IGABI TRUST TV

IGABI TRUST TV IGABI TRUST TV
(Murar Al'umma)

ALLAH BA YA BARCI.Bai kai shekara ashirin ba lokacin da mahaifinsa ya rasu, ya gaji dukiya mai yawa wanda hakan ya sanya...
23/09/2025

ALLAH BA YA BARCI.

Bai kai shekara ashirin ba lokacin da mahaifinsa ya rasu, ya gaji dukiya mai yawa wanda hakan ya sanya ya iya karasa karantunsa a Turai a daya daga cikin jami’o’i mafi tsada. Bayan ya kammala ya bude kamfaninsa, saboda girman kamfanin da kuma kaurin albashi sai ya darje wajen zaben ma’aikata.

A cikin ma’aikatan da ya dauka akwai wani saurayi mai kamala da addini, kuma shi ma injiniya ne kamar mai gidansa, kuma kwararre. Saboda nutsuwarsa da kwarewarsa mai gidansa ya ba shi bangaren gidansa don ya zauna (boys quarters), a nan kuma ya nemi izini ya kawo matarsa da ba su dade da yin aure ba.

Ya kawo matarsa, ya nemi ta je ta gaida mahaifiyar wannan mai gidansa, a nan ya ga mata kyakkyawar gaske, kuma take sai shaidan ya fara aikinsa a cikin zuciyarsa. Haka dabara ta zo masa, a cikin ayyukansu wadanda suke yi a wajen wannan gari, sai ya tura wannan bawan Allah don ya je ya duba, wanda zai dauke shi kwanaki har hudu, shi kuma yana tunanin dama ta samu.

A washe garin tafiyar wannan bawan Allah sai wannan uban gidan nasa ya nemi mahaifiyarsa da su je can wani gidan gonarsa wanda ya gada don su dan canja yanayi, ya nemi kuma ba ta shawarar ta nemi wannan matar da ta raka ta. Haka kuwa aka yi.

Bayan sun shiga gidan gonar suna ta yawatawa, sai mahaifiyar ta gaji, ta je ta zauna, shi kuma sai s**a ci gaba da zagayawa s**a isa wani bangare, shigarsu ke da wuya, sai ya ja kofa ya rufe, don ya yi abin da s**a saba yi wa duk wanda s**a shigo da ita wannan gidan gonar.

Kayaya-kayaya yana faman kokarin samun hanyar da da zai aikata aika-aikansa, sai ya ji ana buga kofa, take ya kyale ta, yana zaton ko mahaifiyarsa ce ta jiyo abin da yake faruwa. Yana bude kofa sai ya ga wani abokinsa da s**a saba irin wannan aika-aika tare ya yi sharkaf da gumi, har rigarsa ta dan yage, sai ya ce masa:”Yau me ya same ka ne! ka kawo mana wannan matan masu taurin kai, dubi wancan ma da kyar na iya yin ……… da ita”

Jin haka ke da wauya, sai mai gidan ya rude, ya bazama waj

HON.HUSSAINI MUH.D JALLO  IS THE ONE MEMBER FOR HOUSE OF REPRESENTATIVE IGABI FEDERAL CONSTITUENCY LOOK AT PHOTOS:THIS I...
21/09/2025

HON.HUSSAINI MUH.D JALLO IS THE ONE MEMBER FOR HOUSE OF REPRESENTATIVE IGABI FEDERAL CONSTITUENCY

LOOK AT PHOTOS:

THIS IS THE WORKS THAT HE DID IN OUR AREA REALLY HE GOT THE SOLARS IN DIFFERENT TOWNS

THAT IS WHY WE MUST SHOW AND TELL OTHER PEOPLE THIS THING THAT HE DID WE WILL NOT HIDE IT.

BY RABI'U NUHU ƊAN BABA
IGABI TRUST TV

Wata ɗaliba ƳaR aji 9 ta haihu a cikin bandakin makaranta. Abin mamaki shi ne, babu wanda ya san tana da juna biyu, ko m...
31/08/2025

Wata ɗaliba ƳaR aji 9 ta haihu a cikin bandakin makaranta. Abin mamaki shi ne, babu wanda ya san tana da juna biyu, ko malamanta, ko abokan karatunta, har ma da iyayenta...

26/08/2025

RANAR HAUSA TA DUNIYA: Rubuta Mana Karin Magana Daya Da Ka Sani A Yaren Hausa

A cikin  babban birnin Tajikistan, Dushanbe, akwai wani mutum mai suna Talabshoh Sheikhov.Shekaru da dama da s**a wuce, ...
25/08/2025

A cikin babban birnin Tajikistan, Dushanbe, akwai wani mutum mai suna Talabshoh Sheikhov.

Shekaru da dama da s**a wuce, wasu mafarauta s**a farauci wata dabbar Bear daji Mai karamin da. Ɗanta ƙarami ya rage, wanda ba zai iya rayuwa shi kaɗai ba. Wani dattino Mai suna Sheikhov ya bayar da akuya aka bashi wannan jaririn bear ya ceci rayuwarta daga hannun mafarauta ya kawo ta gidansa, ya rainonta kamar ɗaya daga cikin ’ya’yansa goma sha uku. Ya sanya mata suna Maria.

Maria ta tashi tana shan madara daga kwalba, tana kwana a tsakanin yara, tana bin Sheikhov ko’ina. Lokacin da abinci ya yi ƙaranci a tsaunukan da suke rayuwa, sai ya kai ta birnin Dushanbe.

Fiye da shekaru 20, mutanen birnin s**a saba da gani abin ban mamaki, na wannan Tsohon da wannan Bear

Maria tana yin wasanni, tana yawo a t**i, tana hawa bas, har ma tana ɗaukar Sheikhov a bayanta. Ga yara abin mamaki ce, ga manya kuwa al’ajabi ne. Sun zama wani ɓangare na tarihin birnin , har ma daga baya mazauna s**a nemi a gina musu mutum-mutumi.

Amma kowane labari yana da ƙarshe. A shekarar 2013, Sheikhov ya rasu yana da kusan shekaru 80. Bayan wata biyu kacal, Maria ma ta mutu , kamar dai ba za ta iya rayuwa ba tare da shi ba.

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta dakatar da shirin sauyawa sauro ƙwayar halitta ƙarƙashin wani shiri da gidauniyar Bill G...
25/08/2025

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta dakatar da shirin sauyawa sauro ƙwayar halitta ƙarƙashin wani shiri da gidauniyar Bill Gates ke ɗaukar nauyi, wanda aka ce baya ɗauke da cutar Malaria, da sunan yaƙi da cutar haɗi da sauran cutukan da ake kamuwa da su ta hanyar cizon ƙwari a nahiyar Afirka.

Ƙarin bayani: https://rfi.my/BwzB

Yanzu fa duk wannan cikar farin dango da aka yi a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, wani ...
25/08/2025

Yanzu fa duk wannan cikar farin dango da aka yi a filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, wani yana cikin garin ma, amma bai san yau kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta yi wasa ba, Kuma har ta yagalgala Plateau United.

Shin kavsan da labarin wasan, ko kaima dan yankin Yelwa ne, baka shigowa gari sai ranar Sallah?

📷 Muhammad Audu Sharinah

Shirye-shirye sun yi nisa na auren fitaccen jarumin Kannywood KB International wanda za a yi a mako mai zuwa.Wane fata z...
25/08/2025

Shirye-shirye sun yi nisa na auren fitaccen jarumin Kannywood KB International wanda za a yi a mako mai zuwa.

Wane fata zaku yi musu?

Akwai wani mutum mai karamin karfi wanda yake samun abin da zai ci ta hanyar sayar da zuma.Wata rana da sassafe ya ɗauki...
25/08/2025

Akwai wani mutum mai karamin karfi wanda yake samun abin da zai ci ta hanyar sayar da zuma.
Wata rana da sassafe ya ɗauki kwaryar zumar sa ya daura a kansa, ya tafi kasuwa. Rana na ta dukan kansa kamar wuta, garin yayi zafin da ba’a misaltawa.

Yana cikin tafiya sai gajiya ta kamashi sosai, sai ya ce:
"Bari in huta kadan a ƙarƙashin wannan bishiyar."

Ya ajiye kwaryar zumar a gefe, ya zauna sai ya nutsa cikin tunani.
Daga nan kuma sai ya fara mafarki:

"Zan sayar da wannan kwaryar zumar, sai in sayi akuya.
A kuyar za ta haifa mini awaki guda biyu, in raine su.
Idan sun girma, in sayar da ɗaya, in sayi saniya.
Saniyar za ta haihu, in sayar da ‘ya’yanta, in sayi fili.
In gina gida, in auri mace kyakkyawa, in haifi yara, in tarbiyyantar da su yadda ya kamata!"

Ya ci gaba da yin mafarkin rayuwa mai kyau…

Kwatsam a cikin mafarkin sa sai ya ɗauka a cikin tunaninsa cewa ɗansa ya yi masa laifi.
Sai ya yi masa ihu da ƙarfi:
"Kai! Me yasa zaka yi haka!"

Ya miƙe da sauri yana faɗa, ya kai masa bugu da ƙafa kamar wanda ke dukan yaro…
Amma kafin ya ankara, sai ƙafarsa ta buge kwaryar zumar, ta kife!
Kawaryar ta fashe, zuma ta zube a ƙasa, ta lalace baki ɗaya.

Ya tsaya yana kallon zumar tana kwarara, sai ya ce:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...
Na riga na gina katafaren gida a cikin mafarkina…
Sai gashi yanzu ya rushe tun kafin ma in siyar da kwaryar zumar!"

📝 Darasi:

Kada ka yaudari kanka da mafarki har ka manta da hakikanin rayuwarka ta gaskiya.
Ka gina rayuwarka da abin da ka ke dashi a hannunka, ba ka gina ta a kan mafarkin da bai zai tabbata ba.

Alamar tozarta ita ce ka ga mutum ya shagalta da binciken aibin wasu, ya mance da aibinsa. Ya yayata laifukan wasu, shi ...
24/08/2025

Alamar tozarta ita ce ka ga mutum ya shagalta da binciken aibin wasu, ya mance da aibinsa. Ya yayata laifukan wasu, shi kuma ya take nasa laifin.

ABIN A YABA: Sarauniyar Kyau Ta Jihar Adamawa, Franca Amos Malgwi Ta Raba Kyautar Naira Dubu 250 Ga Wadanda Ambaliyar Ru...
24/08/2025

ABIN A YABA: Sarauniyar Kyau Ta Jihar Adamawa, Franca Amos Malgwi Ta Raba Kyautar Naira Dubu 250 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwan Ta Shafa A Jihar

Wane fata zaku yi mata?

Menene Ra'ayinku Da Wannan Hadin A Gidan Sarauta?IGABI TRUST TV
24/08/2025

Menene Ra'ayinku Da Wannan Hadin A Gidan Sarauta?

IGABI TRUST TV

Address

Bauchi

Telephone

+17044197587

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IGABI TRUST TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to IGABI TRUST TV:

Share