01/10/2026
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUH
AMADADIN SHUGABAN ƘUNGIYAR MATASAN ALARAMMOMI
Muna farin cikin sanar da ɗaukacin ’yan uwa cewa mun buɗe wannan shafi mai albarka, domin ci gaba da bayyana manufofin alheri da ƙoƙarin da muke yi domin amfanin al’umma, musamman matasan Alarammomi da sauran ’yan uwanmu matasa.
Manufarmu ita ce mu haɗa kanmu, mu taimaki juna wajen jawo alheri, da kuma haɗa ƙarfi wajen kawar da abubuwan da ke kawo mana cikas.
Lokaci ya yi da ya kamata matasan Alarammomi su haɗa kansu wuri guda, domin tunkarar ƙalubalen da ke gabansu, neman mafita tare, da kuma gina kyakkyawar makoma.
Muna fatan wannan shafi zai zama wurin haɗin kai, ilimi, wayar da kai da cigaban matasa.
Muna kira ga kowa da kowa da ya shiga wannan tafiyya mai albarka, tare da niyyar neman alheri, taimakon juna da kuma cigaban matasa, musamman matasan Alarammomi.
Allah Ya haɗa kanmu, Ya albarkaci wannan tafiya, Ya sanya ta zama sanadin alheri ga matasa da al’umma baki ɗaya.