
16/08/2025
MUTUMIN DA YA HAIFI 'YA'YA 102 A UGANDA YACE YA DAKATAR DA HAIHUWA HAKA
Wani Mutum a Kasar Uganda, Musa Hasahya Kasera dan kauyen Mukiza, ya shahara wajen haihuwar yara, inda yake da 'ya'ya 102 da mata 12 - duk suna zaune a ƙauye ɗaya! Yanzu ya cika shekaru 68 da haihuwa, ya ce haihuwar “ya isa haka” kuma ya nemi matansa da su fara amfani da maganin hana haihuwa, yayin da yake kokawa wajen ciyar da dimbin iyalinsa da gona kadada biyu kacal da yake dashi.
Yana da jikoki 578, Musa ya bayyana cewa ba zai iya tunawa da duk sunayen ‘ya’yansa ba, don hakane ya dogara da littattafan rubutu don ya taimaka masa wajen gano sunayen.
Wasu matan nasa sun riga sun gudu saboda talauci. Yana yin taron dangi akai-akai don gujewa hargitsi a cikin iyalansa.
Duk da gwagwarmaya da yasha, yana alfahari da babban iyali da ya gina, kuma yana fatan labarinsu ya ƙarfafa wasu game da haɗin kai, al'ada - da kuma mahimmancin tsari a rayuwa.