15/08/2026
DYPAM ta gudanar da gangami a Azare, ta marabci Jonathan, ta halarci Convention.
Makon jiya cike yake da manyan ayyuka da shirye-shirye masu matukar muhimmanci ga ƙungiyar Dr. Yakubu Political Awareness Movement (DYPAM) dake aikin wayar da kan jama'a kan manufofin Hon. Yakubu Adamu (PhD), ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam'iyya me farin jini, APM me rogo.
Ranar tara ga wata, DYPAM ta gudanar da gagarumin rangadin da ta shirya a shiyyar Katagum a garin Azare. Taro ne na gani na faɗa kuma ya gudana cikin nasara.
An gudanar da gangamin wayar da kan jama'a kan alfanun fita zaɓe, manufofin APM da shi kan sa Dr. Yakubu Adamu da kuma irin ɗumbin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Bala Mohammed ta yi a faɗin jihar Bauchi. DYPAM ba ta da kalaman godiya ga dubban mahalarta, magoya baya da masu fatan alheri musamman shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM wadanda s**a bada gudunmawa me girma wajen nasarar taron.
Har ila yau, DYPAM a ranar Litinin cikin makon jiya, ta halarci taron martabar tsohon shugaban ƙasa Dr. Goodluck Jonathan zuwa jihar Bauchi don buɗe wasu hanyoyi da wuraren shakatawa da kuma lakca.
Babu shakka al'ummar jihar Bauchi na cigaba da nuna goyon bayan su ga ɗan takarar mu Hon. Yakubu Adamu. Yayin wadannan taruka an ga sauyi da cigaba sosai a fannin siyasar jihar Bauchi musamman shigowar matasa kai tsaye cikin harkokin gudanarwa.
Sai shekaranjiya Alhamis da aka gudanar da babban taron jam'iyyar APM na ƙasa da ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar daga sassa daban-daban na Nigeria. Shi ma DYPAM ta bi sahun takwarorin ta wajen rangadin tare da tallata jam'iyya da kuma yan takara.
Muna sake godewa Allah da ya ba mu dama da nasarar gudanar da wadannan taruka. Muna ƙara gode masa kan yadda muke cigaba da samun karɓuwa da goyon bayan al'ummar jihar Bauchi kan ɗan takarar mu da kuma APM.
Allah ya dafa mana.