25/09/2025
Dr. Haruna Maiwada Ya Bada Gaggarumin Tallafi Na Milyoyin Kudi Ga Al'ummar Jihar Katsina
.tabbas Dr Maiwada ya cancanci yabo, inji Gwamna Dikko Radda a lokacin da yake kaddamar da bada tallafin
Dr. Haruna Umar Maiwada ya bada tallafin miliyoyin nairori ga al'ummar Katsina a yau Alhamis, inda taron ya wakana a filin wasa na Muhammad Dikko dake birnin Katsina.
Mutane kimanin 1,350 ne s**a amfana da tallafin motoci kirar Hijet 35, matoci 6, litattafai 20,000, mashina 100, injinan Markade 250, injinan taliya 500, da kuma mata masu kanana da matsakaitan masana'antu 700 da s**a amfana da tallafin zunzurutun kudi na naira miliyan talatin (₦30,000,000) hadi da tallafawa masu bukata ta musamman duk don habbaka tattalin arziki da kuma taimakawa kokarin Gwamnan jihar Katsina.
A yayin jawabinsa, Gwamanan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya yaba da kokarin da Haruna Maiwada ke yi, wanda yin hakan shine kowacce gwamnati ke kara samun cigaba idan ana samun ire-iren Dan Amanar Katsina, wanda hakan zai taimaka wajen samun sauki da kuma samar da sana'o'in dogaro da kai ga matasa maza da mata.
Gwamnan ya cigaba da cewa "ba mu yi mamaki ba saboda gado ka yi wajen mahaifan ka kuma uwar jam'iyyar APC tana godiya akan abinda kayi. Allah Ya kara daukaka Haruna Maiwada domin ya tallafi al'umma".
Daga karshe a madadin uwar jam'iyyar APC ta jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya godewa Dan Amanar Katsina akan wannan tallafi da ya bada, inda ya kara da cewa haka ake so duk wani mai hali ya yi.
Taron ya samu halartar shugaban karamar hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD. Saude, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba, Alhaji Umar Tata, Engr. Muttaka Rabe Darma.
Sai kuma Sarkin Sullubawan Katsina Alhaji Yazidu Abdul Kareem, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Malam Abu Ammar shugaban hukumar Hisbah na Jihar Katsina, 'yan kasuwar. Da dai sauransu.
Daga Muhammad Sani Ibrahim Kaita
Mataimaki na musamman ga Dr. Haruna Maiwada akan harkokin Sadarwa
25 ga watan Satumba 2025