Dutsen-Reme Post

Dutsen-Reme Post Wannan shafi zai dinga kawo muku zafafa kuma sahihan labarukan abinda ke faruwa ba a iya Dutsen-Reme kawai ba, a ƙasa baki ɗaya da ma wajen ƙasar.

12/10/2023

Inalillahi wa'inna'illahirrajiun
ALLAH yayi ma shamsu kabiru na gidan su sule naira rasuwa, yanzu nan a general hospital Funtua bayan fama da yar gajeriyar jinya da yayi , Allah ya jikansa da gafara.

Zana'ida karfe 2:30
Layin chemist din Ibrahim karama ,wajan sola
~ Abdullahi Sanusi Mango

12/01/2023

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

A yau Laraba ne dai ɗan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun haɗu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa ɗan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta riƙa karɓar kuɗaɗe a wajen sa, ya ƙara da cewa " haka na riƙa bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na ɓata mata rai. Ma kashe mata kimanin Naira miliyan 60,"

Ya ƙara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, bar hakan ya ɓata masa rai ya koma Abuja da zama.

"Amma duk da haka ta riƙa kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine soyayyar ta mu ta dawo,"

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kuɗi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta deba kula shi.

"Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni," in ji shi

Alƙalin kotun, Sanusi Ado Ma'aji, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya ɗage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

09/01/2023
05/01/2023

Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi

Yar takarar gwamna a jihar Borno a jam'iyyar ADC, Fatima Abubakar, ta ce tana da kwarin gwuiwar lashe zaben gwamnan na ranar 11 ga watan Maris, duba da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan.

Abubakar, mace daya tilo da ta tsaya takara a zaben ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Maiduguri ra yau Laraba cewa ta fara kamfen gida-gida don jin ta bakin al’ummar jihar.

Ta ce tana samun karin goyon baya da farin jini daga masu zabe, tana mai cewa ta kusa samun nasarar lashe zaben.

“Ina kara samun farin jini tare da karin magoya baya, musamman matan da s**a yi imani da karfina na kawo sauyi mai inganci a rayuwar mata da matasa a Borno.

"Ina so in yi kira ga mata da matasa da muke tuntubar juna, suma su isar da sakon ga wasu kan bukatar a gwada 'yan mata 'yan takara a wannan takara don samun canji mai kyau," in ji Abubakar.

Wasu fusatattun 'yan Boko Haram ne s**a harzuka tare da afka wa bangaren ISWAP, bayan kisan kwamandansu Abubakar Munzir ...
06/12/2022

Wasu fusatattun 'yan Boko Haram ne s**a harzuka tare da afka wa bangaren ISWAP, bayan kisan kwamandansu Abubakar Munzir da karin wasu mayaka 15.

Bayanai na cewa tun a ranar 3 ga wannan wata na Disamba, jagoran Boko Haram na dutsen Mandara, Ali Ngulde tare da ayarinsa s**a kaddamar da farautar 'yan ISWAP da ke a dajin Sambisa.
~ DW Hausa

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fara aiki a safiyar Litinin bayan watanni 9 da kai hari kan jirgin.An dauki sabbin matakai ...
05/12/2022

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fara aiki a safiyar Litinin bayan watanni 9 da kai hari kan jirgin.

An dauki sabbin matakai na tabbatar da tsaro a cikin jiragen, ciki har da tura ‘yan sanda dauke da mak**ai.

An kuma samar da wata na’ura inda fasinjoji za su iya haska tikitin jirgin da s**a siya maimakon bin layi a nuna wa masu duba tikiti.
~ BBC Hausa

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya isa birnin Washington DC na kasar Amurka ...
02/12/2022

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya isa birnin Washington DC na kasar Amurka domin ganawa da manyan jami'an gwamnatin Amurka.

Hotuna:NNPP

Wata uwa ta fille kan danta dan wata 11.Daga BBC HausaGetty ImagesCopyright: Getty ImagesAn k**a wata mai suna Blessing ...
01/12/2022

Wata uwa ta fille kan danta dan wata 11.

Daga BBC Hausa

Getty ImagesCopyright: Getty Images
An k**a wata mai suna Blessing bisa zargin ta da kashe danta dan wata 11 a kauyen Ugep, da ke karamar hukumar Yakurr na jihar Cross River.

Jaridar PUNCH ta ce jami'an 'yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru ne daidai lokacin da matasa ke kokarin lakada wa matar duka.

Lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce yanzu haka matar tana hannun hukuma.

Ugbo ya kara da cewa "ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ta yanka yaron, amma labarin

AN JANYE DOKAR HANA MASU TUKA ADAIDAITA SAHU BIN WASU TITUNA A KANO...Sanarwa ta nuna cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da ...
30/11/2022

AN JANYE DOKAR HANA MASU TUKA ADAIDAITA SAHU BIN WASU TITUNA A KANO...

Sanarwa ta nuna cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar da ta sanya na hana matuka Adaidaita Sahu bin wasu Tituna a birnin Kano...

Sai dai duk da haka, Gwamnatin ta amince da baiwa wasu daga cikin masu tuka Adaidaita Sahu da yan kungiyar masu tuka Taxi sabbin motocin da zasu dinga amfani dasu wajen gudanar da sana'ar tuki a Kano, cewa da nayi An basu ba ina nufin Kyauta ba, an basu bisa Ka'idoji da s**a sanya hannu akai...

Sannan su kansu manyan motocin Saffa da Gwamnatin ta fito dasu kan tituna, zasu cigaba da nasu aikin tare da wadannan sabbin...

Sabbin motocin guda Hamsin ne zasu fara aiki a karon farko, zaa cigaba da fito da wasu sabbin don inganta hanyoyin sifuri a birni da kewaye, akwai ma wasu motocin na musamman da aka tanada saboda masu zuwa daurin aure ko taro a wasu jihohin, mutane zasu je su cika kaida su biya kudi a basu manyan motoci masu AC ko marasa AC ya danganta da wacce ake so....
~Rabi'u Biyora

Aisha Buhari: Kotu ta tura Aminu Muhammad gidan yariDaga BBC HausaBBC ta gano cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake z...
30/11/2022

Aisha Buhari: Kotu ta tura Aminu Muhammad gidan yari

Daga BBC Hausa

BBC ta gano cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba s**a nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

''Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.''

''Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,'' in ji CK Agu.

Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace '' yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.''

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin k**a shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Address

Dutsen-Reme Katsina Road
Bakori

Telephone

+2347032910220

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dutsen-Reme Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dutsen-Reme Post:

Share