31/10/2025
Babbar kotun jiha dake Miller Road a Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahiru, ta tura wani magidanci gidan gyaran hali bisa zarginsa da kashe matarsa, bayan ya ce ta ki daka masa ƙuli-ƙuli kamar yadda ya buƙata.
Freedom Radio ta rawaito cewa magidancin, mai suna Idris Kurma, ya gurfana a gaban kotun dauke da takardar tuhumar kisan kai, wanda ya saba da sashi na 221 na kundin hukunta laifuka.
Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ne ya gabatar da karar, inda bayan karanto masa takardar tuhumar, wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Lauyan gwamnati ya roki kotu ta ba su lokaci domin su kawo shaidu. A nasa bangaren, Barista Ibrahim Adakawa, wanda yake kare wanda ake tuhuma, ya roki kotu ta basu cikakken bayani kan shari’ar.
Kotun ta amince da rokon lauyoyin sannan ta sanya ranar 12 ga Disamba, 2025, domin sake gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.
Ana dai zargin Idris Kurma wanda yake zaune a garin Goda, cikin karamar hukumar Shanono, da kashe matarsa Aisha Idris, bayan ya umarceta da ta daka masa kuli-kuli amma ta ki yin hakan. A cewar rahotanni, hakan ne ya sa ake zargin ya shaketa, wanda kuma ya haifar da mutuwarta.