29/07/2024
Ƙungiyar "Arewa Media Writers" Ta Umurci Dukkanin Membobinta Na Jahohi 19 Har Da Abuja Dasu Fito Zanga-zangar Lumana A Ranar Alhamis Mai Zuwa
Kungiyar marubutan tayi wannan kiran ne ga membobin kungiyar baki ɗaya bayan kiraye-kiraye da nuna wa gomnati irin halin da al'ummar Arewa suke ciki na matslolin rashin tsaro, yunwa, tsadar rayuwa amma gwamnati ta kasa magance su.
Hakan yasa kungiyar ta ɗauki wannan mataki na fitowa zanga-zangar lumana domin ƙara sanar da gomnati matsalolin da muke fuskanta a yankin Arewa.
Haka zalika kungiyar ta kara jaddada wa magoya bayan ta, da cewa babu fitowa da makami ko cin zarafin wani, ko ɗaukar kayan wani yayin zanga-zanga.
Kungiyar ta yi kira ga dukkan masu fitowa zanga-zangar da su bawa jami'an tsaro hadin kai yayin fitar, haka kuma su kula da bin tsari da doka da oda na ƙasar mu Nijeriya, ba fito na fito muke da gwamnati ba, illa kira ga hukuma da su san halin matsi da ƙunci da al'umma suke ciki.
Kungiyar "Arewa Media Writers" bata kowa bace, kuma bata gomnati bace, an samarda ita ce domin kare muradun yankin mu Arewa.
✍️✍️ Muhammad Kwairi Waziri, National Director Media And Publicity II, Of "Arewa Media Writers".