03/09/2025
Gwamnan Bauchi ya gargaɗi Wike
Shugaban ƙungiyar gwamnanonin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed ya ce jam'iyyar ta gaji da mutanen da ke jefa ta cikin rikici.
Gwamnan Bauchin na mayar da martani ne kan sharuɗan da tsagin Nyesom Wike ya gindaya kan gudanar da babban taron jam'iyyar na ƙasa. Tsagin na Wike ya gindaya wasu sharuɗɗa da ya ce dole jam'iyyar ta bi idan tana son komai ya tafi yadda ya kamata.
Sharuɗɗan sun ƙunshi dole shugaban jam'iyyar ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.
Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar a Ebonyi da Anambra
Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar na Kudo maso Gabas
Amincewa da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calaba
Sake zaɓen shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomin a Ekiti ba tare da ɓata lokaci ba
To sai dai yayin martanin nasa, gwamnan na Bauchi ya ce jagororin PDP mutane ne da s**a san ciwo kansu.
“Ba za mu ci gaba da yin shiru muna barin wasu mutane suna yi mana yawo da hankali ba.'' in ji shi.
Gwamnan ya ce, “Shugaban jam'iyya na ƙasa ya yi magana da kyau, babu wani kokwanto game da jagorancin kwamitin shirya babban taron ba, domin sun yi a baya, kuma mun yi imanin za mu yi nasara'', in ji shi.
Jam'iyyar PDP dai ta faɗa rikici tun gabanin zaɓen 2023, matsalar da wasu masana ke alaƙanta rashin nasarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar.