
14/04/2025
Idan ka duba halin da muke ciki a Arewa, zaka gane cewa akwai aiki jajawur agaban mu.
Wasu generation ne masu tasowa yanzu, wanda zaka iya kiran su da "NFA-Generation"
(No Future Ambition)
Wasun su Yara ne 'kananu da aka rabo su da uwayen su suna yawo a tituna da anguwanni dan neman abinci ko kudi.
Ga Samari wadanda ya kamata ace suna neman ilimin addini ko na zamani ko neman skills domin dogaro da kai amma babu ko daya.
Wasun su sun zama yan daudu, wasu yan haura katanga ne, wasu yan sara s**a ne, wasu yan bangan siyasa ne, wasu kidnappers ne, wasu yan zaman kashe wando ne sun matar da zuciyar su sun zama "beggers with pride"
Menene yasa malamai da masu wa'azi bazasu fiskanci wadannan matsalolin ba, wadanda sune ainihin matsalan society dinmu?!
Me yasa irin wadannan baza su zama abun tattaunawan mu a kafofi mabanbanta da muke dasu dan neman mafita ba?!
Meyasa attajirai baza suyi gidauniyoyi da cibiyoyi su sadaukar dasu dan ilimantar wa da koyar da sana'u wa samari maza da mata ba?!
Abubuwan takaici da bakin ciki dayawa in kana yawo a garurukan mu na Arewa zaka yita cin karo dasu!
NOTE: wasu yara 'kananu 'yan daudu nagani suna kwarkwasa da maganganun batsa da sunan "content creation" duk cikin su babu dan sama da shekara 15, shine dalilin wannan rubutun.
Allah ya shirya Al ummar mu albarkan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم