Hausa Online

Hausa Online Ziyarci shafin Hausa Online, Domin karanta Sahihan labarai Cikin harshen Hausa. Chibiyan Yada Sahihan Labaran Duniya

01/07/2025

SAM SAM BABU FASHI...

18/06/2025
07/06/2025

Barka da sallah...

28/05/2025

Duk Mai zagin shugaba. zai iya zagin Iyayensa, Ko kana da ja ne?

Allah ya shiryar da 'yan Nigeria 🙏

MAGANAR LAFIYA TINUBU YA SAMU YABON BUHARI, NASIHA A TSAKIYA Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasa...
28/05/2025

MAGANAR LAFIYA

TINUBU YA SAMU YABON BUHARI, NASIHA A TSAKIYA Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara guda, yana mai cewa yayin da jam’iyya da gwamnati ke murna ya k**ata a tunatar da kasar nan cewa shugabanci tafiya ce mai ci gaba.

Muhammadu Buhari ya yi kira da a ba gwamnatin APC goyon baya a daidai lokacin da take cika shekara biyu a kan karagar mulki, inda ya bayyana cewa gyara za a samu nasara a hankali ba dare daya ba.

Ya yi gargadin cewa sauye-sauyen da ake bukata da sauye-sauyen da ake bukata kada su fada cikin mummunan siyasar cikin gida.

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga kokarin da gwamnatin ke yi na dakile fatara da hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya ce ya fi yiwa iyalai wahala, duk da haka aikin rage radadin talauci da hauhawar farashin kayayyaki da ke da yawa, bai k**ata a bar wa gwamnati kadai ba.

"Kamfanoni masu zaman kansu da dukkanmu a matsayinmu na 'yan kasa dole ne mu shiga duk hanyoyin da za mu iya."

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu kyakkyawan fata kuma su kasance da kwarin gwiwa game da makomar kasar.

“Kada fatanmu daga gwamnatocinmu ya yi nauyi,” in ji Shugaba Buhari a karshen sakonsa.

"Ina yi wa Shugaba Tinubu fatan alheri bisa shekaru biyu da ya yi a ofis. Allah ka ci gaba da jagoranci cikin hikima da kulawa."

Sa hannu Garba Shehu
28 ga Mayu 2025

12/05/2025

RIBAR DEMOKRADIYYA

Taja kaya....
22/01/2025

Taja kaya....

NEMAN ADALCI GA YAKUBU DA AMARYA SA.Wannan shine matashin da aka kaishi gidan yari dashi da amaryar sa, ana nema musu sh...
05/01/2025

NEMAN ADALCI GA YAKUBU DA AMARYA SA.

Wannan shine matashin da aka kaishi gidan yari dashi da amaryar sa, ana nema musu shekar iskan .

Yanzu haka suna gidan gyara hali dake Yolde Pate, Yola na Jihar Adamawa.

Yakubu ya nemi auren A'isha k**ar yadda addinin Musulunci da al'ada s**a tanadar kuma an bashi damar biyan dukkan abinda aka umurce shi ya biya aka kuma bashi damar yin shirye shiryen aure.

Bayan wani lokaci, Iyayen A'isha s**a umurci Yakubu ya janye neman auren A'isha ba bisa wani dalili kwakkwara ba.

A'isha ta yanke shawarar zuwa hukumar HISBA don duba kan lamarin nasu.

Bayan bincike da aka gudanar daga ɓangaren biyu na iyayen YAKUBU da Aisha HISBA ta daura musu aure.

Daga Kano YAKUBU ya dawo Yola ita kuma A'isha ta tafi Abuja wajen addar ta don addar A'isha ta roki Yakubu da A'isha taje ta taimake ta bata da lafiya kafin ta samu sauki.

Bayan zuwan A'isha Abuja, aka soma shirin sauya wa A'isha tunani kan angon ta YAKUBU, daga nan A'isha ta yanke shawarar ta dawo Yola gidan mijinta Yakubu.

A lokacin da A'isha ta k**a hanyar ta zuwa Yola aka kira Yakubu a waya akace A'isha ta daukawa addar ta ɗan kunnen da sarka na gold da kudin sa ya kai million 10 hankalin Yakubu ya tashi.

Lokacin da A'isha ta iso Yola ba tare da sanin A'isha ba Yakubu ya hau binciken jakokin ta daga nan ya shaida mata abinda ake zargin ta dashi ta rantse da Allah bata dauka ba.

Daga washe gari Yakubu ya amsa kira daga ofishin yan sanda ana zargin sa da sace A'isha, ita kuma A'isha ana zargin ta da satar gold.

Daga ofishin yan sanda aka tura A'isha da Yakubu CID daga nan aka tura su kotu inda ake zargin Yakubu da sace A'isha wannan shine laifin da aka tsaya a kai.

Rahotanni na cewa ana bukatar YAKUBU da ya saki A'isha kafin su sami iskar yanci.

Wannan shine jawabin iyayen YAKUBU, su kuma ta bangaren A'isha sunki cewa komai a cewar su magana na Kotu sai abinda kotu ta zartar.

Akwai shikken hirar ga masu bukatar don .

Karin bayani
09115203031

28/12/2024

Allah ya albarkaci rayuwanmu duniya da lahira 🙏

Wasu sojojin Isra'ila sun ce ba za su ci gaba da yaki baAkalla sojojin Isra'ila 130 s**a rubuta wasika wa gwamnatin kasa...
21/10/2024

Wasu sojojin Isra'ila sun ce ba za su ci gaba da yaki ba

Akalla sojojin Isra'ila 130 s**a rubuta wasika wa gwamnatin kasar cewar ba za su ci gaba da yaki ba, muddin hukumomin kasar ba za su dauki matakin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktobar bara ba. A wata wasikar da s**a rubuta ta ranar 9 ga wannan watan, sojojin da wadanda aka kira domin yiwa kasar yaki sun ce sun fahimci gwamnatin kasar ba ta son kawo karshen yakin domin gudanar da zabe. Daya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yakin da kasar ke yi. Sojan ya ce wannan wani matsayi ne ya dauka na bijirewa gwamnatin kasarsa saboda yadda ta kai matakin karshe na yaudara. Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da tintini anyi nasara, amma ana tsawaita yakin ne domin kin gudanar da zabe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki. Rahotanni sun ce wasikar ta harzuka gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.

📷 Reuters

Jaridan Amana Ta Karrama Umar Abdullahi Ajiya a Matsayin Gwarzon Shekaran 2024An Karrama Mai Neman Sanatan Bauchi Ta Kud...
21/10/2024

Jaridan Amana Ta Karrama Umar Abdullahi Ajiya a Matsayin Gwarzon Shekaran 2024

An Karrama Mai Neman Sanatan Bauchi Ta Kudu Engr Umar Ajiya da Lamban Yabo Bisa Tallafawa Mata da Matasa

Daya daga cikin manya Jaridun Najeriya wanda take da ofishin ta a Babban Birnin tarayya Abuja ta karrama daya daga cikin yayan jihar bauchi kuma daya daga cikin mutanen da kungiyoyin mata da matasan shiyar Bauchi Ta Kudu a jihar Bauchi ke kira da su fito su nemi kujeran Sanatan Bauchi Ta Kudu a babban zaben Shekaran 2024

Jaridan Amana Newspaper Hausa ta Karrama Injiniya Umar Abdullahi Ajiya, a Matsayin Gwarzon Shekaran 2024 bisa irin kokarin sa na inganta rayuwan mata da matasan kasancewan sa matashi wanda ya dauki lokaci yana taimaka ma mutane musamman kan harkokin ilimi da samar da aiyukan dogaro da kai da tallafin karatu

Jaridan Amana Newspaper Hausa ta dauki tsawon lokaci ko muce Shekaru tana Karrama Yayan jihar Bauchi musamman mutanen da s**a bada gudumawan su sosai wurin ci gaban al'umman su da inganta rayuwan al'umma musamman bangarurin da s**a shafi yan siyasa yan kasuwa Malamai Dalibai dama kungiyoyi masu zaman kansu Wanda s**a bada gudumawan su wurin ci gaban al'umman
a Shekarau da s**a gabata kamun wannan abaya wannan Jarida Ta Amana Hausa ta Karrama mutane irin Hon. Faruk Mustapa tsohon Dan takaran Gwamnan jihar Bauchi a jam'iyan APC a Shekaran 2023 kuma yanzu Kwamishina a gwamnatin jihar Bauchi, haka kuma wannan Jarida abaya ta karrama tsohowar Kantoman riko na karamar hukumar Bauchi Hon Zainab Baban Takko, haka kuma ta karrama babban Dan kasuwan nan a jihar Bauchi wato Alh Adamu Manu Abdulkadir Soro, CEO/MD Soro Petroleum Nigeria Nig, Lmd da tsohon shugaban babban kasuwan bauchi na Central Market wato Alh Muhammad S. B haka zalika Jaridan Amana ta Karrama Alh Muntaka Muhammad Duguri haka zalika a bangaren ilimi Jaridan Amana abaya ta karrama Tsohon shugaban kungiyar Dalibai yan asalin jihar Bauchi wato (NUBASS) Kwamared Adamu Dauda Yashi

Sai kuma wannan Shekaran na 2024 kanda Jaridan Amana Newspaper Hausa ta Karrama daya daga cikin yayan jihar Bauchi masu gwazo da aiki tukuru wurin ganin ya inganta rayuwan al'umman sa musamman mata da matasa wato Injiniya Umar Abdullahi Ajiya, kuma daya daga cikin yayan jihar Bauchi da kungiyoyin mata da matasan jihar Bauchi musamman Shiyar Bauchi Ta Kudu ke ci gaba da kira ya amsa kira da ya fito ya nemi kujeran Sanatan Bauchi Ta Kudu a Zaben Shekaran 2024.

Daga Malam Ahmadu Manaja Bauchi.

Arziƙin Aliko Dangote ya ninka ne zuwa dala biliyan 28 bayan matatar man da ya gina ta fara aiki a watan Satumba, k**ar ...
18/10/2024

Arziƙin Aliko Dangote ya ninka ne zuwa dala biliyan 28 bayan matatar man da ya gina ta fara aiki a watan Satumba, k**ar yadda mujallar Bloomberg ta bayyana.

A watan da ya gabata ne Dangote ya shaida wa BBC cewa matatarsa tana iya samar da fiye da man da ake buƙata a Najeriya.

Address

Azare

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category