Dambam Online TV

Dambam Online TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dambam Online TV, Media/News Company, Dambam, Bauchi.

07/11/2025
07/10/2025

KILISA! KILISA!! KILISA!!!
Sulaiman Ghali Muhammad Yana gayyatar Dokacin Al'umma zuwa wurin KILISA da ya shirya a ranar Juma'a 10/10/2025 da misalin karfe 04:30 na yamma A Fadar Mai Girma Hakimin Dambam
fans

BAUCHI CENTRAL KAI TAKE JIRA 2027Hon. Ibrahim Makama Misau Mutum Ne Jajirtacce Wanda Yayi Fice A Jahar Bauchi Dama Arewa...
02/10/2025

BAUCHI CENTRAL KAI TAKE JIRA 2027

Hon. Ibrahim Makama Misau Mutum Ne Jajirtacce Wanda Yayi Fice A Jahar Bauchi Dama Arewacin Nigeria Ta Bangarori Da Dama

Saboda Jajircewarsa A Cikin Dukkan Lamuransa Yasa Ake Masa Lakabi Da Suna (JAN-ZAKI)

Ibrahim Makama Dan Karamar Hukumar Misau Ne Dake Cikin Jahar Bauchi, Dan Siyasa Ne Sannan Kuma Dan Kasuwa Ne

A Aikin Gomnati Kuma Tsohon Dan Sanda Ne, Wanda A Lokacin Da Yayi Aikin Dan Sanda Saboda Kwarewar Sa Da Iya Aikin Sa Sai Da Yayi ADC A Gomnoni Biyu A Kasar Nan

Yayi ADC Wa Tsohon Gomnan Jahar Bauchi HE Ahmed Adamu Mu'azu A Farkon Tenure Nasa, Daga Nan Ya Koma ADC Wa HE Malam Ibrahim Shekarau Tsohon Gomnan Kano

Bayan Ya Kammala Aikin Dan Sanda Al'ummar Mazabar Misau Da Dambam Suka Masa Kiranye Daya Fito Takarar Dan Majalisar Tarayya A Mazabar Misau Da Dambam A Shekarar 2007

Ibrahim Makama Yaci Zaben Sa Na Dan Majalisar Tarayya A Lokacin A Karkashin Tutar Jam'iyar ANPP, Ya Bada Gudumawa Matuka Gaya A Wancan Lokacin Wajen Kawo Malam Isa Yuguda A Matsayin Gomnan Jahar Bauchi

A Lokacin Da Ya Zama Dan Majalisa Ibrahim Makama Yayi Fice A Cikin Majalisar Tarayyar Nigeria Duk Da Kasancewar Sa Daga Jam'iyar Adawa Ya Fito A Lokacin (ANPP)

A Bangaren Kawo Sauyi Da Taimakon Al'umma Kuwa Al'ummar Yankin Da Ya Wakilta Sun Tabbatar Da Cewar Daga Lokacin Da Yahau Kayin Mulki A Shekarar 2007 Daga Lokacin Suka San Amfanin Dan Majalisar Tarayya

Ibrahim Makama Ya Samar Da Ayyukanyi Wa Matasa Masu Yawa A Wannan Lokacin, Wanda Ya Hada Da Aikin Yan Sanda, Sojoji, Imagration, Fire Service, Prostatal, Da Board Board Tare Da Sauran Ayyukan Raya Kasa

Bayan Wa'adin Mulkinsa Na Shekaru Hudu Sun Kare Ibrahim Makama Bai Nemi Damar Takarar Tazarce Ba A Wancan Lokacin Kamar Yanda Wasu Suke Nema Bisa Al'adar Siyasa

Bayan Shekaru Takwas Da Saukansa Akan Kujerar Dan Majalisar Tarayyar, Mazabar Ta Tura Mutane Biyu Sun Wakilce Ta, Wanda Kowa Yayi Shekaru Hudu Akayi

Bayan Dogon Tunani Da Nazari Da Wassu Kungiyoyi Sukayi Daga Masarautar Misau A Shekarar 2019 Sai Suka Sakeyin Kiranye Wa Hon. Ibrahim Makama Daya Daure Yazo Ya Sake Amsa Kiransu

Cikin Yardar Allah Da Yardar Al'ummar Mazabar Misau Da Dambam Hon. Ibrahim Makama Ya Sake Zama Dan Majisar Tarayya A 2023 A Karkashin Tutar Jam'iyar APC

Dawowar Sa Kan Karagar Mulki Kuwa Bai Rasa Nasaba Da Irin Ayyukan Alkhairan Da Yayi Wa Al'ummar Mazabar Sa Bane Na Baya A 2007

A Tarihin Kujerar Dan Majalisar Tarayya A Mazabar Misau Da Dambam Tun Daga Dawowar Dimokradiya A Shekarar 1999 Zuwa Yau Ba'a Tabayin Dan Majalisar Daya Samar Wa Matasa Ayyukan Yi Wanda Yakai Na Hon. Ibrahim Makama Ba

A Cikin Binciken Kokof Da Mukayi A Cikin Jam'iyar Mu Ta APC A Cikin Shiyar Mu Na Bauchi Ta Tsakiya Bamu Ga Wanda Ya Kamata Mu Turashi Majalisar Dattawa Domin Ya Wakilce Mu Ba Wanda Ya Wuce Hon. Ibrahim Makama

Muna Kira Zuwa Gareshi A Madadin Al'ummar Bauchi Ta Tsakiya Daya Zo Ya Amsa Kirammu Na Neman Takarar Kujerar Sanatan Bauchi Ta Tsakiya A Shekarar 2027

Sako Daga
Comr. Mustapha Sale Warji
Central Zone Co-odinator APC Research For Develoent Forum
08025863196

Address

Dambam
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dambam Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share