30/12/2025
2026 🌙✨
Ya AL-LATIF (Mai tausayi da kyautatawa ta ɓoye): Ka haɗa mu da mutanen kirki a cikin wannan shekarar, sannan Ka siffanta mu da kyawawan halaye yadda za mu zama silar farin ciki da kirki a rayuwarsu.
Ya AL-BARR (Mabubbugar dukkan alkhairi): Ka haɗa mu da mutane masu halacci da sanin darajar dangantaka. Ka sa mu zama masu cika alkawari da nuna halacci ga duk wanda ya kyautata mana.
Ya AL-WADUD (Mai tsananin ƙauna): Ka haɗa mu da masoya na gaske, waɗanda za su ƙaunace mu don kanka, su zama sanyin idaniyar mu, mu ma mu zama inuwar natsuwa a gare su.
Ya AL-FATTAH (Mai buɗe kofofin nasara): Ka buɗe mana kofofin alkhairi da nasara waɗanda ba mu taba tsammani ba. Ka sa 2026 ta zama shekarar buɗi ta fannin dukiya, ilimi, da addini.
Ya AL-HAFIZ (Mai kiyaye komai): Ka tsare mu, Ka tsare iyalai da dukiyoyinmu daga dukkan sharrin mutane da aljanu, da dukkan wata masifa da wannan shekara za ta zo da ita.
Ya AR-RAZZAQ (Mai azurta kowace halitta): Ka azurta mu da abinci da abin sha na halali, Ka sa albarka a cikin sana'o'inmu, Ka wadatar da mu ta yadda ba za mu rinka roƙon kowa ba sai Kai.
Ya ASH-SHAFI (Mai warkarwa): Ka ba mu lafiyar jiki da ta zuciya. Duk wanda yake jarrabacce da rashin lafiya, Ya Allah Ka ba shi lafiya cikakkiya a cikin wannan shekara.
Allahumma Amin. Muna roƙon Allah Ya sanya wannan shekara ta zama mafi alkhairi a gare mu fiye da dukkan shekarun da s**a gabata.
Abdullahi Aliyu Boza ✍️
copied by
Ibrahim Bello Madara