
23/09/2025
ALLAH BA YA BARCI.
Bai kai shekara ashirin ba lokacin da mahaifinsa ya rasu, ya gaji dukiya mai yawa wanda hakan ya sanya ya iya karasa karantunsa a Turai a daya daga cikin jami’o’i mafi tsada. Bayan ya kammala ya bude kamfaninsa, saboda girman kamfanin da kuma kaurin albashi sai ya darje wajen zaben ma’aikata.
A cikin ma’aikatan da ya dauka akwai wani saurayi mai kamala da addini, kuma shi ma injiniya ne kamar mai gidansa, kuma kwararre. Saboda nutsuwarsa da kwarewarsa mai gidansa ya ba shi bangaren gidansa don ya zauna (boys quarters), a nan kuma ya nemi izini ya kawo matarsa da ba su dade da yin aure ba.
Ya kawo matarsa, ya nemi ta je ta gaida mahaifiyar wannan mai gidansa, a nan ya ga mata kyakkyawar gaske, kuma take sai shaidan ya fara aikinsa a cikin zuciyarsa. Haka dabara ta zo masa, a cikin ayyukansu wadanda suke yi a wajen wannan gari, sai ya tura wannan bawan Allah don ya je ya duba, wanda zai dauke shi kwanaki har hudu, shi kuma yana tunanin dama ta samu.
A washe garin tafiyar wannan bawan Allah sai wannan uban gidan nasa ya nemi mahaifiyarsa da su je can wani gidan gonarsa wanda ya gada don su dan canja yanayi, ya nemi kuma ba ta shawarar ta nemi wannan matar da ta raka ta. Haka kuwa aka yi.
Bayan sun shiga gidan gonar suna ta yawatawa, sai mahaifiyar ta gaji, ta je ta zauna, shi kuma sai s**a ci gaba da zagayawa s**a isa wani bangare, shigarsu ke da wuya, sai ya ja kofa ya rufe, don ya yi abin da s**a saba yi wa duk wanda s**a shigo da ita wannan gidan gonar.
Kayaya-kayaya yana faman kokarin samun hanyar da da zai aikata aika-aikansa, sai ya ji ana buga kofa, take ya kyale ta, yana zaton ko mahaifiyarsa ce ta jiyo abin da yake faruwa. Yana bude kofa sai ya ga wani abokinsa da s**a saba irin wannan aika-aika tare ya yi sharkaf da gumi, har rigarsa ta dan yage, sai ya ce masa:”Yau me ya same ka ne! ka kawo mana wannan matan masu taurin kai, dubi wancan ma da kyar na iya yin ……… da ita”
Jin haka ke da wauya, sai mai gidan ya rude, ya bazama waj