13/10/2025
Gwamna Bala Mohammed ya ziyarci karamar Hukumar Alƙaleri don gabatar da Ta'aziyya
A yau Litinin tawagar Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta kai ziyara karamar hukumar Alƙaleri don Ta'aziyyar Rasuwar wasu fitattun mutane a ƴan kwanakin nan.
A Duguri, Gwamna Bala Mohammed yayi ta'aziyyar Rasuwar Malam Husaini Yusuf wanda ɗan uwa ne ga iyalan Gwamnan.
A Gwaram, Gwamna Mohammed yayi ta'aziyyar Rasuwar Malam Bakoji Miskili wanda Allah yayi cikawa a kwanakin baya.
A Alƙaleri, Tawagar tayi ta'aziyyar Rasuwar Alhaji Ubayo Usman wanda ɗan uwa ne ga Sarkin Alƙaleri Alhaji Bala Mohammed Giɗaɗo.
Gwamna Bala Muhammad ya bayyana kaɗuwar sa bisa rashin inda ya bukaci iyalan da su ɗau rashin amatsayin kiran Ubangiji wanda ke kan kowa.
Sarkin Na Alƙaleri Alhaji Bala Mohammed Giɗaɗo ya nuna godiya ga Gwamna Bala Muhammad bisa zumuncin sa ga al'ummar Alƙaleri.
Ya kuma yi Addu'ar Ubangiji ya bashi lada tare da sauran ƴan tawagarsa bisa ziyarar.
Daga Suleiman Musa Kwankiyel