01/08/2026
Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya ce bai yi wa kowa laifi ba a sabuwar wakarsa mai taken "Malam Ka Yi Rawa", yana mai cewa bai ambaci sunan wani mutum a cikin wakar ba.
Rarara ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa, inda ya ce manufarsa ita ce yabon ɗan takarar gwamnan jam'iyyarsa ta APC, ba tare da yin nuni ga wani mutum kai tsaye ba.
A cewarsa, "Riga na dinka ba wuya; duk wanda ya ga ta masa dai-dai, sai ya saka." Ya jaddada cewa wakar ba ta ambaci sunan kowa ba, don haka bai ga cewa ya aikata wani laifi ba.
Sai dai, tun bayan fitar wakar, ta janyo muhawara a tsakanin al'umma. Wasu na ganin cewa wakar ta yi nuni da fitaccen malamin addinin Musulunci kuma ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Jihar Gombe, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, duk da cewa ba a ambaci sunansa kai tsaye ba.
Masu wannan ra'ayi sun yi zargin cewa wasu kalaman da ke cikin wakar na iya zama cin mutunci ko bata suna, inda suke ganin an danganta su da batutuwa kamar shan miyagun ƙwayoyi da ta'addanci.
A gefe guda kuma, akwai masu kare Rarara da ke cewa tunda bai ambaci sunan kowa ba a wakar, bai kamata a ɗauki cewa ya yi wa wani mutum nuni kai tsaye ba.
Lamarin dai na ci gaba da haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan ma'anar wakar da tasirinta.
Shin ku mene ne ra'ayin ku?