi ke da shi wajen wannan lamari.
Muna miƙa saƙon godiya ga Sheikh Ibrahim Zakzaky. Allah Ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.
Atba’uddalil TV — Tsage Gaskiya, Komai Dacinta.