03/08/2026
GWAMNATIN TARAYYA TA ƘARA ƘAIMI WAJEN YAƘI DA RASHIN TSARO, AN YAYE DAKARUN FOREST GUARDS A KADUNA DA KOGI
Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi, ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro ta hanyar yaye sabbin dakarun Forest Guards domin daƙile ayyukan 'yan ta'adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka da ke amfani da dazuka a matsayin mafaka.
A Jihar Kaduna, Gwamna Sanata Uba Sani ya jagoranci bikin yaye dakaru sama da 1,000 da aka horas ta haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da Hukumar DSS. An zaɓo dakarun ne daga cikin jami'an Kaduna Vigilance Service (KADVS) guda 7,000, inda aka ba su horo na musamman tare da tanadar musu kayan aiki domin ƙarfafa yaƙi da 'yan ta'adda a yankunan dazuka.
A Jihar Kogi kuwa, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya yaye rukunin farko na dakarun Forest Guards guda 530 bayan sun kammala horo na makonni takwas. Ya bayyana cewa rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen kare dazuka, tattara bayanan sirri da kuma hana masu aikata laifuka samun mafaka.
Gwamnonin jihohin biyu sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da sauran hukumomin tsaro bisa goyon baya da haɗin kai wajen aiwatar da shirin. Haka kuma, wani jami'in ONSA ya bayyana cewa Kaduna ita ce jiha ta farko da ta nemi Gwamnatin Tarayya ta horas da dakarun Forest Guards, yana mai cewa shirin ya samu gagarumar nasara.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa faɗaɗa rundunar Forest Guards wani muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen hana 'yan ta'adda amfani da dazuka a matsayin mafaka, tare da inganta zaman lafiya da samar da yanayin da zai bunƙasa noma, kasuwanci da sauran ayyukan raya ƙasa.
— Burra Daily News