28/12/2025
Ban-ga Abinda Muhammad Ali Pate Zai Dauka A Baitulmalin Jihar Bauchi Ba
A lokacin annobar cutar mashako (COVID 19), tsakanin shekarar 2019, zuwa shekarar 2021. Farfesa Muahammad Ali Pate a matsayinsa na daraktan lafiya, kididdigar jama'a, sannan kuma daraktan kudi na bankin duniya, shi ya jagoranci rabon tallafin zunzurutun kudi har dala biliyan goma sha takwas wa kasashen duniya kimanin dari. Duk mai inkarin wannan magana, zai iya bincikawa.
Ka san nawa ne dala biliyan goma sha takwas a nairan Najeriya? wannan kudi yana daidai da sama da naira tiriliyan ashirin da shida. Ya raba wadannan kudade cikin nasara, babu korafi, sai dai ma yabo.A duk mukaman da farfesa Muhammad Ali Pate ya taba rikewa a duniya, da nan gida Najeriya, ba a taba samun sa da matsalar cin abinci, ko kuma karban rashawa ba.
Saboda tsantsan zuhudunsa, gidan farfesa Muhammad Ali Pate a Bauchi, tamkar gidan wani tsohon komishina yake. Kai! na san gidajen tsofaffin komishinonin da s**a fi na Mainasaran Bauchi kyau. Gidansa na Abuja kuwa, gwanjon gwamnati ne. A tarihin rayuwarsa, bai taba satan dukiyar gwamnati don ya azurta kan sa ba, sannan kuma da saninsa, bai taba barin wani ya sata ba.
Ban-ga abinda farfesa Muhammad Ali Pate zai dauka a baitulmalin gwamnatin jihar Bauchi ba idan ya zamo gwamna. Inda kuma tara dukiya ne damuwarsa, da bai dawo Najeriya ba. Idan Allah ya kaddari zamowarsa gwamna, zai rike amanar dukiyar al'ummar jihar Bauchi, tamkar yadda ya rike amanar dukiyar al'umma a sauran guraren da ya yi aiki. Kana kuma, zai samar wa jihar Bauchi hanyoyin samun karin kudaden shiga daga kasashen duniya.
Pate Media Center