North East community advancement initiative

North East community advancement initiative MATASA DON GOBE MAI KYAU💯💪
DOMIN SAMARWA AREWA MASO GABAS
DAWWA MAMMEN MAFITA

30/07/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdurrahim Yahya Muazu, Khadijah Yahaya Muhammad, Mubarak Wada, Ramlat Muhseen, Abdu Ibrahim Takanda

26/07/2025

North East Community Advancement Initiative (NECAI)

"Matasa don Gobe Mai Kyau"

Wannan kungiya mai Albarka ta North East Community Advancement Initiative (NECAI) ta kasance ginshiki na cigaba da hadin kai a yankin Arewa maso Gabas. A cikin tsananin kalubale da matsin rayuwa, NECAI ta bayyana a matsayin murya mai tsarki, wadda ke tunkarar matsalolin da s**a dabaibaye yankin kamar rashin sahihin ilimi, tabarbarewar kiwon lafiya, matsalolin tsaro, da karancin ababen more rayuwa.

Ta hanyar hadin gwiwa da shugabanni nagari, gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisa masu kishin kasa, NECAI na kokarin tabbatar da cewa al’ummar yankin sun samu wakilci na kwarai da nagarta, domin yankin ya samu ingantacciyar rayuwa.

A yayin da muke matsowa kusa da zaben 2027, NECAI na kira da kakkausar murya ga daukacin jama’ar Arewa maso Gabas da su farka daga baccin sakaci, su nutsu su zabi shugabanni na gaskiya wadanda ke da tsantsar kishin yankin da nagartar zuciya.

Wannan dama ce, ba za mu sake yarda ta wuce mu ba. Lokaci ya yi da Arewa maso Gabas za ta tashi tsaye ta tabbatar da gobe mai kyau!

✍️Abdulmumin Adam Abdulmumin
Zonal Media Director
NORTH EAST COMMUNITY ADVANCEMENT INITIATIVE (NECAI)

26/07/2025

KIRA ZUWA GA MANYAN AREWA
DANGANE DA MAN FETUR DA AKA SAMU A JIHOHIN BAUCHI DA GOMBE

A yanzu haka an fara kwashe manyan kayan aiki da aka jibge a gurin da aka fara tona rijiyar man fetur din Arewa na farko dake Kolmani karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi zuwa wani gurin da ba'a sani ba

Ana ta ficewa da kayan aikin, mutanen da suke kauyen Pali inda hanyar zuwa gurin rijiyar man fetur din yake zasu iya bada shaida akan haka

Menene manufar da tasa aka dakatar da tona rijiyar man fetur din da kuma dalilin da ya sa ake kwashe kayan aikin tonan rijiyar man?

Haka aka yi a makarantar koyar da tukin jiragen sama dake jihar Kaduna, an dauke wani sashi na makarantar an mayar dashi Kudu

Sannan akwai bayanai da suke nuni da ita kanta makarantar horar da sojojin Nigeria DEPOT-NA ita ma ana shirin tarwatsata zuwa wani yanki a Kudancin Nigeria

Ya kamata manyan Arewa da manyan Malaman Arewa da Sarakuna su shiga taitayinsu fa, su samu mutumin nan su tsawatar masa, menene dalilin da yasa ake yiwa Arewa haka?
Yin shiru zai iya zama babbar cin amanar Arewa

Allah Ya isar mana

✍️Abdulmumin Adam Abdulmumin
ZONAL MEDIA DIRECTOR
NORTH EAST COMMUNITY ADVANCEMENT INITIATIVE (NECAI)

24/07/2025

SAKON TUNASAWA GA SHUGABANNINMU NA SIYASA NA AREWA MASO GABAS
Daga Kungiyar: North East Community Advancement Initiative (NECAI)

A matsayinta na ƙungiyar ci gaba da haɗin kai, North East Community Advancement Initiative (NECAI) na kira da roƙo ga Gwamnoninmu, ‘Yan Majalisu, Manyan ‘Yan Siyasa da Sanaroci na shiyyar Arewa Maso Gabas da su susa ido tare da ɗaukar matakin gaggawa don tallafawa yankinmu a wannan dama da gwamnatin tarayya ta buɗe na daukar jami’an tsaro kamar:

Civil Defense (NSCDC)

Nigeria Immigration Service (NIS)

Nigeria Correctional Service (NCoS)

Wannan dama ce mai mahimmanci da za ta taimaka wajen:
✅ Rage rashin aikin yi da ke addabar matasanmu
✅ Tabbatar da kawo ci gaba na gaske a yankinmu
✅ Bada dama ga 'ya'yan talakawa su shiga aikin gwamnati
✅ Kawo zaman lafiya da tsaro a Arewa Maso Gabas

Muna tunatar da shugabanninmu cewa lokaci yayi da za a tsaya tsayin daka wajen kare muradun yankinmu. Wannan dama ba za ta amfani wasu yankuna kaɗai ba, dole ne mu tsaya mu tabbatar da cewa yawan mutanenmu sun samu nasu kaso mai yawa a cikin aikin da gwamnatin tarayya ke bayarwa.

NECAI na kira da a kafa kwamitin tallafi da wayar da kai a kowanne jiha domin:

Taimaka wa matasa wajen cika fom da samun shaidar takardun da ake bukata

Tabbatar da cewa matasanmu sun samu kwarin gwiwa da cikakken goyon baya

Samar da wurin karɓar bayanai da shawarwari ga masu neman aikin

Ya shugabanninmu! Wannan dama ce da za ta kawo sauyi a rayuwar dubban matasa kada a bari ta wuce mu haka kawai.

NECAI Kungiya ce don Gobe Mai Kyau!
Tare da shuwagabanni nagari, Arewa Maso Gabas za ta taci Gaba!

Abdulmumin Adam Abdulmumin
Zonal Media Director
08101691484

Address

Bauchi
740001

Telephone

+2348105133329

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when North East community advancement initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to North East community advancement initiative:

Share