14/08/2025
"Ko a Fim ɗin Indiya, Mutum Mai Mugunta Yana Burge Ni" — Hauwa Musa Adam
A wata tattaunawa da BBC Hausa, fitacciyar jarumar Kannywood, Hauwa Musa Adam, ta bayyana irin yadda ta fara sha’awar harkar fim tun tana ƙaramar yarinya a garin Jos, Jihar Filato.
Hauwa, ‘yar asalin kabilar Birom, ta ce ta tsaya karatunta ne a matakin sakandare, amma rayuwa ta koya mata darussa masu amfani.
Ta yi aure amma ta fuskanci ƙalubale, inda daga bisani ta rabu da mijinta. Bayan rabuwar, wata abokiyar ta mai suna Hajara — wadda yanzu haka kwamishiniya ce a Jihar Bauchi — ta gabatar da ita ga kamfanin Hayas Film Production.
Daga nan aka kai ta Lenzcup, sannan yayanta ya samu mata aiki a gidan rediyo, duk ba tare da ta sanar da iyalanta ba.
Ta fara fitowa a fina-finan Hausa ne a cikin shirin Babban Kasa, inda ta haɗu da jaruma Daso a karo na farko. “Na yi mamakin ganin ta sosai har sai da na buga kaina da murfin taga,” in ji ta cikin dariya.
Hauwa ta ce ƙalubalen da ta fi fuskanta a harkar fim shi ne yawan sauya kaya don ɗaukar gurare daban-daban.
Sai dai ta bayyana cewa abinda ya fi faranta mata rai shi ne yadda mahaifinta ya karɓi harkarta da hannu biyu, bayan jin an yi hira da ita ba tare da ta boye asalinta da yarenta ba.
“Mahaifina ya ce in ci gaba da yin fim ɗina, Allah ya sa a samu albarka,” in ji ta.
A cikin hirar, Hauwa ta bayyana wata dabi’a: “Ni ko a fina-finan Indiya, mutum mai mugunta yana burge ni,” in ji ta.
Jarumar ta ce babu abin da ya fi damunta a yanzu fiye da rashin mahaifi da mahaifiya, sai dai ta ce tana samun kwanciyar hankali idan ta yi wani abu da ta san zai faranta musu rai.
Ta kuma bayyana burinta na zama k**ar Laylah Ali Othman, matar wani ɗan majalisa a Jos, wadda ta shahara wajen taimakon al’umma.
Shawarar da ta bai wa sauran jaruman Kannywood ita ce su kasance masu tsoron Allah a duk inda suke da kuma a duk abin da suke yi.